Sashe 28
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ta na bin Tahir da kallo kafin ta yamutsa fusaka tace"Waye kuma wani Sahir? Sadiq na Dariya yace"Attahiru abokina Innani" Ai sai ta washe baki tana Fadin"A'a dan kwalba uba kace Attahiru naga ya yi wani fari ne kuma shine don sheganta bai zo ya rumgumeni mun yi masa Oyoyo ba." Sadiq ya kalli Tahir ya na Dariya Shima Dariyan ya ke ya Sauke Afiya ya Nufi Innami ya Rumgumeta yana Fadin"Allah ya bar mana Ran Innaninmu" Ta make kansa tana Fadin"Kaji dadin Tsokana ta ko" Dariya ya saka idanuwansa na kallon Sultana da ke bayan innani kanta na kasa ta na wasa da gefen Hijabinta. Da karfi yace"Sultana daman kina nan? Ya makaranta" Sai alokacin Sadiq ya ganta kallo Daya ya yi mata bai yi mamakin Tana wajen bai sani ba. Yarinyar ba ta da Hayaniya ko kadan. Yana mamakin yadda ta so ta zo daya ma da Innani. Sai a lokacin ta gaishe shi ya amsa cikin Sakewa kadahan kadahan. Ta kuma gaida Tahir ya amsa yana Tsokarta da Matarmu.. Tana jin haka ta ruga da gudu tana jin kunya Sadiq ya Take kafar Tahir yana Hararansa da ido shi ko ya yi kamar bai gani ba. Innani ta tattara su sai Shashenta bayan ta ce ma Siyama"Maza je ki gayama iyayen ki ga Magajin gida nan da Attahiru a kawo musu abinci. Ta juya ta na kallonsu suna zama a kujerun falonta domin Dakin Innani ko amarya ta sameshi to sai Hamdala. Sadiq ta kalla kafin tace"Magajin gida me zaka ci ne a kawo muku? Kai ne baka fadi kuna hanya ba da Tun Safe na hana kowa zaman lafiya a gidan nan" Sadiq yace"Innani sai anjuma ko zamu iya cin wani abu. Sai da muka karya sannan Hajja ta bari muka kamo Hanya" Innani ta washe baki tace"Shiyasa na ke kaunar kakar Attahiru. Ta na kular min da kai kamar yadda na ke kula da kai, To ya kuka baro su? Attahiru ya wajen yan'uwa ka na chan Dauran? Tahir ya bata amsa da suna gaisheta lokaci daya da Tura mata ledan gabansa yana Fad'in"Hajja tace a kawo muku Innani. Ayar ciki tace taki ce" Innani ta ja ledan ta kara gyara zaman gilashin idanuwamta Lokaci daya tana Fadin"Kai naji dadi kamar tasan ina son wasa hakora na kwanakinan" Sadiq ya kalleta yana mamakinta matar da kullum cikin cin nama take da kayan dadi ammh tana Fad'in kwana Biyu bata wasa hakora ba. To ina ma taga hakoran? Ta na washe bakin yaga na Robanta das a bakinta suka kalli juna da Tahir suka saka Dariya. Sultana kunya yasa ta kasa zuwa Falon Abba ta fad'a musu dawowan Yaya Sadiq sai Siyama ce taje ta Fad'a. Umma ta mike da Sauri ta na Fadin"Auta na yazo ganin gida kenan" Haka ma Abba ya mike har jikinsa na Rawa Fadi ya ke yi"Mun yi mgana da shi jiya kuma bai ce min zai zo ganin mu ba. Ke Suwaiba a shirya ma Magajin gida abun karyawa." Siyama ta yi saurin cewa"Abba shi da Ya Tahir ne" Abba na bin bayan Umma yace"To daman duk in da kika ga Magajin gidan zaki ga Attahiru a wajen.. ki yi kokari Suwaiba kafin Innani ta fara fadan an barsu da yunwa." Mama ta ce"To Alhaji ammh mu je nima mu gaisa da su. Siyama zata yi ma Salima mgana zata ji da abun karyawan na su" Abba yace"A'a ba na son korafin Innani kinsan Halinta kije kawai ki yi abunda na saka ki" Mama bata da mafita illa juyawa zuwa Shashenta tana Danne abunda ke ranta. Tana shiga ta ga Sa'ima da Salima suna Hira afalo ganin yanayinta yasa suka hada baki wajen fadin"Mama lafiya? Sai ta saki Fuska kafin tace"Magajin gida ya zo. Kuje shashen Innani ku gaisa da shi kafin kakarku ta fara tsinan ku." Salima ta mike da Sauri tana Fadin"Bros ya zo? Kafin mama ta kara mgana ta fice a guje Sa'ima ta mike ta na gyara Lullubinta tace"Mama bari na je mu gaisa da kanina na yi kewarsa sosai." Mama ta murmisa tana fadin"Ki turomin Siyama ta taimakamin wajen hada musu abun kari" Sa'ima ta amsa ta na Ficewa. Tunda Mama ke da girki sannan Ranar asabar da Lahadi yan aikin su basa zuwa tunda yaran nan na gida kuma a Tsarinsu a karshen sati duk mai girki ita zata yi da kanta saboda Alhaji na gida. Ko da Sa'ima ta isa Shashen Innani ta iske Abba rike da Hannun Sadiq kamar wani zai kwace sa gefensa Umma kuma ce ya d'ora kansa saman kafadanta ya narke kamar yaro. Gabansa kuma su siyama ne da Salima sai su Afiya kowa sai mgana ya ke yi Salima fadi ta ke yi"Yaya Sadiq tun wata daya da ya wuce na yi chart dinka a wsop baka duba ni ba" Ta fad'a cikin shagwaba Siyama kuma fadi take yi"Yaya Sadiq mu ma a siya mana waya ni da Sultana" Sai dai aka fadi Sultana ya Daga kai yana kallonta tana gefen Innani ta Rakube kanta kasa kamar wata marainiya. Tahir ya kallah da ke kallonsa gira ya daga masa shi kuma ya balla masa Harara. Innani sai msifa ta ke yi"Haba don Allah ku bar min jika ya Huta daga Dawowarsa kun fara damunsa da Korafe korafe." Sa'ima ta yi mirmishi sannan ta yi sallama Falon Innani Tunda ba wanda yasan da Tsayuwarta.. Tana shigowa Sadiq ya mike yana Fadin"Ya Sa'im" Kai tsaye ya mike ya Nufeta suka Rumgume juna cikin Farin ciki ta shafa kan shi tana Fad'in"Dan kanin mu min yi kewarka" Yana Dariya yace"Bakwa kai min ziyara Shiyasa" Ya fad'a cikin Shagwaba da Sauri tace"Kada ka damu zamu rika zuwa..Sannu da hanya Tahir sai tare da Sadiq muke ganinka ko? Tahir na mirmishi suka gaisa ta na masa Tsiyan baya zumunci sai da Sadiq ko. Umma da Abba bakinsu ya ki Rufuwa duk wani walwalan gidan Alhaji Sulaiman yana tafiya ne tare da Farincikin Abubakar Sadiq. Dakyar ya kwaci kansa zuwa Shashensa shi da Tahir suka yi wanka sannan suka kwanta su huta. Tahir na kwance saman makeken gadon Sadiq a cikin Bedroom dinsa. ya na kuma kare ma Dakin kallo ba bu abunda babu na more rayuwa. kaya ga su nan kala kala takalma shurfa ne guda kamar wadrope,Shi bai ga abunda Sadiq ya nema ya rasa ba abunda ma bai nema ba ya samu. Har cikin Bedroom dinsa akwai karamin Tibin bango bayan faskekiyar plasma da ke falo, Sadiq gajiya tasa ya fara barci shi kuma ya kasa sai kawai ya tashi ya koma falo ya yi flat saman Daya daga cikin kujerun Falon Sadiq bayan ya kunna kallo remot a hannunsa yana Sarrafa tashoshi. Iskar A.c na kala shi sanye yake da karamin wando da riga mara Hannu kayan Sadiq ne sabbi yana ma Tunanin bai Taba saka su ba. Yana nan kwance Siyama da Sultana suka shigo da basket cike da kayan karyawan su. Suka masa sannu da hutawa suka fita. Tarbiyan gidan su Sadiq mai kyau ce duk da sun taso cikin gata. Ko da Sadiq ya ke yayansu ba'a ba su daman su shigo shashen kai tsaye ba. yanzu ma sai da ya ba su izini sannan ba su zauna ba suna kawo abunda aka aikosu su ke tafiyarsu, gwarama yayenshi su Yaya Surayya su kan shigo su zauna ayi ta Hira.