Sashe 65
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau tun safe da Fad'uwar gaba na tashi ko mgana akayi sai naji gabana ya ba da wani Ras! Har sai na fad'a ma Amma tace na karanta Falaqi da nasi da Ayatul kursuyi kafa uku uku da Amanar Rasuli. Shawaranta na bi na karanta sai abun ya yi sauki ammh Suku suku na tashi har ina zaton ko Ulcer dina ce ta tashi jin baya na da kugu duk ya rike, Kuma da Safen na sha mgani ammh jikina kamar an yi min duka ko Amma ta fi ni karfi da Kuzari.
Ita na kai ma ruwa ta yi wanka ni ce ban yi ba saboda naji ba na ra'ayi. Da Safe kunu na dama muka sha da rana kuma na siyo mana Alala. Shiyasa na yini kwance kamar ruwa Amma dai har ta gaji ta kalleni bayan na idar da sallar la'asar taga na kara bin leda na kwanta tace"Hasiya lafiyar ki kuwa?
Ina daga kwance nace"Amma ni yau bansan me ya sameni ba. Faduwar gaba da mutuwar jiki."
Amma ta yi shuru kafin tace"To Allah ya sauwake."
Nace mata Ameen a Hankali.
Lumshe idanuwana nayi kamar baeci na son fizgata Amma na daga gefe ta na jan cashaba
Naji muryan Salihi ya fad'o dakin mu ya na fad'in"Adda Hasiya ga mai siyan Danwaken nan da safe, a waje ya ce ki zo."
Sai naji kamar a mafarki naji mganar da Sauri na Bude idanuwana.
Sai dai ban tashi ba sai da naji Amma na fad'in"Ke Hasiya Abubakar ne inaga"
Sannan na yi zaraf na mike jikina ba inda baya rawa. Da Hijabin da nayi sallah takalman Amma silafas na wajen na zura na fice da gudu.
Ban zarce ko'ina ba sai kofar gida Fata na da Muradina na ci karo da abunda Zuciyata ta gama yanke kauna da sake gani.
Shi ne ko yana Tsaye daga gefe rike da Hannun Datti da ya ke ta zuba masa uban surutu.
Ganin fitowata da yadda naja na tsaya ina kallonsa ko Kiftawa ba na yi yasa ya zaro walet dinsa ya Dauko 200 ya bama Datti ya karb'a ya na ta washe baki da tsalle ya shige cikin gida.
Da kansa ya kariso gabana hannuwansa duka zube cikin Aljihun wandon da ke jikinsa.
Kallonsa na ke yi ko kiftawa ba na yi kamar wacce ta warke makanta.
Shi kuma ganin haka yasa ya ciro hannunsa guda d'aya ya murza a saman Fuskata lokaci d'aya ya na fadin"Kin yi mamakin ganina ne?
Da sauri na Dawo hayyacina sai kuma naji dariya ta kwacemin.
Shima Mirmishin ya yi kafin yace"Baki zata zan dawo kwanakin nan ba ko? Daman nace miki bazan wuce sati biyu ba in ma na wuce bazan kai uku ba"
Cikin shagwaban da bansan sadda ta kwace min ba nace"Ban zata zan sake ganinka ba ASSADIQ."
na fad'a idanuwana na kawo Ruwa kai Tsaye yace"Da sai ku tashi ku koma wani garin Batare da kun jirani ba HASIYA.?
Kallonsa na yi ina mamakin ina yaji labarin tashin mu sai ma Tuna Datti nasan bani da haufi shi ya fad'a masa.
Rufe fuskata na yi da Tafukan hannayena ina yar dariya wani Farincikin da bansan daga ina ya ke Tunkudo'wa daga kasan raina ba.
Cikin sanyin murya nace"Shiyasa muka kasa tafiya ko'ina har sai da ka dawo ka ganmu."
Kai ya jinjina kafin yace"Ina Amma? kanwata Habiba ta na lafiya?
Fuskata na bude ina fadin"Bismillah mu shiga."
Ina gaba ya na baya har zuwa Dakin Amma bayan ya gaisa da matan gidanmu.
Gulmammu kafim ma ya fara gaishe su su suke fara gaishe shi suna washe bakin munafunci da Gulma.
Amma ma bakinta yaki rufuwa ganinsa a gabanta a duke ya na gaisheta ta amsa ta na fad'in"Abubakar idanuwanka kenan?har na fidda rai da zamu sake Had'uwa ga shi Hasiya ba ta da lambar wayarka."
Kansa na kasa yace"Haka yaron chan ke fad'amin zaku tashi Amma"
Amma tace"Wlh kuwa ba domin an samu Tsaiko ba da tuni muna chan da yanzu baka same mu ba."
Cikin mamaki yace"Me nan gidan ya tada ku ne Amma.?
Amma ta girgiza kai kafin tace"A'a wlh. Mu zamu tashi da kanmu"
Shuru ya yi jin Amma bata warware mgana ba.
Ni ina daga gefe ina Sauraransu sai ya waiwayo ya na fadin"Habiba na makaranta ne?
Amma ce ta amsa shi da cewa"Habi ta koma wajen Fati da zama gabadaya."
Cikin mamaki yace"Me yasa Amma?
Sai da ta kalleni na wani Lokaci ni kuma sai na daga mata kai sannan ta jiya ta na fuskantansa tace"Saboda zamu koma mahaifata da zama gabadaya."
Sadiq ya dago ya na kallon Amma kafin yace"Ina kenan?
Amma tace"Gadan mallam Mamman chan hanyar kaduna zuwa Abuja."
Ni ya kallah kafin ya kalli Amma lokaci d'aya ya na fadin"Har da Hasiya?
Sai Amma ta kasa mgana Idanuwanta suka ci ko da kwallah. Ni ce na ba shi da amsa da cewa"Eh harda ni. Gidan Adda zamu koma yayar Amma ce can take da zama ita da iyalanta."
Gabadaya Dakin sai ya Dauki Shuru shi bai yi mgana ba nima ban kara mgana ba.
Kaina na kasa ina wasa da gefen Hijabin jikina kawai sai ji nayi Amma ta fashe da kuka da sauri na Dago ina kallonta a tare da ni da shi muka isa gabanta cikin rawan jiki da na murya muke tambayamta me ya faru?
Amma ta kalleni hawaye Jage jage haka shima ta juya ta na kallonsa ko Kiftawa ba ta yi na tsorata na kalleshi shima ya kalleni a tare muka Dora hanmu a kaf'adan Amma muka girgizata kuma bakin mu a tare ya Furta sunanta.
"AMMA.."
Kuma a tare hannumuwan mu suka had'u waje d'aya sai da muka ji wani Zir kamar wutar lantar yajamu da kuma Sauri muka saki hannun juna.
Amma ta kallemu kafin ta murmusa da haban zaninta take sharewa.
Ni kuma na durkusa gabanta ina fadin"Amma baki da lafiya ne?
Sai ta girgizamin kai shi kuma sai yace"Taba jikinta ko da zafi sai mu tafi asibiti."
Ba gaddama na taba goshinta naji sanyi sai na juya ina masa motsi da ido alamun lafiyanta kalau.
Kallona na maida kanta kafin nace"Amma me ya same ki?
Cikin mirmishin karfin Hali tace
"Bakomai Hasiya. Ina so ki bamu waje zan yi mgana da ABUBAKAR."
Dagani har shi juna muka kallah cikin mamaki kafin na kalli Amma zan yi mgana kenan tace"Gaddama ba Halin ki ba ne Hasiya kada ki fara Daga yau."
Jikina ne ya yi sanyi ina jin haka sai na mike shi na kallah shi kuma kansa na kasa daga gaban Amma inda ya Durkusa.
Har zan fice Amma ta kira sunana na waigo kafin tace"Matso ma da Abubakar Darduman nan ya zauna dakyau."
Ba musu ma matsar masa da shi gabansa yaja ya zauna ya tankwashe kafa ya na Fuskantar Amma.
Ni kuma sai na fita waje na koma bakin kofar Maman Salihi na zauna.
Wake take tsinta sai na saka hannu in tayata domin kada na zauna shuru Tunani ya yi min yawa.
Kallona ta yi kafin tace"Bakon ya tafi ne? Bakinta washe cikin basarwa nace"Suna mgana da Amma."
Sai ta shuru nima daganan ban kara mgana ba duk ko da suna sako ni cikin Hiransu sai kiji suna ko ba haka akayi ba Hasiya? Iyakata mgana da kai ko na yi gum suna ganina zaune ne ammh gabadaya Tunanina da Hankaluna suna dakin Amma ina Hasaso wani irin mgana ne Amma zata gayama Assadiq ya sa sai da tace na basu waje?
Wata zuciya tace ya wuce Labarin ki"
Daman nasan ai Tsatsuniyar gizo bata wuce ta kogi.
Har aka kira sallar mangariba Assadiq bai fito ba.
Ganin duk sun watse sun shige dakanunsu yasa na ari butar maman Boy na yi alwala na yi sallar mangariba adakinta.
Ina cikin azkar naji na kasa natsuwa a Daddafe na gama na mike na fita.
Ganin ba takalminsa kofar dakin Amma yasa nasan ya tafi.
Da sauri na fad'a dakin Amma sai na yi Turus ganinta ta na sallar mangariba.
gefenta na koma na zauna gabana naji ya na Di' di'
Bakina kuma ya kasa Furta komai.
*******
Tunda ya baro gidansu Hasiya ya fara ganin Duhu Duhu. Kansa ko da ya ke sara masa daman tun yana gaban Amma ya fara sara masa.
Ko da ya iso dakinsu jikinsa ne ya saki kwata kwata kwakwalwarsa ta daina amfani ballatana ta kaisa ga wani Tunani na Dabam.
Yaraf ya fad'a kan katifa ko takalminsa bai cire ba.
Tahir na Dakin Ammah ko kallo bai ishesa ba ballatana ya fahimci halin da ya shigo, ya na jinsa ya fita ya je ya yi alwala yazo ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci ammh shi duk yadda ya so ya yunkura ya mike domin ya fita ya Dauro alwala ya tafi masallaci ya kasa.
Gabbansa yaji kamar an sauke masa su ko'ina na jikinsa ya saki kamar ba shi da lakka ajikinsa.
Kansa na sara masa ammh kuma kwakwalwarsa ta tsaya cak din da ya kasa Dora wani sabon Tunanin tun bayan fitowarsa daga gidan su Hasiya.
Halin da ya ke ciki shi ake kira TSAKA MAI WUYA halin da ya kasa sarrafa Tunaninsa ma gabadaya.
Tahir sai da tara ta wuce ya shigo Dakin yana jin tashin muryansa a waje yana hira da yan makaranta da suke zaune tare.
Har kuma alokacin bai iya ko motsi da kafarsa ba. Yana jin Tahir har takasa ya yi ammh bai iya tashi ba.
Shi kuma Tahir haushin Sadiq yake ji shiyasa ya yi kamar bai gansa ba.
Da farko ya zata gajiya ce ta kwantar da shi sai da yaga bai je sallar mangariba sannan aka yi isha'i ma bai je ba sai yasan ba lafiya.
Lafiyar Sadiq kalau baya fashin sallah
Ko da ba shi da lafiya ne sai dai ciwon da ya kasa tashi shine zai hanasa zuwa masallaci.
Sannan ya shigo yagansa yarda ya barshi da gangan ya takashi Saboda ya yi mgana ya Fahimci Halin da yake ciki ya ji shuru daganan yasan ba lafiya
Kusa da Sadiq ya matsa ya na Taba kafarsa lokaci daya ya na kiran sunansa
"Sadiq Sadiq. Kai Sadiq"