Sashe 24
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya fad'a yana saka kallon wajen Tahir wanda ya rufe kular ya dawo gaban Sadiq ya zauna saman katifa yana Fadin"Danwake a kula kamar wani yaro dan firamari Sadiq? Ina laifin in Danwaken ka ke son kaci ai akwai a Restaurant sai ka shiga ka siya kaci tunda kai dai ka san nasan abinci ko wani Restaurant in kana Ra'ayi zaka ci bai fi karfin aljihun ka ba"
Yadda Tahir ya ke mganar zaka san abun ya mishi ciwo, duk da yasan Waye Sadiq ta wannan bangaran bai taba Tunanin abun na shi ya kara Lalacewa kamar haka ba.
Wai Danwake a kula abun ma ba shi kunya ya ke yi wlh in ya tuna kuma wai ka shiga cikin mutane da shi kamar wani karamin yaro.
Lura da Hakan da Sadiq ya yi shiyasa ya ture Laptop din gabansa ya Fuskancesa kafin yace"Rayuwa ce. Kowa da irin yadda ya ke tafiyar da tasa Rayuwar Tahir. Miye aibu aciki don na siya abunda nake so na tafi da shi wajen aiki na?
Da Sauri Tahir yace"Wlh akwai aibu. Babban aibu ma kuwa. Aikin yara fa ka ke yi? Yaran ma kanana Sadiq. Haba don Allah"
Tahir ya fad'a har yana wani juya Fuska irin yaji kunyan nan. Dariya Sadiq ya yi kafin yace" A wajen ka kenan ya ke aibu ni dai a wajena a daidai na ke kallonsa kasan Hausawa na cewa Daidai wani.."
" Karkatan wani.."
Tahir ya karishe cikin mamaki kawai yana kallon Sadiq. Shi kuma yana yi masa mirmishi sai kawai ya rike Haba yana fad'in"Ikon Allah.. Allah mai mutane kala kala kawai sai aka ganka ka fito da kula ka bud'e ka na cin Danwake da wake da Manja."
Sadiq yace"I sata na yi? ni zan ci kayana ra'ayi na ne. Ban kuma takurama Ra'ayin wasu ba."
Tahir yace"Ni tsaya ma a ina ka ke siyan Danwaken nan ne?
Sadiq ya ce"chan ne wani gida a kasan layin wajen masu awaran nan da Dankali"
Cikin takaici Tahir yace"kai ko a ina kasan gidan? Ko da ya ke in wajen ciye ciye irin wannan ne kai tsuliyan gari ne"
Sadiq yace"Ni fa ranar naje siyan awara a wajen naji wani na tambaya ina ake saida D'anwake mai dad'i? sai wata mai awara ta kwatanta masa gidan kuma ta yabi Danwaken shiyasa nima nake zuwa ina siya. Kuma Alhandulillah akwai dadi ga tsafta"
Tahir ya karkace baki kafin yace"A ina kasan ya na da Tsafta? Hala a waje ne a ke d'anwaken? Ko kasan me yin Danwaken ne?
Sadiq cikin kosawa da Tambayoyin Tahir yace"ba'a waje ba ne acikin gida ne. Ta ya za'ayi na san mai yin Danwake Tunda ba gidan na ke shiga ba"
Tahir ya ce"Uhm sai kaga yadda ake D'anwaken ka raina kanka Sadiq. ba fa kowa ke tsaftace abun sana'arsa ba, barin ma irin gidajen anguwannin nan. Wani abun wlh in kagani kamar kayi Amai.."
"Tahir.. Tahir don Allah.."
Sadiq ya katseshi bayan ya Daga masa hannu Dariya Tahir ya kwashe da shi kafin yace"Wai don nace Amai..Amai..!"
Sadiq ya ce"Daman kazami ne kai. na sani"
Tahir yace"Tabdijam! Ai dama a Shinkafi a ka haife ka zaka fi Dacewa da Katon kauyen Shinkafi ba na Birnin Zamfara ba."
Sadiq ya yi dariya har sai da ta yi Sauti lokaci d'aya kuma ya kimtse fuska ya kurama gefe d'aya ido kamar mai Nazari. Kansa ya jinjina kafin yace"To ai ban yi maka karya ba Tushena kauye ne. Kuma kauyen Shinkafi. Ko ba'a Haife ni achan ba chan aka Haifi Abba. Sannan lokacin da aka haifeni Umma ta fara rashin lafiya ko arba'in d'ina ba'ayi ba Abba ya ce Innani ta tafi da ni da Umma Shinkafi ta na kula da ni, Sannan ina da wata Takwas saboda Laluran Umma Innani ta yayeni babu abunda bata ba ni na ci Saboda inganta lafiyata ba, Tahir ban sha Nonon uwa kamar yadda ka sha ba. Hannun Innani na zauna har na tsawon Shekara Shidda sannan Abba ya karbo ni na dawo zamfara Ka ga kuwa ka daina mamaki in kaga ina cin wani abu akwai sabon haka Tun ina da kuruciya da su na Saba, kuma ni Inanni ta yi min Renon uwa ka sani ko a yanzu ta mini gatan da ko Abba da ke d'anta ba ta yi ma shi ba"
Tahir da ya yi Tagumi yana kallon
Sadiq ya na jinsa ya Sauke ajiyar zuciya kafin yace"Shiyasa ko Hajja na je gida ta rika rawan jikin kawo min abubuwa taga na fara cewa ba na cin kaza sai ta fara fad'a tana fadin kai dai ka cika kircin tsiya shiyasa nake son abokin nan naka Saddiqu yaron nan har mamaki ya ke ba ni ga shi Dan gata gaba da baya ammh a irin Rayuwarsa kamar wanda baisan gata ba komai ci ya ke har kaji ya na fad'in Hajja zogalen nan ki ijiyemin zan ci da Daddare ammh kai sai shigen iyayin banza da Wofi tafi mara wayau shiyasa baka kiba kullum lange lange kamar iska"
Gabadayan su suka kwashe da Dariya Tahir yace"Ina shan gori wajen Hajja komai sai tace Saddiqu ya fi ka Tahir kai kam sai fatan Shiriya."
Sadiq yace"Allah sarki Hajja na yi kewar Dambunta da kwad'en Zogalenta yaushe zamu je Daura?
Tahir yace"Kasan ko kwanaki ta yi ta fama da Zazzabi."
Sadiq ya kallesa kafin yace"Subhanallah yaushe? Shine baka Fad'amin ba?
Tahir yace"Kawu ya ce da Sauki shiyasa kaji ban Fad'a maka ba. Kasan Hajja da kafiya ga shi ta na ciwo ammh taki bari aje asibiti wai ita ta warke."
Sadiq yace"In na ganta Innani na nake gani a tare da ita. Bambamcin kad'an ne ita Hajja ba ruwan Tsine tsine a bakinta.".
Tahir ya fashe da Shegiyar Dariyansa yana Fadin"Allah Sarki Inanni gaskiya ina missing nata. Yaushe zaka gida na bika nima?
Sadiq yace"mu bari weekend, Jiya Abba ke fad'amin Innani na Shinkafi chan ya barota wajen sha'anin Diyar Baba Saminu da akayi, So kuma ba na son zuwa ba ta gida. Abba yace dakyar suka lallasheta da ta ce sai tazo ta ganni ina nan ba uwa ba uba Allah yasa ina Hannu nagari"
Tahir ya kara kwashewa da Dariya kafin yace"Allah ya ja da ran magajin gida da girman kujeran ka.." ya fad'a har yana daga masa babban yatsansa alamun jinjina.
Sadiq ya make hannun yana Fadin"Ka bari Tahir."
Shi ko sai fadi' ya ke"Takawarka Lafiya Autan Umma dan gatan Abba. shalelen Innani. Angon SULTANA"
wata uwar Harara Sadiq ya sakar masa kafin yace"Tahir sunan Sultana ya fita a bakin ka? Inanni bata kyautamin ba"
Ya fad'a yana yamutsa Fuska Tahir ya Dafa kafad'arsa yana Fad'in"Mutumina kaji dadin ka. Kai dan gata ne irin wannan zukekiyar Yarinyar duk ka kai kadai? Ya ke fad'a yana Dariya Lokaci daya yana kashe masa ido d'aya.
Ture hannunsa Sadiq ya yi yana fadin"Tahir Allah ya shirye ka."
Tahir yace"Ni dama Hajjo nima ta kamamin wata achan Daura yar Fara haka Danya Sharaf mallam"
Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Ai tasan halin yan kayanta ne. In ko ta kama maka zaka iya kunya tat
Tahir."
Cikin Magiya da Fuskar Tausayi Tahir yace"Wlh a'a. Kaga da mun gama Hidiman kasar nan muka kama aiki sai kawai kaji mun angwance Rana Daya da yan Shillan mu Abokina."
Dukkansu Dariya suka saka har suna Tafawa kafin Sadiq yace"A'a in muka angwance Rana d'aya wa zai rakani Dakin Sultana?
Tahir ya bushe da Dariya ya Daki kafadar Sadiq da karfi yana Fadin"Shige abokina ashe kana son yarinyar nan sai ka rika wani basar da ita?
Sadiq na mirmishi yace"Tahir ba komai ke bukatar bayyanawa ba. Sultana Zabin Umma ce. Sannan Burin Innani ne, ni kuma kaga matan nan biyu suna da Muhimmamci a Rayuwata da ko wuta suka ce na shiga wlh zan shiga. Sun gama min komai a Rayuwata. Sultana a gaba na Umma ta Reneta yarinya ce karama fa Tahir sai na zauna ina Biye mata? Ni ma yaron ka ke so na koma?
Tahir ya ce da Sauri"ko ba ka koma yaro ba akallah dai ka Damu da ita kamar yadda ta damu da kai."
Sadiq ya mike tsaye yana gyara zaman 3Quater da ke jikinsa lokaci d'aya yana Fad'in"Tahir har yanzu da Sauran Lokaci. Baka gane abunda na ke gayamaka ne? Shekarata Talatin wannan Shekaran Sultana ba ta wuce sha Shidda ba Jss3 fa take. Ba ta ko gama socondary ba, Sannan ni ma ina son Dora Masters dina bayan mun gama Servise din mu, ina da abubuwan yi a gababa ma su tarin yawan da ba na so wani abu ya Daukemin Hankali itama ba na so na zama Silan samun matsala a bangaran karatunta shiyasa kaga ina mata haka kuma mganar kira muna gaisawa, daga gaisuwa da tambayan makaramta bata iya fa mgana da ni,wani Lokacin ma in ta kirani da wayar Umma ina Dauka sai dai ta ce bari ta kaima Umma. Ka kyale yariyanan Kuruciya ne da Wauta ke Dawainiya da ita fa"