← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 69

Sashe 30

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Lokacin Sadiq ya yi mgana cikin Halin ko in kula yace"Yauwa Umma Fad'a musu ba mai zab'amin abunda zan ci, cikina ne rayuwata ne ok.! Sannan in kun ga na baro Garin Zariya na gama abunda ya kaini ne sai ko in mutuwa."
Kawai sai ji akayi Innani ta fashe da kuka Tana fadin"Allah ya tsine ma duk wanda ke jifan jikina da kalmar mutuwa. Sulaimanu ba shi da wani magaji yau in magajin gida ya mutu ina zamu saka kanmu.?
Allah dai ya tsine ma duk mai yi masa fatan Mutuwa akansa wlh."
Ta karishe fad'a lokaci daya kukan nata ya Dauke ai sai falon ya dau shuru kada wata ta tofa Innani ta Sauke mata Tsine tsinen da ke bakinta.
Sai Dakyar Sadiq ya lallabata ta yi shuru ta hakura, Shima tunda ya ce bazai bari ba suka kyaleshi sanin Halinsa na kafiya da Shegen girmama Ra'ayinsa saman na kowa.
Hira suka cigaba da yi na zumunci sallar la'asar kadai ya ta da su kafin nan sun yi masa bakin me zasu kawo masa? Kowacce na masa magiyan ya kawo mata ziyara kafin ya tafi tare da Tambayanshi me dame me dame zasu had'a masa in zai koma?
Kai tsaye yace"Kowa ya san abunda na fiso ko?
Salima ta yi tsalle tace"Nama."
Suka saka Dariya gabadaya su san Sadiq kamar kura ya ke wajen cin Nama.
Innani ce ta fattakesu da Masifarta fad'i ta ke yi"Kai dilla kowacce ta ja ya'yanta ta tafi gidan mijinta kun zo kun cikama D'ana gida zaku cinyemasa dan abunda ya tara to shima ba shi da komai Rufin asirin Allah ne"
Surayya tace"Innani ke fa ki rika kiran mu kina fadi'n mu zo ga magajin gida yazo sannan yanzu kuma munzo, kina korarmu"
Innani tace"fisabilillah an yi na mutumci da arziki. Ba sai ku tattara ya'yan ku ku tafi ba? To billahillazi in ma bazaku tafi ba ku fice min daga Shashena kun isheni yarinyar nan Sulsana na so ta kebe da magajin gida kun bi kun kankane, ku fa wani Lokacin girma ne kawai ammh ba ku da wayau kwata kwata ba ku san ya kamata ba"
Ta fad'a ko ajikinta ta na kara ma zaman gilashinta zama a idanuwanta.
Sultana da ke gefenta ta Dago a tsorace ta kalleta baki Bude tace"Innani.."
Innani ta juyo a masifan ce ta na Fad'in"Innani me? Don ubanki ai ba karya na yi miki ba? In ba mgana kike son yi da shi ba uban kike min a baya kamar wata yarinya? Ko ni ce uwarki? Ba ga salamatu chan ba meyasa baki je kin nanike ta ba. ni tashi daga baya na tsufa haba fisabillahi ai na yi wahala da ya'yana ya isa haka wani shegen jika ya yi ta kansa ni ma ta kaina nake yi."
Ga dariya ba Halin ka yi Dariya Salima ta saki dariyanta ganin yadda Sultana ta yi kamar kazar da aka Tsoma a ruwan zafi da Innani ta Tureta.
Innani ta ji tashin Dariya ta Daga Sandar ta tana fadin"Wata shegiyar ce ina mgana ta na min Dariya?
Salima ta Rufe baki tana zaro ido aka yi shuru ba wanda ya tanka ta Surayya taje ta dago Sultana da har ta fara hawaye ta riko hannunta tana Fadin"Karki damu da Innani an juma sai tayi cigiyarki.."
Innani taji an yi banza da ita ana ta mgana sai kawai ta karkace baki kafin tace"Ko wacece ta yi dariya nan Allah ya tsine.."

"Innani.."

Sadiq ya katseta da karfi jin Muryansa yasa ta yi shuru ta kama Jan hanci kamar zatayi kuka ta na Fad'in"yaran nan na sulaimanu na arzikin dai duk sun kare yanzu duk diyan banza ne"
Sadiq ya bude muryansa ya na Fad'in"Innani wlh in na fita daga Shashen nan har na koma bazan kara dawowa ba. Sau na wa zan hanaki tsine tsine nan? Ki na ta aibata jikokin ki da kanki..?
Sai Innani ta kasa mgana, jin ya yi shuru yasa ta dago ta na kallonsa kafin tace"Ka yi hakuri magajin gida Raina ne ya baci. Ka yi hakuri in ka gujeni ina zan saka raina ni Dije ba ni da kowa sai kai anan duniya nan"
Kai Tsaye yace"Ba ki na da D'a ba. ga Abba nan mu ba kin gama tsine ma na ba?
Da sauri Innani tace"Wlh ban tsine muku ba. Dukkan ku ya'yan nan Allah ya yi muku albarka ya tsare gabanku da bayanku ya kare min ku. Allah ya shirya muku zuru'an ku gabadaya."
Sadiq ya yi mirmishi ya karisa gaban innani ya zauna ya Rungumota yana Fadin"Ameen Ameen Innani na."
Suma Sauran da Ameen suka amsa saboda Sadiq an samu Innani na ta zabga musu addu'o'i kafin su fita daga Shashenta dukkansu sai da suka sauke mata kudade Inanni na Hawaye tana fadin"Kai duka ya'yan Sulaimanu yan albarka ne. Allah dai ya yi muku albarka ya kare ku da Sharrin makiya.    
Ke sulsana ina kike ki kirgamin kudin nan muga nawa na samu?
Surraya tace"Innani wata Sulsanan? Wacce kika ture kika kora.?
Innani tace"Kaji sharri da karya abakin manya ni Dije yaushe na Taba Sulsana? Kai Saddiqu maza kaje ka tahomin da Matarka nan"
Ba shi da mafita illah yace mata toh ficewa suka yi suka barta da Siyama itama din Innani sai fad'a take yi tana Fadin'Uban wa yace ki zauna min afalo? Ni fa Sulsana nace magajin gida ya kirata so na ke yi su samu kebewa tunda dai nan da wata Shekaran zan ce Sulaimanu ya yi musu aure nagaji da ganin wannan watsewar aciikin gidan D'ana yara sai rashin kunya da Rashin Tarbiya gwara kowwcce tayi ta kanta shima d'ana ya yi ta kansa"
Siyama dai karshenta Fattakanta Innani ta yi ta fito tana fadin"Ga shi nan kici falon gabadaya. In ma kin kara ganin kafata."
Innani ta Daga sandarta tana Fadin"In kika kara Dawowa sai na ci Ubanki. Lallataciyar yarinya mara tarbiya kawai. Kai Suwaiba dai bata iya Haihuwa ba duk ya'yanta ne suka batamin zuru'ar d'ana."
Kowacce shashen uwarta ta shige kafin mangriba Sakina da Shahida suka hau motocin su suka tafi,bayan mangariba kuma Surayya da Sa'ima da Sadiya ma suka tafi da cewa gobe Zai ga Sakon su.

Shi daman ya na waje tare da Mallam Tajudden suna karatun Bukhari da Musulim, Mallam Tajuddeen malami ne sosai mahaddaci masanin Hadisa shiyasa Sadiq in dai yana gida baya wasa da daukan karatu a wajensa.
Tahir na cikin Shashensa yana fama da waya bai ma gayyacesa ba sanin Halinsa.
Suna karatu karnukan Abba suna Damunsu da Haushi Sadiq ya kalli Mallam Tajudden kafin yace"Abba bai rage karnukan ba ko?
Mallam Tajudden yace"an fita da wad'anda ka sani wad'anan manya ne guda biyu aka kawo su kwanaki."
Shuru ya yi bai yi mgana ba ba domin Hujjar Abba ba. Da bazai bari ya ijiye karunuka a cikin gida ba.
Sai da aka kira sallar Isha'i sannan suka Rufe karatun alwala suka Daura suka fita zuwa masallaci nan kusa da su.
Bayan sun dawone suka yi musabaha tare da sallama Mallam Tajudden ya shige muhallinsa shi ma Sadiq ya koma shashensa. Ya na shiga ya ga Tahir rashe rashe kan kujera ga basket din abinci nan a gabansa ya ci duk ya watse komai. Kuma ya kure karan Tv kuma alokaci daya yana amfani da waya..
Sanye Sadiq ya ke da Jallabiya Mai ruwan kasa da Hula. Hannunsa kuma littafin bukhari da Musulim ne a Hannunsa. Yana shigowa kallo daya ya yi ma Tahir ya Dauke kanshi kafin ya cigaba da Tafiya zuwa Bedroom dinsa.
Kamar daga Sama yaji Tahir na Fad'in"Alarammah barka da Dawowa."
Sadiq ya juyo kafin yace"Yauwa. Ka yi sallah?
Tahir yace"Wace sallar?
Kai Tsaye Sadiq yace"Isha'i.."
Sai Tahir ya zaro ido kafin yace"Wai kana nufin har an yi isha'i.?
Sadiq ya yi karamin tsaki kafin yace"Ana ta jiran ka Tahir kaji ana ta jiran ka. Ka na da rauni wajen ibada ammh wajen Shagalan duniya baka da wannan Raunin Tahir ka gyara ka gyara Rayuwarka."
Tahir ya yi dariya kafin yace"Ka na ba ni mamaki ko da yaushe sai ka na mganar na gyara Rayuwata?. Shin rayuwata ba ta  akan hanya ne ko ya ya?
Sadiq haushi yasa bai kara mgana ba ya Juya ciki ya na ji Tahir na Fadin"Naji yanzu zan ta shi nayi shikenan".
Shi dai Shigewarsa ciki ya yi ya adana Littafinsa a muhallinsa. Wanka ya shiga bayan ya fito ne Tahir ya shigo ya shiga ya yi alwala sama sama ya yi sallar tasa kamar yadda ya Saba ya fita ya koma Falo kan waya kai kawai ya girgiza Tahir sai Allah kawai.
Riga da wando ya saka Fari da baki yana son ganin Abba Kafin ya kwanta akwai mganar da ya ke so su yi.
Falo ya fito kujeran da ke fuskantar Tahir ya jawo basket din gabansa.
Pepe kitchen din da akayi domin sa ya ci duk da Tahir ya ci ammh ko Rabi bai ci ba naman kawai ya ci ya kora da lemu ya yi hamdala. kayan da Tahir ya bata duk shi ya tattara ya ijiyeshi nan gefe yasan su siyama zasu zo su dauka.
Sai alokacin ya Dauki wayarsa ya na Dubawa. shi waya ya Dauketa kawai a kira ka kira Mutum ba shi da Juriyan Chart gwara ma karanta labaran abunda ke Faruwa. Ammh Tahir har mamaki ya ke ba shi baya gajiya Tahir na daga cikin mutanen da waya ta ke hanasu koomai ciki har da cikakkiyar Ibada ta shiga ransu da ta sanya suka Shagala.

"JB na gaishe ka.."
Chapter 30 · 0% Book details