Sashe 11
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba mu da kowa sai kawunan mu sai Allah, sai Adda fati da ta ke taimako mu, sai Inna talatu tunda Yayan Ramatu tela ne na mata kuma yana samu sosai, tabbas zaman su a gidan nan sun taimaka mana matuka. Adda Rukayya kuma ba ta cikin Lissafi ita wannan da ita da ba bu duk D'aya ne sai ta jima ba ta zo ba, in ma tazo ba ta zuwa da komai, matar da ko haihuwa zata yi sai dai ta kira kawayenta ko Dangin miji sai daga baya ma muke samun Labari. Adda fati ke zuwa ni tun sunan Yarta ta Biyu Madina. Da muka je dangin mijinta suka rika nuna ni suna mganganu. Har suna fad'in daga ganin fari na daman na cuta ne ba na lafiya ba, Allah ya sa ma ba maita na ke da shi ba, a gabanta kuma bata tsawarta ba Da Adda Fati ta yi mgana sai ta fara Fad'an in mun zo mu watse mata taro nata ne, mu kara gaba ta gode. Tundaga ranar ban kara kafafuwana ba su kara taka gidanta ba sai jikin Amma da ya tashi na je na gayamata ta fito ta ce min kada na kara zuwa saboda Mijinta ya ce ba ya son ina zuwa masa gida. Ba ni da Fad'a ina da mgana ni d'in ba Shuru Shuru ba ce sai dai na san a inda na ke yin sa, Ina da wani Hali na zuciya da Taurin kai ko dan'uwana ne ya nemi ya wulakanta ni ina janye jikina Daga garesa wulakanci ne babban abunda zaka yi min kaga bacin rai na. Ko ka taba Amma to a nan ne zaka ga ainihin wacece Hasiya Mamman kona. Bazan iya fad'in wani lokaci ne Abubakar ya shigo rayuwata ba. Ni dai nasan watarana na je kasuwa siyo ma Amma dawa da rogo na garin Danwake, muka had'u da shi a bakin Hanyar cikin motar abokinsa,ya yi min mgana ya nemi lambar wayata na ce masa ba ni da waya sai ya nemi na kwatanta masa gidanmu. Na kwatatan masa, a daran ya zo ya ganni mganarsa ta farko da bazan taba mantawa ba ita ce"Hasiya ni fa son ki na ke yi da gaskiya. Kuma in sha Allahu Auran ki zan yi" Tabbas mganganun sa sun yi tasiri a raina yadda ya ke d'an gayu dan boko dan gidan manyan mutane. Gidan su gidan arziki ne,tunda Mahaifinsa dan kasuwa ne shima Abubakar din Shaguna garesa na kayan yara a kasuwar sabon garin Zariya. Fari ne tas Bakano ne tunda Mahafinsa bakano ne mahaifiyarsa yar Danja ce da ke jahar katsina. Ni da bakina na fad'amai komai da ya danganci Rayuwata saboda naga kamar yanayinsa ya yi nisa da tawa rayuwar ammh ya ce yaji ya gani. Har ga Allah kyakyawan dabi'unsa mu'amalansa ya sa na fara son shi ban sani ba. Abubakar ya yi min komai a rayuwa in nace komai ina Nufin komai!. Ya so ni,ya kaunace ni a yadda na ke ya kuma toshe kunnuwansa da duk wasu suka ko yarfe a kaina shi dai ya ce yaji ya gani. Abun da ya yi min da har gobe na ke jin sa a raina ya Daraja abunda ya ke a kusa da ni. A lokacin ko ni ban kaisa kula da Lafiyar Amma ba. Ba ni da fargaba ciwon ta ya tashi Ina da Abubakar. Cikin Lokaci ya maidani mace mai aji da alfarma ya siyamin waya da kayan kwalliya da Suturu ban san iyaka ba. harta Kanwata Habiba yana yi mata Hidima Amma ko har yau ta na Daura d'aya daga cikin irin kayan da Abubakar kan siyo ya bata. Adda Fati har gobe ta kan ce bazata daina min bakincikin Rabuwa da Abubakar ba Masoyi ne da ya amsa sunan masoyi a gareni. Har gidanta mun sha zuwa tare, Har gadan mallam Mamman mun je na kai ma Adda shi sun gaisa ta na ta saka albarka bakinta ya ki rufuwa. Ban tab'a tunanin watarana soyayyata da Abubakar zai iya kasancewa a tsaka mai wuya ba. Na riga na gama sakin jiki da shi ban sani ba ashe sanda ya kai mgana ta gidansu a kayi bincike komai nawa sai da aka warware har da Kagen abunda ma bai faru ba. Mahaifiyarsa ta yi tsalle tace Allah ya tsareta Abubakar ya auro mai Farar kafa Rigima ta yi tsami domin Abubakar ya ce sai ni Hasiya. Gaddama ta farko da ya taba yi ma iyayen shi a kaina, ni bansan Halin da ake ciki ba tunda baya Fad'amin. Sai da Mahaifinshi ya tsawarta da mganar yace abunda Abubakar ya ke so shi za'ayi mishi. Shi ya jagoranci neman auran wajen Dangin Babbanmu Alhaji Tanko shi ya karbi mganar Tunda shi ne waliyin mu. Kuma ba kunya ba tsoron Allah. Ya ke karb'an mgana ba tare da sanin ya muke rayuwa ba. Ammh yana karb'an mganar ne sisin shi in bai ga Dama ba, bazai ba da ba. In sha'anin ya tashi matansa su zo in kuma bai ga dama ba, ba wanda muke gani. Ballatana ya'yan sa da suke ganin kansu suma wasu ne. An saka mana Rana da Abubakar wattani bakwai. Dalilin da ya kawo Kannen Abubakar gidan mu. Har tsakar gidanmu suka ci mana mutumci, sai ga sirrin mu A bakinsu suna mana maimaici. Sai alokacin nasan Dangin Abubakar ba su sona. Da nayi masa mgana sai yace kada na Damu shi dai yaji ya gani. Na tab'a masa tambayar "Haka zai aureni Ahalin ina da farar kafa? Kada wani abu ya same shi fa? Dariya ya yi kafin yace'"Farar kafa ba shi cikin addini ban yarda ba Hasiya ki bar ma wannan Tunanin Allah ne ya isa ya yi komai ba Mutum ba'" wannan yakinin na shi yasa na kara sakin jikina a kan Abubakar ballatana da Mahaifin shi ya zo har gida ya ba ma Amma Hakuri sannan ya Tursasama kannen Abubakar suka Dawo har gida suka ba ni Hakuri ni da Amma. Sai mgana ta wuce zukata suka samu natsuwa da kwanciyar Hankali. Komai da akayi min na aurena Amma ce da Adda Hari, sai Adda Fati da ni kaina Tunda ina samun kyatuttuka wajen Abubakar na kudi da Suturu, sannan ga Ramatu a gefe lokacin itama ta Had'u da Nura shima ba laifi yana sonta sannan Hidima Daidai misali ya na yi mata. Ga Inna talatu ita ce kamar Aminiya wajen Amman mu, an yi min kaya Daidai misali na yar talaka. Gidan da Abubakar ya na a Hanwa ne 2bedroom da falo sai kitchen an samu dai an yi min gado d'aya. Shi ne wajibi wadanda sukeje jere sun dawo suna Santin Muhallina. Akwatuna Bakwai Abubakar ya yi min shake da kayan alfarma kayan da aka jima ana zencen su a gidanmu da anguwan gabad'aya har ta da dangin baban mu da ban san ta ina labari ya je musu ba, sannan sunzo ganin ma idon su. Ko acikin Dakin ku akwai wada'anda basa son Cigaban ka. Irin Adda Rukayya ce kiri kiri ta kalleni tace" ina fatan kin fad'a masa gaskiyan yanayin ki? Sai na kasa bata amsa Adda Fati ce ta mata mgana sai ta tabe baki tace"Ahto gwara dai a fad'amai tunda wuri kada wani abu ya biyo baya. " Ni fa na jima da cire Adda Rukayya a matsayin yar'uwata na riga na gama Fahimtar ta, bakinciki ta nuna da Hassada ga nin ko ita albarka. Ta rika Fatan wani Sanadi ya yanke wannan jin Dadin da zan shiga Tunda tun asali bata kaunata. Shiyasa ba zata so Cigaba naba. Tunda ta na Dauka komai ya faru damu ni ce sila. Tun Amma na Dauke mata kai, har sai da ta dawo tana mata Fad'a in ta yi wani abun gaban mutane. A chan gidan Marigayi Mammadi Mamman kona aka daura aurena da Abubakar. Auran da ya zo cikin Tarin kalubale da ban tab'a tsammanin Farincikina zai koma bakinciki da kuka ba. Lafiya lau muka yi taron biki na tara yan makarantar mu ta Dare sai makota ma su zuwa ganin kwakwaf. Sai Adda da iyalanta sai matan gidanmu sai Matan Baba Saminu da iyalansu sai Goggon Kona Baaba ta Lagos sako ta turo ma Adda Fati dubu ashirin tace a ba ma Amma ba yawa. Alhji Tanko da Baba Jibiril ba sako ba aike ba kuma iyalansu. Amma daman bata jira su ba. Har gwara Baba Saminu bayan Daurin aure ya zo har gida ya yi ma Amma Murna shi daman ko matansa na kukan Son abun Hannunsa ba ya kwantuwa. Na dauka sanda aka kaini gaban Amma ta min nasiha na yi kuka na har abada kenan. Ashe ban ma yi kukan ba, An kai ni gidana a d'aya daga cikin Tsala Tsalan Motocin da abokan Abubakar suka kawo mana. An je da yawa kuma duka motocin sun Dauke mutane da Kafar Dama na shiga gida tare da Rikon Inna Adda da Goggon kona. Na samu salama da farinciki Lokacin da na ji ni saman gadon aurena. Daga lokacin hayaniya da Mganganun mata ya rika tashi an kawo mana abinci da nama da Ruwan gora sai lemuka an ci an sha har mutane sun yi guzarin sa. Zuwa Tara na dare suka maida mutane gida Ramatu kad'ai a ka bar min sai da Angaye suka shigo. Bayan yan Nasihu da barkwanci suka mike suka tafi. Ina kuka Ramatu na kuka muka Rabu. Na san Abubakar ya raka su ya kuma dawo bayan ya Rufe gida, ya zauna a gefe na yana kiran Sunana da Hasiya Amarya. Na ga sanda ya cire Babban Rigansa ya fita sai ga shi ya dawo da Filet da Kofuna ya baje kazan da ya shigo da shi. Shi ya rika ba ni a baki har na koshe daganan duk wata Hidima shi ya yi a wannan daran ya jagoranci sallar Nafilan albarkan aure. Daganan ya bi da ni cikin Salama har ya maidani Cikakkiyar mace mun yi kwanan Farinciki da Annushuwa. Daga wannan Daran har rabuwata da Abubakar bamu kara kwanan Farinciki ba. Da asuba wayar sa ta tashemu da mummunan Labari da ya yi silar Rugujewar aurena. Labarin Shagunan Abubakar sun kama da wuta cikin Dare ko Tsinke ba'a fitar