← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 69

Sashe 34

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abba ba shi da mafita saboda Umarnin Innani ne, haka ta koma Shinkafi da zama tare da Umma da Sadiq tana kula da Umma gefe daya ta na kula da Magajin gida. Shiyasa Sadiq yace Innani na da Muhimmanci a Rayuwarsa yana da wata takwas ta cireshi a nono saboda daman sai da Dubara Umma ke iya ba shi Nonon Tunda har Lokacin sai a hankali.
Shiyasa Sadiq ya gini da ciye ciyen abincin gargajiya tunda duk shi Innani ta rika Dura masa.
Ya taso ya gansa a Shinkafi ne tare da Umma da Innani, sai dai Abba da Sauran yan'uwansa na zuwa dubashi a kai akai ko da suke a shinkafi ba bu gatan da Sadiq bai gani ba Abba da Inanni kamar zasu lashe shi Saboda so da kauna in kana son su soka to ka so magajin gida sai suma su soka.
Umma sai da ta kusa shekara Biyar cikin wannan Halin sannan ta warke da taimakon magungunar musulumci,da addu'o'in malamai lokacin da ta warke ita kuma Sai Hauwa ta fara ciwo daga zazzabi ta fara sai rama kuma Sai Innani bata koma Gusai ba sai Umma ce ta koma Gidan Mijinta aka kuma bar ma Innani Sadiq a hannunta.
Shekara takwas ya kwashe a shinkafi sannan ya dawo gusai wajen  iyayensa da zama tare da Innani wacce ta kasance itace komai na shi. Tun yana karaminsa ya ke da katon bangare shi kadai kuma ya mallaki komai da yan gata ke mallaka.
Sai dai shi ra'ayinsa ba shi kan Sauran Ra'ayin wadanda ke zagaye da shi.
Ra'ayinsa Dabam ne da na kowa sannan Rayuwarsa mai Sauki ce ba kamar yadda akayi Tunanin Magajin gida zai kasance ba.

Sultana Diyar Hauwa ce wacce ta Haifeta ko ganinta ba ta yi ba Allah ya yi mata rasuwa,Umma na ganinta ta ji ta na sonta ta Dauketa Innani ta Daurre mata Gindi Dole Shitu ya bar musu Sultana yasan Tijaran Innani bai isa ya musa ba. Dalilin da zamanta ya Dawo gidan su da Sadiq kenan Hannun Umma.
Sadiq tun yana karaminsa mutum ne mai sanyin Hali Tausayi da jinkai, ga Abba da mako da son abun duniya shi da Innani ammh kuma shi ba su iya masa gaddama. Tun yana da sha wani abu a duniya yasan ya taimaki wadanda ba su da shi, ko a hanya yaga mutum na neman taimako zai ce ka Biyosa sai gida sai dai Abba yaji sallama kuma ba shi da ikon cewa a'a kai tsaye Sadiq zai ce Abba a taimaka masa don Allah.
Sannan shi Yaro me da ke son zama cikin mutane ko da bazai Rabesu ba, ammh yana son zama cikin Anguwan da ke da cikowar Mutane shi dai ya kasance ya na ganin Mutane kowa na Harkan gabanshi.
Mutum ne da ke son Rayuwa daidai misali bai cika son Dora Rayuwarsa kan Babban mizanin da kowa ya Dauke shi ba. Ya san shi dan gata ne gaba da baya. Ba Iya Innani ba kaf Dangi kowa shi ya ke so burin shi ya farantamasa rai. Tausayinsa ya siya masa soyayyan Mutane tun kafin ya zama Saurayi su Baba Sammani suka rike shi kamar shine Abba Tunda in ka fad'amasa matsalanka to kaje gida ka kwanta ka gaddara ma matsalarka ta kare.
Ya na son Mutane da son yan'uwa mafi girman abunda ke ranshi Shine Tausayi Sadiq ba ya so yaga Mutane na cikin wani Hali ya kasa taimakawa baya so yaga wani cikin halin Babu ko Damuwa in dai yana da Halin taimakawa shiyasa in kaga Abba ya yi kyauta to Sadiq shi ne in yace ba'a iya Saba mganarsa Innani ta kan ce yi masa komai ya ke so tunda komai da ka mallaka na shi ne magajin gida.
A shinkafi ya fara Fimari dinsa sannan yazo gusai ya karisa secondary school dinsa wata makaranta ya yi mai hade da boko da arabi saboda son addininsa.
Yana da naci kan abunda ya ke so ya koya,yan'uwansa ba su so ya yi karatu ma a Nageria ba, sai dai kuma Uban gayyar baya Ra'ayin haka.
Sannan ga Mallam Taju da ya ke Daukan karatu a wajensa.
A makaranta suna hadda sannan in ya Dawo gida yana yi wajen Mallam Taju shiyasa cikin Lokaci ya samu ilmin da ko iyayensu ba su taba Tunanin yana da shi ba.
Kafin ya gama Secondary School ya Sauke Qur'ani sauran littafai ya Durfafa kowa ya san shi yana da Saukakkiyar Rayuwa. A kallo daya in kayi masa bazaka ce yana da wani gata ba saboda yana Daidaita Rayuwarsa daidai da ta kowa. An sha Fama da shi akan ya je waje ya yi karatun Likitanci ammh Sadiq fur yace baya Ra'ayi shi Quantity Surveying zai karanta masu kula da harkan Shimfid'a tituna kuma kowa yasan Ra'ayin shi ne gaba da na kowa hatta da Abba da Innani.

Suna ji suna gani ya tattara kayansu ya tafi zariya, in da ya samu Admission a ABU ZARIA zai karanta Ra'ayinsa.
Abba ya so ya kama masa gida ya zauna yace baya so a Hostel zai zauna cikin Dalibai yan'uwansa.
Wannan shine Mafarin Haduwarsa da Tahir kenan.
Tahir ya zo daga Daura ne d'an talakawa maraya da taimakon yayyensa da Kakarsa ya samu makarantar, Daki daya suke mafarin Zamansu kuma abokai duk cikin Dakin Sadiq ya fahimci Tahir ya fi su maida kai ga karatu, Su hudu ne Shi da Tahir sai Jabir sai Usman Muhammad Balarabe Mb kenan.
To har gwara Usman akan Jb da shima yaron mai kudi ne babanshi dan siyasa ne, kuma daga kano yake daga ganinsa zakasan ba karatu ya zo yi ba illah Shagala.
Da Farko Sadiq da Tahir fad'a suke yi kan gyaran Daki Tunda Sadiq baya son yaga Shirgi a Daki yana son Tsafta daga baya kuma sai suka zama abokai duk da ba Course daya suke karanta ba.
Cikin Lokaci kadan suka Fahimci Hallayan juna. Suna shekara ta uku Jb ya bar Dakinsu ya koma ya kama daki a wajen makaranta yana cigaba da watsewarsa.
Sadiq ya yi suna Abu zaria saboda Tausayinsa da taimakonsa Abba ya sha Biyama Dalibai kudin makaranta bai san iyaka ba. Sai dai Sadiq ya kirashi yace"Abba akwai wani a makarantarmu bai biya kudin makaranta ba  gashi za'a fara Jarabawa. Abba zamu taimaka masa."
Abba ba shi da mgana illah yace"Za'a taimaka musu Magaji gida zamu taimaka musu in sha Allahu"
Tahir ko da Usman shekaran ta kusa da ta karshe  duk Sadiq yasa Abba ya Biya musu kudin makaranta. Shi Usman dan gangare ne, yana da kokari sosai phamarcy ya karanta da suka gama ya samu Scoolarship zuwa kasar Ughanda domin cigaba da karatunsa.

Rabuwarsu kenan, Jb kuma daman Sadiq ya yanke alaqan sa da Jb Tahir ne ya kasa Rabuwa da shi.
Sadiq akan kirashi da sunan Alarammah Saboda Addininsa sannan masanin Qur'ani ne da Sauran littafai kuma yana cikin malaman MSS na makaranta yana kuma limanci a masallacin makaranta, Sannan duk karattukan da ake yi da Sadiq a ke shi Yazo karatun boko ammh kuma ya samu har da karin na addini kuma in ya koma gida Hutu ya rika Daukan Wajen Mallam Taju.
Sadiq ba bu abunda ya taba nema  ya rasa a makaranta sai dai ma ya kyautar shine siyama marasa karfi Handout sannan ya dinga Rabon kayan abincinsa ga duk wanda yasan yana Bukata. Sadiq tausayinsa ga Mutane mai yawa ne.
Duk da Abba da mako da son abun duniya ammh Sanadin Sadiq yasa ya ke alheri a chan Shinkafi sai kiga Mutum na da lambar Sadiq ammh kuma ba shi ta Abba. Saboda abunda Sadiq zai yi maka Abba bazai iya yi maka ba shiyasa shi ba iya magajin gida ya ke ba,  shi magajin kowa ne.
Shi kuma yasa Abba ya jawo yan'uwansa ajiki ya kuma ba da Kofar kowa na zuwa gidan Abba ayi zumumci.
Shi kuma ya saka Tsarin zuwa Shinkafi zumunci da kuma in sha'ani ya tashi Duk bala'in Innani bata iya ma Magajin gida shi ma kuma ya Fahimci har da Jahilci ke damun Innani shiyasa ya ke kokarin Gyara mata in tayi kuskure.
Maganar auran sa da Sultana kuma Umarnin Umma ce, Sannan Innani ta Dora Burinta shi kuma Umma da Innani suna da Daraja a wajensa shiyasa batare da Tunanin watarana zai iya shiga tsaka mai wuya ba ya amince.

Sultana ta taso ne da mganar Sadiq shine mijinta a bakin kowa. Yarinya ce shiyasa ba zata daura mizanin komai a yanzu ba ammh Abu daya ta sani Sadiq shine mijin da kowa yasan zata aura hatta iyayenta sun sani da Yan'uwanta, ta na zuwa Hutu ganin su ammh fa In innani ta yi ra'ayi har a yanzu Innani Tsine ma Shitu ta ke yi tace bakincikinsa da na matansa ya yi Sanadiyar Rasuwar Hauwa kulu.
Sadiq ya zabi ya yi karatu a zariya saboda Dalilinsa na zama in da Mutane ke harkokinsa  ya yi kuma rayuwarsa kamar yadda daidai da yanayin da ya ke so Rayuwarsa ta kasance sannan ya zabi zama a Hostel saboda halinsa na son Mutame da mu'amala in da Mutane suka fi yawan zama.
Chapter 34 · 0% Book details