← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 69

Sashe 67

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tabbas Hasiya ya gani da Tsohon ciki? Me wannan mafarkin ya ke nuna masa.
Wannan mafarkin ya na nuna masa Zahirin abunda zai faru matukar ya aminta da bukatar Amma zai rasa Sultana sannan zai rasa duka Ahalinsa gabadaya.
Sannan ya nuna masa amsa Bukatar Amma zai iya zama alheri garesa ammh kuma kafin cimma haka akwai tarin kalubale sannan zai iya jefa rayuwarsa cikin Tsaka mai wuya da Halin k'ak'ani k'ak'ani.
Ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya ya na Share zufan Goshinsa. Wayarsa da ke gefe ya laluba ya kunna sai yaga biyar da minti goma na asuba shiyasa yaji ana kiran salla a wasu masallatan.
Kansa ya koma ya dafe a fili ya sake Furta"Hasiya."
Wanda kamar acikin barci Tahir yaji sunansa ya mike a razane ya na fadin"sai naji kamar kana ambatan sunanta?
Ya fad'a ya na haske Sadiq din da fitila a saman gado sai kuma ya tsince shi shima a kasa kusa da shi.
Cikin alamun barci a idon Tahir yace"Sunan Zabiyar yarinyar nan naji kana ambata. Na shiga uku Allah yasa ba itace ta ka maka ka ke kwance ba Lafiya ba."
Cikin mamaki Sadiq yace"Ita wacece ta ka mani?
Tahir ya mike ya na mutseke ido kafin yace"Ita Hasiyar da naji ka na kira ko ba sunan wannan zabiyar yarinyar kenan ba.?

Karamin Tsaki Sadiq ya ja kafin ya yunkura ya mike Lokaci daya ya na Fad'in"Man ni naji sauki fa."
Tahir ya dafa sa lokaci d'aya ya na Tattaba goshinsa da wuyansa lokaci d'aya ya na fad'in"Eh naji jikin ka ba Zafi sosai kila taga bazaka ciwun mata ba ne yasa ta sake ka"
Sadiq ya kyalkyalce da Dariya lokaci d'aya ya na Dafe kansa saboda Saramai masa da ya yi.
Tahir ya kallah kafin yace"Tahir.. Tahir.."
Ya ke fad'a ya na kallonsa Tahir yace"Wlh da yanzu zan nemota duk inda ta ke ta tsallaka ka muguwa kawai."
Ya na wucewa wajen kayansa ya ce ma Tahir"Ba fa mayya bace Tahir. Kowa da irin tashi kaddaran"
Tahir ya karkace baki yace"Maita fa gaskiya ne."
Kai Tsaye Sadiq yace"bamu san maita a addininmu ba. Mu kambun baka kad'ai muka sani maita kuma da ka ke mgana duk Aljanu ne su ke yin abun su da aikin Tsaface tsaface irin nasu"

Daganan bai kara mgana ba ya Dauki Buta da Sauran ruwa ya bude kofa ya fice ya bar Tahir na mgana bai tsaya jinsa ba yasan ko kwana ya yi ya na mgana Tahir bazai aminta da mganarsa ba ya riga ya gama aminta da duk abunda aka Fad'a masa.
Shi kuma cikin bayanan Amma ya Fahimci Rayuwar Hasiya ba komai cikinta sai Kaddara da ke Dawainiya da ita haka Allah ya tsara mata komai in zai Faru da mutum daman akwai Sanadi.
Kuma ita sai ta kasance itace Sanadin na su kaddaran shiyasa ta ke Fuskatar kyama da Tsagwamma.

********

Na gama zura ma Amma ido ko zata min mganar abunda ta tattauna da Assadiq ammh kuma har muka yi shirin kwanciya ba ta ce min komai ba.
Sai da na yi mata shirin kwanciya sannan na zauna a gefen kafafunta ina Shafa mata man zafi a kafafunta tunda tace sun rike mata.
Ina cikin Shafa mata ina ta so na yi mata mgana ammh na kasa sai na yi kamar na yi mata mgana sai kuma na kasa.
Dakyar na yi karfin halin kiran sunanta"Amma.."
Ta amsa da cewa Umh. Kallonta na yi cikin wani yanayi kafin nace"Amma me kika fad'a ma Assadiq? a  kaina ne?
Amma ta yi shuru ta na kallona kafin tace"Me yasa ki ke son sani?
Kai Tsaye nace"Ina Son sani ne kawai Amma."
Mirmishi ta yi kafin ta Dafa kafad'ata ta na Fad'in"Kada ki damu. In abunda na rokesa ya ji rokona ya amshi Bukata ta zaki ji komai zuwa da Safe. In kuma bai amimce da Rokona ba har Abada bazaki taba sanin me muka Tattauna ba."
Cikin mamaki na kalleta kafin nace"Amma."
Kai ta gyad'amin tare da mirmishi da ya Kashe min baki.
A sanyaye na gama shafa mata man zafinta sannan na gyara mata kwanciya.
Hannuna ta rike ta na fad'in"Khairan in sha Allahu Hasiya."
Jinjina mata kai na yi batare da mganarta ta shiga jikina ba.
Mamaki na ke yi wata mgana ce wannan da Amma ta kasa Fad'amin?
Da farko na dauka Labarin abubuwan da suke faruwa da ni ne sai daga baya kuma na Fahimci wata mgana ne ta Dabam.

Barci na a ranar rabi da rabi ne duk sanda na farka sai na hangi Amma saman Darduma ta na sallah. Na fad'a daman ba ni da kokarin sallar Dare shiyasa har akayi asuba ban iya tashi ba har sai da Amma ta tasheni sannan na iya tashi ina kallonta ina jinjina abunda zai hanata barcin na tsawon Dare duk da nasanta ta na daga cikin mata masu kokarin Ibada ammh bata kaiwa har dare ya fara ya kare bata yi barci ba Sai zargina ya tabbata da cewa tabbas akwai wani abu da ke faruwa wanda bansani ba.
Jikina a sake na tashi da shi, Amma kuma ta lura ammh kuma ba ta min mgana ba sai dai na lura da wani abu tunda garin Allah ya waye Amma ke duban hanya kamar ta na jiran wani ko wata. da ta ji sallama sai ta leko har na nagaji nace mata wa ta ke nema tace min bakomai.
Cikin ikon Allah mun gama karyawa kenan sai ga Hamma Isuhu ya diro ba makawa tafiya ta tabbata a ranar kenan Tunda yace tare da wani mai Motar da zai daukan mana kaya suka Taho dagachan ya Dauko Itace ne zai shiga cikin gari ya sauke sannan sai yazo ya kwashemu mu da kayanmu.
Jin haka yasa Amma tace na kira su Adda na fad'a musu su zo mu yi sallama.
Da wayar Maman Boy na kira su, nace Adda Fati ta kira Inna Talatu da Ramatu ta sanar da su. Daganan sai na fara wanke yan kanukan da muka bata da Safe daman kayammu suna kammale waje d'aya.
Isuhu ko na ciki suna Hira da Amma na wani Lokaci kafin yace Amma bari ya shiga cikin gari ya dawo lokacin mun gama fitar da komai zai kira mai Motar in ya gama sai su dawo tare.
Na kasa Fahintar yanayin fuskar Amma a lokacin. Ta na dai zaune ta na jan Cashaba ni ce na ke kazar kazar ina had'a mana sauran kayan sawan mu da kayan amfanin da na fito da su.
Su Adda ba su tsaigaita nan da nan sai ga su sun taho cikin Damuwa da jimami.
Adda Rukayya ma ta riga Adda Fati zuwa ita da ya'yanta duka haka itama Adda Fati har da mijinta Inna Talatu ce ta zo daga baya sai Ramatu ma ta rigata zuwa.
Kowa kagani jikinsa duk ya yi sanyi na ganin tafiyar fa da gaske ne.
Ni na had'a gawayi na saka mana Ruwan zafi Amma ta fara yin wanka sannan ni nayi daga baya.
Na saka wani leshi na cikin kayan Abubakar ne mai Riga da zani, Amma kuma ta saka wata atamfarta da Adda Fati ta Dinka mata, ta kuma koma ta zauna ta cigaba da jan cashabanta duk hiran da su Adda ke yi bata saka musu baki ba.
Tuni har yan gidanmu sun aikama Makota cewa yau zamu tashi sai shigowa su ke suna mana sallama.
Ba wanda ya damu da yanayin Amma kowa ya na zaton cewa Saboda sabo me yasa jikinta duk ya yi sanyi ba ta walwala.

******

Ya gama Had'a duka Tunaninsa da Hangensa mafita d'aya ce kuma ita ya Tsaida har acikin ransa yasan Allah yaga kyakyawan Niyyarsa na Alheri da taimako kuma ya na da yakinin bazai barsa ya tabe ba.
Bai yi wani yunkuri ba sai da suka dawo sallar azahar shi da Tahir saboda saboda zazzabin da ya yi yasa shi bai je wajen aiki ba Tahir ma bai Fita ba.
Suna dawowa sallah daman akwai wuta ya saka ruwan wanka a Kittle sai da ya yi zafi sannan ya juyo ya yi wanka Tahir na kwance ya na ta Chart a wayarsa.
Sai da ya fito yaga ba shi da Niyyar tashi sannan ya ce masa bazai yi wanka ba ne?
Tahir ya dago ya na kallonsa kafin yace"Sai anjuma zan yi."
Sadiq ya kallesa kafin yace"Ka tashi ka yi zaka rakani wani waje ne."
Tahir yace"Ina.?
Sadiq sai ya yi masa banza bai yi mgana ba Tahir ya mike ya na mika kafin yace"Ka samu kanka kenan za'a fita?
Da Eh Sadiq ya amsa masa daidai Lokacin ya na bude akwatinsa.
Tahir shi kuma sai ya juyo ruwan da Sadiq ya saka masa shima ya fita zuwa wanka.

Ya yo wanka kenan ya shigo Dakin ya iske Sadiq ya ci gayunsa cikin wata shadda mai ruwan madara sabuwa ce ya na Tunanin ma bai taba sakata ba.
Abun mamakin har da Hula dara  mai yanayin aikin jikin kayan sannan ya sanya takalmi budadde na Fatar damisa sannan ya na tashin kamshin Turare.
Yana cikin karya Hulan kansa Tahir yace"Daurin aure zamu je ne?
Kai Tsaye Sadiq yace"Kamar ka sani."
Tahir yace"Ikon Allah Daurin aure ranar Laraba ko dai Bazawara ce.?
Kai Tsaye Sadiq yace"Eh.!"
Tahir ya tsaya ya na kallonsa kafin yace"Eh fa kenan bazawara ce? To kai ya aka yi ka santa?
Sadiq yace"Zan sani mana."
Tahir na goge jikinsa da Towel yace"Nagane kila abokin aiki ka ne ko?
Sadiq ya daga masa kai Lokaci d'aya ya na Dora wani brown din Agogo na Fata mai kyau da yarari lokaci d'aya ya na ce ma Tahir"Ka yi sauri.."
Tahir yace masa Toh yanzu zai shirya.
Jin haka yasa Sadiq yace bari yaje ya ciro kudi ya dawo fita ya yi ya ganganra bakin Titi wajen masu POS ya ciro kudi ya Tura cikin Aljihun wandonsa.
Chapter 67 · 0% Book details