Sashe 21
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna tafe Rai rai har bakin Titi suna zuwa Tahir yaga Sadiq na kokarin sama musu adaidaita, da Sauri Tahir yace"Mu hau mashin mana. mun makara fa."
Ya fad'a yana kara Duba agogon Hannunsa Tara saura. Bai tanka sa ba sai da ya tsare musu adaidaita sannan ya kallesa lokaci d'aya yana Fadin"A daidaita zamu hau Tahir"
Tahir ya bata rai kafin yace"Haba don Allah. Kamar wasu mata? Mu hau mashin mana Sadiq"
Sadiq ya ja sa yana Fad'in"Adaidaita nace zamu shiga Tahir. Kuma da ka ke mganar Mata daman kai namiji ne?
Yana mgana ya na Tura Tahir cikin adaidaita shima ya bi bayansa lokaci d'aya yana fadin"Ni kwangila za ka sauke ni. Shi kuma"
"Pizzet zan sauka mallam"
Tahir ya katse shi da Sauri yana kunkuni,;Sadiq sai da ya yi dariya kafin yace"Mallam mu je"
Mai adaidaita yaja suka Fara tafiya Tahir ya sha kuni, yaki mgana ballatana Dariya sai ma ya fiddo wayarsa yana Famam dannawa shi kuma Sadiq na kallon Hanya.
Sun kawo Bakin ABU aka tsaida shi wata mace ta shiga. Tahir ya matsa kusa da Sadiq ya na Hararansa cikin kunkuni ya yi tsaki. Sadiq na jinsa bai yi mgana ba yana dai ta mirmishi kafin su isa in da Sadiq zai sauka an dauka an ijiye yafi sau biyar Ran Tahir ya baci sai masifa ya ke wai yana Duba agogo wai ya makara Saboda Sadiq ya tankasa su yi tsiyar a hanya sai kuma bai kulasa ba har ya sauka, ana sauke shi ya ba da kudin gabadaya bayan ya fito da Wallet dinsa. Ta baya ya dawo ya Dafa kafadan Tahir ya na Fad'in"Abokina sai mun had'u ko?
Da Sauri Tahir ya fizge kafad'ansa yana Fad'in"Mu je don Allah mutane sun makara ka tsaya kana ta share share a kan hanya."
Mai adaidaita ya tada Napep dinsa yana fadin'"Bawan Allah adaidaita ta haya ce in da baka san share share sai ka dauki Drop. Kare da kud'insa ya sha lahaula.".
Sadiq sai da ya yi dariya har Fararan Hakoran sa suka bayyana a waje. Daganan titi ya tsallaka zuwa Ofishin Road Safety. Chan ya ke C.D.S. dinsa shi kuma Tahir Fada zai je a secateria za su had'u da yan team din su dagachan zasu wuce in da suke na su C.D.S. d'insu kuma rana d'aya su ke yi duk Ranar Talata.
Sai bayan La'asar ya baro wajen yunwa ya ke ji,cikinsa har wani kara ya ke yi, Yau furan da ya ke siya ya sha ya siya yaji nonon da karni ya kyutar da shi. Matar da ta ke kawo nonon bafullatana ne to ba ta zo ba yau sai wata ce ta kawo kamar Nononta ba pure ba wani iri ya yi masa baki da ya bata masa Yanayin bakinsa.
Ba shi da matsalan siyan duk abunda ya gani yaji yana sha'awa. Bayan nan ya siyi zogala aka kwad'an ta masa shima yaji Bakinsa ba Dad'i ya kira almajiri ya ba shi. Sai rogo da gyada ne ya siya bayan ya kamo hanya. In dai ya zo ranar shi ya ke ba da sallar Azahar da La'asar a wajen in bai zo ba kuma wanda ya saba jan su sallah sai ya ba su.
Adaidaita ya sake tara har samaru ya kuma gangaro da kafarsa har inda suka kama domin zaman bautar kasar su a garin Zariya. Yasan Tahir ya dawo tunda yasan ba sa Dad'ewa. Tura Dakin ya yi yaji a rufe bai damu ba ya na da key a hannunsa. Kuma yasan ya rufe ne ta ciki tunda aka taba musu sata suke kulle dakin su ko da suna ciki. Ya na ko budewa sai ga shi ya shiga yaga Tahir kwance share share akan katifa kamar ya mutu daga shi sai gajerun wando, ga kayan da ya cire nan watse a kasa takalminsa har da agogo jakarsa ga wata bakar leda nan a kasa itama ana ta muhallin.
Sadiq yq bi sa da kallon Takaici. Tsallake kayan ya yi zuwa chan kurya ya zauna gefen katifar,Tahir cikin barci ya mulmula ya maka ma Sadiq kafarsa, shi ko cikin fusata ya juyo ya Hauresa da Kafarsa shima bayan ya mike. Tahir ya kara juyawa zai koma Barci Sadiq ya sa takalminsa ya taka masa kafa yana Fad'in"Dilla ta shi mallam. Yanzu haka ko sallah baka yi ba ka kwanta kamar wani gawa"
Tahir ya bude ido dishi dishi yana kallon Sadiq kafin ya yi mika ya mike zaune tare da Hamma haaaaa..!
Sadiq ya ji haushi cikin kufuluwa yace"Ka tashi daga barci ba Salati ba kiran sunan Allah. Sannan ka yi hamma ba Alhamdulillah ka bud'e baki kamar wani sakarai yanzu ko yara sun san in sun tashi daga barci su kira sunan Allah. Sannan sun san in sun yi Hamma su Rufe baki"
Tahir ya bisa da kallo da Shanyayyun idanuwansa da alamun barci bai ishe shi ba.
Sadiq ya shure kayansa da kafarsa yana Fad'in"Kai dai mugun kazami ne Tahir. Miye haka?
Tahir ya mike yana mika lokaci d'aya yana Fadin"Kar ka isheni fa. Na dawo a gajiya me ka ke tunanin zan iya tsinana ma kaina?
Sadiq ya kalli Tahir cikin takaici ya ma kasa mgana illah kad'a kai kawai da ya yi yana fad'in"Biyar saura ka je ka yi sallah Mallam"
Ba musu Tahir ya ja wandonsa ya zura ya saka wata karamar riga da ya Dauko saman akwatinsa,:sannan ya fice Daga Dakin bayan ya zuba ruwa a buta .
Sadiq ya bishi da kallon Haushi. Ba ya iya zama da kaya a watse a daki shi Mutum ne da ke son kimtsi. Karshenta shi ya kare da tattara ma Tahir kayansa ya ninke masa ya Bude akwatinsa ya saka masa. Sannan ya fito masa da karamin wando da Riga na shan iska. Yasan waye Tahir da Hauka wajen dauko kaya sai ya kara watsar da wasu kayan kuma bazai maida ba ko ya yi mgana kunnen uwar shegu ya ke yi da shi. Bakinsa har tsini ya ke yi saboda mgana ammh in dai akan Tahir ne a banza ne.
Shima kayan jikinsa ya cire ya shanyasu saman Hanger saboda su sha iska, Akwatina uku ne a Dakin Biyu na Sadiq d'aya na Tahir ne shima karamin ciki ya Bud'e ya Dauko Jallabiya ya saka Mai ruwan kasa. Ya zura ya kuma kai komai nasa a muhallinsa Dakin Tsaf kamar na mata,komai yana muhallinsa.
Gefe katifarsu ce Babba na kwanciya Sai wajen kayansu, Kayan kwalliya na maza sannan sai wani Dirowa kasa kuma inda suke jera takalmansu. Daga gefe kuma Gas din girki. Sai kayan abinci da kayan girki. Sai botikan wanka guda Biyu sai babban roba in da suke Tara Ruwa. Daga kusurwa kuma ga karamin Fridge din su tunda suna zuwa da miya ko wani abun da zai lalace shiyasa suke da Fridge din.
Kafin Tahir ya shigo har ya gyara gadon ya share Dakin. Sai da ya gama Hiran sa da Matasan da ke gefen dakinsu suna waje suna wanki sannan ya shigo ya ta da Sallah.
Sadiq na zaune a gefe yana kallon shi har ya Idar ya mike yana ninnike Darduman Lokaci d'aya yana fad'in"Sultana dai ta huta in dai ta bangaran gyaran Daki ne"
Yana jinsa ya yi masa banza sai ma ya jaho Ledan Rogonsa ya Dauko ya Bude ya fara ci. Gefensa Tahir ya zauna yana leka ledan gabansa kafin yace"me ka ke ci ne?Rogo da aya?
Tab! A ci lafiya"
Tashi ya yi ya bude fridge ya Dauko bakin Coke dinsa guda d'aya da ya siyo da zai dawo ya saka a Fridge ne Tunaninsa za'a kawo wuta kuma yau suna jin Halin na su.
Gefen Sadiq ya kara komawa ya zauna ya jawo ledansa da Sadiq ya ijiye masa nan gefen Littafansa tunda kowa bangaran da yake kwanciya yana ajiyan littafansa masu muhimmanci.
Cake ne babba aciki ya fito da shi yana ci yana korawa da lemu gefe d'aya kuma yana Faman chart ta wayarsa.
Sadiq bai ci rogon da yawa ba yaji ya Chusemai ciki sai kawai ya Ture ya kalli Tahir yana fad'in"Ka ci."
Tahir yace"A'a Arammah kai dai kaci ni nagode"
Sadiq ya yamutsa Fuska kafin yace"Ya cushemin ciki ne."
Tahir ya kallesa a karkace kafin yace"Ka ma ci sa'a a irin yameyamen da ka ke yi ma cikinka baka fara ciwon Tsakuwar ciki ba"
Sadiq ya kallesa kafin yace'"Fatan da ka ke yi min kenan?
Tahir ya Daga lemun hannunsa da Cake yana fad'in"Afuwan"
Daganan ya cigaba da shan lemunsa yana had'awa da Cake
Status ya ke kallo an saka wakar Turanci har yana bi. Sadiq ya koma ya kishingid'a yana Fad'in"Ka dafa mana abinci"
Tahir ya yi masa banza sai da ya kara maimaitawa sannan yace"Wani abinci kuma? Baka ci rogon ka ba. Ni kuma kaga iya wannan ni da wani abu sai gobe in muna raye"
Sadiq ya yi kasake yana kallonsa yasan rashin Mutumcin Tahir saboda yasan girki na da D'aya daga cikin abunda ke ba shi Wahala baya ma kwantatanwa Tahir din ke musu abinci.
Shiyasa wani Lokacin bai juran wulankancin Tahir ya ke fita ya samu wani abu yaci. Tahir kuma kamar da gayya sai yaga Dama ya ke d'ora abinci ko ya yi ta abubuwa ya na bata Lokacin barin ma in yaga ya yi mgana ko ya Lura yana jin yunwa.
Yadda ya Fahimci Tahir ya so ya wulakanta ne yasa ya mike ya saka Dogon wando ya Dauki kudi cikin Wallet dinsa ya fice. Yana ji Tahir na Fad'in"Me zamu Dafa?
Ko amsa shi bai yi ba ya zura Takalminsa masu taushi ya fita,Sallama ya yi ma matasan da ke waje yan makaranta ne su. Ganganrawa ya yi cikin Layin Tsamiya in da yake siyan awara. Yaje da kansa ya siyo aka saka masa yaji da kabeji har da albasa Dabam sun san shi Custumer din su ne Sosai Sadiq yasan muhimmancin awara. Sadiq ba bu abunda ba ya ci shi mutum ne kamar Social kamar kuma ba Social ba. Rayuwarsa Sannu sannu ya ke binta yadda ya Dauki al'amuransa sai ya baka mamaki a irin matsayinsa na Rayuwa. Ababen duniya masu dadi da kawatuwa ba su dameshi ba ya fi son na Mutanen da suka Dauki Rayuwa a sannu.