← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 69

Sashe 45

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ba domin siyan wani abu ya fito ba iskar gari ya ke so ya shaka Tunda Tahir ya sauya iskar Dakin gabadaya.
Tafe ya ke kawai ya na kallon zirga zirgan Mutane kamar rana sai kuma yaji ya samu natsuwa har bakin Titi yaje sannan kuma ya sake kwana ya Juyo yana cikin tafiya ne ya hangi dandalin Samari a wani Rumfa sai da karisa yaga mai Shayi ne matasa da magidanta an taru ana ta shan Shayi ana Hiran Siyasa da yadda kasa ta ke ciki na Hauhawan man Fetur kowa na fad'in Ra'ayinsa.
Sai kawai yaji abun ya Burgesa Sallama ya yi musu suka amsa kafin ya ba su hannu dukkansu suka yi musabaha. Shima ya samu gefen wani matashi ya zauna.
Mai Shayin da bai taba ganinsa a wajen ba ya kariso ya na Fadin"Yallabai me za'a yi maka? Shayi ka ke so ko kwai za'a soya maka ko kuma wainar kwai?
Sadiq ya dago ya na kallonsa matashi ne ba Wani babba ba shi fa a Tunaninsa Masu yin shayi sai magidanta sai daga baya ya Fahimci matasa suma sun mike da neman na kansu. Saboda yadda Kasar tamu ta koma aikin Gwammati sai wane da wane.
Aljihunsa ya laluba ya ciro wallet dinsa duka duka 2k ne a ciki sai ya Dago ya na kallon mai shayin kafin yace"Tea zaka had'amin."
Sale mai Shayi ya ce"An gama yallabai sikari da yawa ? Madara ko melo?
Sadiq yace"Madara. Sugar din ba da yawa ba."
Ya juya kawai ya wuce wajen tukunyar Shayinsa.
Su kuma sauran suna ta labarinsu, acikin Hiran na su ne yaji wasu duk sun yi karatu ammh ba bu aikin yi sai Buga Buga mai shayi na Had'a masa Tea ya Daga Murya yana Fad'in"Yallabai a had'o da Buredi.?
Sadiq bai san ma da shi ake mgana ba sai da na kusa da shi ya tabashi sannan ya amsa masa da kadan ba da yawa ba.
Cikin Lokaci ya hado masa Tea dinsa mai kauri ya kawo masa. Ruwan ya yi zafi da ya sa yaji dadinsa ya gasa masa ciki. shi kanshi da ya kalli kansa a Teburin mai shayi sai da ya Murmusa Sadiq mai abun mamaki suna da kayan Tea a gida ammh sai yaji kamar yafi samun jin dadi da sukuni shan shayi a cikin Mutane daman haka ake ji? Abun mamaki ya sha da yawa kadan ya Rage saboda ya na sha ne ya na jin Hiran matasan da ke wajen. Anan kuma ya ke jin ashe Sale mai Shayi Degree garesa a BUK  ya yi karatu bai samu aiki ba ya fara sana'ar Shayi ya na Rufa ma kansa asiri da iyayensa.
Tambayan kudinsa ya yi aka gayamasa  600 sai ya ba shi Dubu Daya yace ya rike chanjin Sale na ta Godiya baisan ya Dauki Lokaci ba sai da ya Duba agogon wayarsa ya ga sha daya saura na Dare Dole ta sakashi ya mike ya yi ma matasan sallama ya wuce.
Tunda ya zo garin zariya bai taba wuce tara a waje ba. Ba shi da Dabi'ar yawo hatta Tahir da ke da Rawan kai baya yawo Tunda ba su san kowa a garin ba.

***

Bansan Lokacin da Barci ya kwasheni ba chan cikin barci naji Nishi da wani irin kakari.
Na mike a firgice jin Sautin daga wajen da Amma ke kwance ya ke fitowa da sauri na mike ina Fad'in"Amma. Amma.."
Na ke fad'a ina Yin kanta da Sauri na Dagota ammh ina Amma bata hayyacinta numfashinta na fita da Sauri Sauri jikinta ya Dauki Zafi sai makyarkyata ta ke yi kamar wacce aka Jona ma Shooking.
Bude Murya na yi ina Kiran sunanta Ammh ina Amma ba ta jina kamar ta yi nesa da Duniyarmu gabadaya. Jikinta ya saki Gabadaya ga Zufa na uban keto mata ta ko'ina.
Zufan da nagani da kuma nauyin da ta sakarmin yasa na Tsorata tunda na sha jin ance in mutum ya mutu ya na yin nauyi sannan ya na jikewa da Zufa ya yin Daukan rai sai na gigice.
Na fara girgiza Amma ina kiran sunanta cikin kuka da wani irin Tsoro ta ina zan iya daukan rasa Amma a wannan Lokacin?
Fadi' na ke yi"Amma don Allah kada ki mutu ki bar ni. Ka da ki tafi ki barni cikin wannan rayuwar ni kad'ai bazan iya ba. Wlh bazan iya ba."
Na ke fad'a ina kuka ammh sai naga kamar Amma ba ta Numfashi ji nayi zuciyata ta tsinke da Gudu na Saketa na fice ina haki nima kamar Shed'ata zata Dauke.
Dakin Maman Boy na tafi ina Bugawa Cikin kuka nake fad'in"Ku taimaka min Amma Amma kada ta mutu"
Duka Dakunan gidanan ba in da ban buga ba. Na tabbata in wasu ba su ji ba, wasu sun ji kuma lokacin dare bai Raba ba duk da ban kalli Lokaci ba ammh ba wanda ya fito ballatana ya taimakamin.
Ganin haka yasa na kwashi gudu na koma Daki na kara tarairayo Amma jikina na kara kunnena saitin zuciyarta ta ji dif kamar bata Numfashi, sai naji kamar wani abu ya Sare daga baya na. Tashi na yi ina Haki kafata ba takalmi zanin Amma na Raruma na yafa na fice daga Dakin da gidam ma gabadaya domin neman agajin nutane.
Chapter 45 · 0% Book details