Sashe 42
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tausayamin. Na tsugunna na Rufe kirjina ina kuka ina Fad'in"Wlh ni ba mayya ba ce.". Wani Saurayi yace"Ki ta shi ki Tsallakata sai mu tabbatar da ke ba Mayya bace" Ban yi shawara da kowa ba na mike ina Duke jikina na tsallaka matar nan dake numfarfashi. Ba ta tashi ba suka ce sai na kara na kara shima bata tashi ba. Suka ce sai na kara cikin ikon Allah ina kara yin na uku sai gata ta mike ta na faman zare ido ganin Mutane a kanta yasa ta ke fad'in"lafiya me ya faru.? Kawai wajen ya Rud'e da Hayaniyar "Laa! Wlh da gaske Mayya ce." Ko kafin na yi wani yinkuru sun Rufeni da Duka Inna Talatu ta fita da Gudu waje tana neman agajin jama'a. Adda Rukayya ta shiga cikin su tana Ihu ta na Fad'in"Kai kai ku bari mana." Ramatu ko wayarta ta Dauko ta Kira mijinta ita kanta garin kareni dukanta ake yi Noor sai sai Faman Tsala kuka take yi. Inna talatu na Kofar gida ta ga zuwan Mijin Adda Rukkayya a mota. Daman yana Hanya zuwa ne bai ga ko kiran Adda Rukayyan ba inna Talatu ta nufe shi cikin tashin Hankali tana fadin"Za su yi kisa wlh zasu kasheta." Hankalin sa ya tashi jin hayaniya ya Fad'a gidan a guje. Shi kanshi ya shiga Tashin hankali ganin gida cike da mata da Maza daman tare ya ke da abokinshi. Adda Rukayya na ganinshi ta Nufeshi ta na kuka fad'i ta ke yi"Wlh wani abu ya samu Hasiya ba ni ba kai har Abada Adamu." Bai tsaya jin ba'asi ba suka fara watse taron da Kai kai ku bari mana Jumai da Zainab sun fi kowa zakewa wajen dukana. Baban Amna da Abokinsa suka kwaceni lokacin sun gama Min lilis bakina da jini hancina na jini kaina daga goshi na sun fasamin har da masu tsigemin gashin kaina. Sun samu nasaran balle zaren bra dina ta baya Dalilin da yasa na kwanta a kasa na Rufe kirjina da Hannayena ina wani irin kuka mai Cin rai kamar ba ni ba. Baban Amna yace"Subhanallah.." Ramatu ta kwance Noor ta zo ta lullunbamin zanin goyon nata Adda Fati kuma ta cire hijabinta ta Dagoni ta sakamin ta na kuka. Baban Amna yace"Meke faruwa ne?miye haka..? Nan zainab ta shiga warware masa komai ta karishe da fad'in"Ladidi fa ta kama sai da muka sakata ta tsallaketa sau uku sai ga shi ta tashi." Ladidi cikin mamaki tace"Ni fa Inaga Lalurata ce ta tashi. Ina da Aljanu kuma suna yawan bugeni na Fad'i." Sai wajen ya yi shuru. Baban Amna yace"fisabillahi me ye haka.? Sai ku ce ta tafi gida menene amfanin wannan tozarcin? Ni dai kuka kawai na ke yi, Ramatu ta kalli Inna Talatu ta na Fad'in"Inna Nura yazo zan tafi da Hasiya na wuce da ita gidana.? Inna Talatu tace"Eh kada ta koma ta tadama Amma hankali kuje chan gidan ki kawai." Ta amsa da Toh Adda Fati da Habiba suka taikamin na tashi zanin goyon noor na yi Daure gaba da shi, na saka Hijabin Adda Fati dakyar na ke tafiya Fuskata ta Suntuma saboda duka. Adda Rukkaya kuwa fad'i ta ke yi"Wlh ni kuka Tozarta. Ba dai ni zaku yi ma wannan Tozarcin ba.! Ta ke fad'a cikin Tsawa da karaji. Ba wanda ya kulata sai mijinta da ke ta ce ma Inna talatu ayi hakuri. Ko tankashi ba wanda ya yi tunda yana mganar da an koreni ne ba sai an Dakeni ba kenan shima ya amince da komai da ake fad'a kaina. Nura da mai adaidata yazo Tunda Ramatu tace yazo da abun hawa. Nura sai sallalami ya ke yi yana Fadin"Inna yanzu haka Mutane suka zama Jahilai.? Miye haka don girman Allah." Inna Talatu ta girgiza kai ta ma kasa mgana kafata ba ko takalmi ana ta kai wa ke ta kaya. Dagani sai Ramatu muka shiga cikin Adaidata muka tafi Inna Talatu tace yanzu suma zasu tafi chan gida. Abunda ba su sani ba Tuni su Maman salihu sun zame jiki sun koma gida sun kai Amma Labarin duk abunda ya Faru. Suma muna wucewa ba su koma gidan ba suka wuce sun ma mamta da wasu mutanen gidanmu tashin Hankalin da suke ciki ya ishe su. Suna Hanya Inna Talatu na Tunanin me zasu Fad'a Amma in ta tambaye su ni? Adda Fati tace"Mu ce kawai ta na gidan Ramatu zata kwana biyu" Inna Talatu ta girgiza kai kawai tana Uhm.! Kai jama'a. Ni ko muna tafiya ina ta kuka , kuka da Karfi kamar zan Tsaga Adaidaitan Nura na gaba sai juyowa ya ke yi yana Fadin"ki lallasheta ke kuma mana.." Ramatu na matsan kwallah tace"Ba ni da sauran kalamai Nura a gaban idona aka Tozarta Hasiya kan kaddaran da ba ita ke da iko a kan shi ba." Nura yace"Ni kaina abun ya Tab'ani wlh wai ya abun ya faru ne.? Cikin Damuwa ta fara ba shi labari. Ya saka Salati yana fad'in"Kamar wasu Jahilai." Mai adaidaitan da muke ciki yace"ai yanzu mutane sai Allah ba su da yarda da Allah komai ya faru da Mutum sai kaji ana Fadin jifa ne. Wannan Dabi'ar ta canfe canfe wlh ana Fama da ita yanzu nima akwai wata yar'uwata da tayi aure mijinta ya Talauce ya yi ta shiga bala'i itama a karshe an ce Farar kafa gareta ya sakota wajen shekara tara kenan duk wanda yazo neman auranta da ya samu wannan Labarin baya Tsayawaa. Sun kasa gane mutum bai isa ya san gaibu ba. Allah ke da arziki da Talauci." Nura yace"Rashin yarda da Kaddara ne. Shi kuma rashin yarda da Kaddara Daidai ya ke da rashin yarda da Ubangiji. Mutum bai isa ya yi ma Mutum abunda Allah bai yi masa ba." Mai adaidaita yace"Sosai ka ga anan wajen Tauhidi ya raunana. Sannan kuma a musulunci babu maita babu kuma Canfi ammh Mutanen wannam zamanin basa ganewa komai ya Faru da Mutum sai kiji ance ba Daga Allah ba ne akwai sanadi." Nura ya gyad'a kai kafin yace"Abunda ke Faruwa kenan. Kuma malamai na iya bakin kokarin su mutane basa ji kwata kwata." Mai adaidaita yace"Yanzu ai ko mutuwa ba ta zame ma Mutane wa'azi ba. kaga kuwa tunda Mutuwa ba ta zame mana wa'azi ba wlh tallahi ba bu abunda zai zama aya kuma agaremu." Ina jin su suna ta mganganunsu su da suka gane haka kenan su ke kuma Fad'in haka. Muryata bud'e na ke kuka kukan bakincikin yadda aka yi min Tsirara gaban Mutane. Ganin zamu tsaya gidan Ramatu yasa cikin kuka nace"Ku kaini gida. Don Allah ku kaini gida." Ramatu tace"Amma Hasiya" Cikin kuka nace"gida zan je Ramatu..na ce miki gida zan tafi." Na fad'a cikin karaji da kuka Nura ne yace mu tafi gidan gabadaya. Ni dai tunda na ganmu a kofar gidanmu ban tsaya jiran Ramatu ba na Diro daga adaidaita. Ko ganin gabana ba na yi kafata ta yi tsami ina dingishi. Fuskata ta sumtuma ga jini duk ya bata gaban hijabin da na saka ba Takalmi haka na Fad'a cikin gidan cikin kuka da Muryan karaji na ke kwalama Amma kira. Wacce daman tun sanda su Maman Salihi suka zo da Labarin Amma ta kasa zama adaki tana Tsakar gida tana Safa da marwa labari kuma ya shiga kunnen matan gidanmu suna Tsaye cirko cirko. Ina shigowa na zube gaban Amma ina wani irin kuka. Amma jikinta ya fara rawa ta durkushe itama a gabana ta na Fad'in"Hasbunallahi wani'imal wakeel Hasiya yanzu abunda suka yi miki kenan.? Itama sai kuka, daidai lokacin da Ramatu da Nura suka shigo. Ni ko fad'i na ke yi"Amma menene laifina? Wani abu na aikata da na chanchanci shiga cikin wannan matsanancin tsaka mai wuyan? Amma na tsiyayan Hawaye tace"Ba ki da wani laifi Hasiya. Ba ki da laifi har a wajen Ubangiji." Cikin kuka na ce"Amma da gaske to ni Mayya ce? Da Sauri Amma tace"Wlh ke ba mayya bace, kaf zuru'armu ba mu da maita haka zuru'ar mahaifin ku. Ba ki gada ba sannan baki siya ba Hasiya." Ina rike hannun Amma nace"To miyesa haka ke faruwa da ni? Farko Abubakar daga baya Salisu Amma.? Me yasa.? Me ke faruwa da Rayuwata ne..? Na karishe fad'a ina jin Numfashina na cijewa ya na sama da kasa kamar zai yanke. Cikin kuka Amma ta rikeni ta na fad'in"Bansani ba Hasiya. Abu daya na sani ke mutum ce kamar kowa. Baki da bakin fenti a tare da ke, Komai da ke faruwa Hukuncin Allah ne da mutum bai isa ya ja da shi ba." Amma na mgana ina jin amai na tasomin na fara tari ina rike kirjina Lokaci d'aya ina fadin"Amma kirjina, Mutwa zan yi ko? Dama na Mutu na Huta." Sai amai na fara kelaya shi a jikin Amma ina wani irin rawan jiki kamar zan mutu.