← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 69

Sashe 17

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Kina kara kiran sunana zan kwad'a miki mari, bar ganin ina raga miki,sai naci mutumcin ki. Yarinya kin zo kin tasani kina faman kiran sunana, kuma ki yi mgana kin ki yi to uban waye shashasha irin ki? Mtswwww.."

Bayan taja tsaki ta cigaba da bambare gorinta tana watsawa cikin bakinta.
Sultana sai kallonta ta ke yi ta kasa mgana sai daga baya ta kara kiran sunanta ta juyo a zafafe da niyyar kara sauke masifarta.
Sultana ta lamgwabe kai lokaci d'aya  tana mika mata siririn hannunta cikin Shagwaba tace'"Innani san min goron"
Innani tayi kwafa kafin ta dauko goro karami cikin kwanon gabanta ta dangwara ma Sultana a hannu Lokaci daya tana fadin"Na shige su da kwazzaban ki Sulsana. Wannan yarinya Magajin gida zai yi fama"
Fad'ar sunan yasa dukkansu suka kalli juna Sultana ta kauda kanta. Innani kuma kamar an tunasar da ita ta gyara zama tana fad'in"Ke sulsana kun yi mgana da Magajin gida ko kwanaki nan? Ni wajen kwana uku kenan bana samun sa a waya kuma bai kirani ba, Allah yasa lafiya ina ta zuci zuccin in yi ma Sulaimanun tad'insa sai sha'anin duniya ya mantar da ni."
Da kai sultana ta yi mata mgana da girgiza mata kai alamun itama ba su yi mgana ba. Nan da nan Innani ta kara Harzuka cikin daga murya tace"Ke uwarki. Baki zaki bude ki yi min mgana ba ne
Sultana tace" A'a Innani"
Nan da nan Hankalin Innani ya tashi ta fara salati tana Direwa kafin tace"Wayyo jikana. Yana chan wata uwa duniya ba uwa ba uba. Ba kuma dangi ko wani hali yake ciki? Ke sulsana dubamin wayata cikin daki ki zo ki kara kiramin shi Allah yasa jikana yana lafiya. Magajin Sulaimanu bayan shi ba shi da wani magaji anan duniya"
Ta ke fad'a tana kokarin fashewa da kuka. A sanyaye Sultana ta mike tana wannan tafiyar nata Innani ta kalleta cike da takaici tana fad'in"Zaki yi sauri ko sai na turaki da wannan Sandar ta hannuna? Ta fad'a tana kokarin dauko sandan nata da gudu Sultana ta shige cikin Uwar Dakin Innani, ta fara neman wayar na ta.
Ta duba ko'ina bata gani ba, ga shi daga Falo Innani sai faman kiran ta take yi sai da ta gaji ta fito ammh Daga gefe ta tsaya tana fad'in"Ni fa ban ga wayar taki ba Innani"
Yadda Innani ta kalleta da tana kusa sai ta sha duka da sanda, shiyasa ta tsaya daga baya baya. Tsaki tsaki tsut.!
Kafin tace"Ko ke ma idon naki na da Rauni ne na saka Sulaimanu ya kai ki in da ya kai ni aka ba ni wannan gilashin? Ammh ace waya na barta saman katifar da na kwanta ki zo kina ce min wai baki gani ba?
Ta fad'a tana nuna ta da Sanda,kamar zata daketa. Sultana ta tura baki tana kallon gefen kwanon Innani ga wayar nan kirar kamfanin Tecno karama, ammh tana ta kumfar bakin a saman katifa ta barta. An ci sa'a ne da tana cikin Lalinta ne zata rika bala'i tana tsine tsinen an sace mata waya. Yanzu ma ido ta mutsike tana fad'in"Baki gani ba fa da gaske Sulsana?
Allah dai ya tsine ma barawo da uwar barawo wlh"
Sultana ta zaro ido kafin ta karisa gaban Innani ta duka ta Dauki wayar ta mika mata tana fad'in"Ga fa wayar taki nan a gaban ki Innani"
Innani ta bi hannun Sultana da kallo kafin ta karbi wayar ta jujjuya tana Fadin"Ikon Allah! Ni fa saman katifata na barota. Ni fa daman na dad'e da sanin abun nasara ba shi da tabbas, sai ka ijiye abu ka nemeshi ka rasa sai chan ka ganshi a wani waje mtseww"
Ta karishe da tsaki daman Tsina da Tsaki a bakin Innani Allah ya fissheta kada ta zo mutuwa su kama bakinta.
Sultana ta kara damgwara ma wayar tana Fad'in"Maza kiramin magajin gida. Allah yasa yana hannu nagari."
Sultana ta dukufa kiran Magajin Gida kamar yadda Innani ta saka akayi mata Saving a lambarsa. Itama cikin mazari ta latsa lambar nasa sai dai kuma kuzarinta ya ragu da wayar ta ke kara duui! Sai kuma ta yanke, tayi haka har sau uku duk tafiyar d'aya ce tana ji Innani na fad'in"Kin samu magajin gidan ko?
Ta kasa bata amsa Dagowa ta yi ta kafe Inanni da ido. So ta ke yi ta ce mata ya yi blooking dinta ne,ammh tasan Innani ko za'a shekara bazata gane komai ba. Shiyasa ta mikama Innani wayarta ta ki mgana, da kallon mamaki ta bita baki bude kafin tace"Ke na ce kin samu magajin gidan a waya?
Sultana ganin Innani ta ki karban wayanta sai ta dungure mata a saman cinyarta ta mike tana fad'in"Innani wayarsa ba ta shiga."
Inna ta rafka salati tana fadin"Na shiga uku na lalace ni Dije. Ke kinga Sulsana maza jeki ki gayama Babanku yazo ina nemansa"
Sultana tace"Innani Abba kuma? Barci fa ya ke kinsan yau weekend ne"
Innani ta rarumi sandarta tana fadin"Ko barcin mutuwa ya ke nace ki taso min shi kaji min ja'irar yarinya tabbattaciya. Ba gwara ya tashi da wannan barcin da tashin hankalin da ke Tunkaromu ba, Magajin gidan ne gabadaya ba'a san inda ya ke ba yanzu kai co na Dije, daman wlh ban so tafiyar yaron nan ba, ya lallameni da Kalamansa na bayan ya had'a da su jawomin manyan ayoyin Allah Sai na amince ammh har cikin raina Hankalina bai kwanta ba"
Ta karishe fad'a tana face majina,Sultana ta yi tsaye tana kallonta ganin yadda Lokaci daya ta rikice, To daman ai shi kad'ai ne ke rikitar da Innani sannan kuma cikin Mintina ya ke dawo da ita saiti, wanda ko Abba da ta haifa sai ya Dauki awa Biyar Innani ba ta ji mganarsa ba.
Bata sani ba Inanni ta daga Sandarta sama tana fad'in"Zaki wuce ki taso min shi ko sai na Rafke ki?
Sakarya mara wayau in kina da Tunani da Hankali ai kema abun kukan ne ya same ki, in da kara zama zaki yi mu taru mu tashi gidan da koke koken mu"
Sultana dai da gudu ta fice daga Shashen Inanni tana haki kamar ta yi wani gudun tsere.
Babban gida ne mai shashena biyar,bi da bi, biyun na jikin juna suna da girma,Karamin ne ke chan gefe shashen Innani kenan, wanda ya fi girma gabadaya shine na jikin wani karamin Shashe shima.
Sai da ta tsaya a wajen ta kallah kamar zata ganshi ya fito. Sanin ba Fitowar zai yi ba yasa ta juya ta tunkari shashe guda biyun da suka fi girma.
Na farkon ta bude kofa ta shiga, Sad'af Sad'af kamar barauniya. Ta kawo Tsakiyar Falon taji an ce"Sultana."
Cak ta tsaya ko ba ta juyo ba. Ta san Muryan wacece Umma ce!
Cikin sanyin jikinta na Hallita ta juyo kanta na kasa tana had'e kafafunta alamun ba ta da gaskiya.
Doguwar mace ce,mai dan kaurin jiki baka zaune kan kujera remot a hannunta. Sanye ta ke da Atamfa super aura mai kalan Duhuwa ta ci Daurinta kamar wata matashiya. Alhalin zata ba ma Shekarun Hamsin baya.
Sama da kasa ta kalleta kafin tace"Daga ina kike da sassafe daga tashin ki a barci na duba ki ban ganki ba?
A sanyaye tace'"Shashen Innani na je"
Hajiya Umma ta gyad'a kai kafin tace"Ta na lafiya ko? Da kai ta amsa mata bata damu ba sanin Halinta. Mirmishi ta yi mata kafin tace"Sai ki wuce ki je ki yi wanka ki zo ki mu karya"
Kamar tana jira ta amsa da Toh ta wuce da Sauri Umma ta bita da kallon mamaki a ranta tana Tunanin Saurin me Sultana ke yi haka?
Tunaninta ya tsinke ni Lokacin da taji mganar Innani da karfi tana kwalamata Kira.

"Salamatu.. salamatu.."

Kina ina ne salamatu,?
Chapter 17 · 0% Book details