← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 69

Sashe 27

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai karfe sha daya suka watse su ma sallama suka yi ma Hajjo suka dauki kayansu zuwa Dakin Tahir na cikin Shashen Hajja daman nan suke sauka Daki ne irin na yan kauye dai. Tsaf an gyarashi Inda Sadiq ke da Tabbacin Hajja ta gyarashi ammh Tahir ai son jikinsa da kazanta bazai barshi ya tafi ya barki Dakin a gyare ba. Sakamakon sun gaji kuma ba su samu Hutu ba yasa ba su bata Lokaci ba suka bi lafiyan Katifar Tahir wata yar yaloliya da ita. Ba su farka ba sai asuba Da asuban ma Sadiq ne ya tashi Tahir kamar yadda suka saba ko achan baya. Bayan sun dawo sallar asuba suka koma barci ba su tashi ba sai goman Safe shima Hajja ce tazo dubasu tana Fadin barcin su ba na lafiya ba ne su tashi hakanan, ita ta saka musu ruwan zafi dukkansu suka yi wanka suka sauya kaya sannan suka shiga Dakinta suka karya. Sun iske kayan karyawan su kala kala daga Dakunan matan yayyen Tahir har Zulaihat ta yo musu kunin gyada da Fanke shi Sadiq ya ci Tahir kuma Tea ya sha da Buredi. Sannan suka kwanta Dakin Hajja suna ta Hira. Tahir kan gadon karfen Hajja ya yi Dare dare yana charting shi kuma Sadiq na zaune samar Darduma a tsakar daki yana taya Hajja bare gyada suna ta hira in ka shigo ka gansu sai ka yi Tunanin shine jikan nata Tahir ne bakon. Sai da abokin Tahir Jamilu yazo ya jasu suka fita zuwa gidansa ya yi aure Tahir din na Zaria. Chan suka je amarya ta yi musu abinci sai a hankali Tunda karamar yarinya ce Tahir sai shakiyanci ya ke yi ma abokinsa wai ya auri kwaila. Sadiq na kare ma Jamilu Tahir ya kallesa yace"Dole ka kare masa mana. Tunda duk tafiyar ku daya ce" Sadiq yace"Eh mun ji din". Ya na da sakin jiki sosai Tun farkonsa Daman mai son mutane ne kuma ba shi da Bakunta ballatana amincin da ke Tsakaninsa da Tahir ya wuce duk yadda Mutane ke Tunani a kansu. Ranar yini suka yi ziyarce ziyarcen gidajen yan'uwan Tahir har gidan Zulaihat sun je ta yi ta rawan jiki da su Sadiq yace Danwake zata yi masa. Shi kuma Tahir yace ta Dafa masa kwai. Sadiq ya zunguresa ya na fadin"Wai ajiyan kwan ka bata da zaka ce ta dafa maka? Tahir yace"Kai ajiyan Garin Danwaken ka bata da kace tayi maka"? Da ya ke ta na jinsu sai ta yi Dariya kafin tace"Kowa zan yi masa abunda ya ke so" haka ko akayi kowa ra'ayinsa ta yi masa Mijinta ne kuma yace duk abunda suke so ta yi musu Daga karshe Tahir nata Fad'an meyasa ta yayyaka ma Sadiq kwai a cikin danwakensa Tunda yace shi baya cin kawai Sadiq yayi masa bakam yana cin Danwakensa yana Santi. Sai Dare Hajja ta gansu sai fad'a take yi tana fadin"ina kuka shiga ne yau? Tun dazu na gama Tuwon. Yan'uwanka sai zuwa neman ku su ke yi bakwa nan" Sadiq ne ya ke fad'amata inda suke je yau tace sun kyauta sun yi ziyara. Ba su ci tuwon ba sun koshi sai dai Sadiq yace ta yi masa Dumame da Safe. Sai adaran Sadiq ke fad'ama Hajja da Safe Gusai zasu je. Ta fara fadan ba su gayamata da wuri ba nan da nan ta mike ta fara had'a abunda ta ke da shi Wanda zata bama Sadiq ya kai ma iyayensa. Tun safe suka shirya kafin Takwas sun karya ,sun kuma shirya tsab Hajja ta bama Sadiq leda cike da su kuka,kubewa garin kuni,zogale danya da wacce ta bushe kayan kamshi sai aya mai kyau ta ce a kai ma Innani. Yayyen Tahir har tasha suka rakasu suka ba su 10k. Sadiq dai bai isa ya ce komai ba tunda ko ya yi mgana ba za su saurareshi ba. Da zasu tafi Kasim wanda shine Babba ya Dafa kafad'ar Sadiq yana Fadin"Ku kula Sadiq. Allah ya tsare ku mungode Allah ya bar zumumci" Sai da Motarsu ta tashi sannan suka koma gida. Da wuri suka isa Gusai, Sadiq sai yaji wani irin iska farinciki na shiga jikinsa da gaske ne ba gida kamar gidan ku. Ba kuma gari kamar garin ku, daga nan suka samu abun hawa zuwa Tudun wadan Gusai. Lokacin da Sadiq ya Buga makeken get din gidansu Mallam Tajudeen ya Bude get din ya gansa sai ya washe baki cikin Tsananin Farimciki yace"Ma sha Allah. magajin gida barka da sauka. Mallam Attahiru maraban ku da zuwa.." Sadiq ya yi mirmishi ya na Dafa kafad'an Mallam Tajudden kafin yace"Mallam mun same ku lafiya? Daidai Lokacin da ya ke kokarin karban Jakar hannunsa sai ya hanasa ya noke yana fad'in"A'a kai fa malamina ne me yasa zan bari ka karban min kaya? Mallam Tajudden ya yi dariya kafin yace"Ammh ni a karkashin mahaifinka na ke. Biyayyata a gareka Dole ce" Sadiq bai ce komai ba ya mikamasa Akwatin ya karba da Sauri ya sake Bude musu kofar suka shiga Tahir na Binsa a baya Lokaci daya yana fad'in"Mallam Taju Tahir fa sunana ba Attahir ba." Da Sauri Sadiq yace"Ko Dahiru zai ce? Tahir ya tokare shi da takalminsa ta baya yana Fadin"Uban Dahirun" A tare suka saka Dariya shi ko Malam Tajudden da gudu ya shege shashen Innani Saboda yasan itace ta Farkon da ya kamata tasan magajin gida ya dawo. Suna tafe a haraban Gidan Sadiq na kallon Motocin da ke fake a Haraban gidan cikin Tsananin kewa ya ce"Abba na gida kasan yau weekend ko zai fita sai yammah." Tahir ya bi motocin da kallo. Shi fa har mamaki yake in yaga Sadiq a wani wajen na wata irin rayuwa. Sai ya Tuna mahaifinsa da gidansu da Duka Danginsa sai ya rika mamaki gata iya gata ba wanda Sadiq bai mallaka ba Motar hawa ko wace iri ya ke so zai hauta ammh in ka ganshi a yana yawo da kafarsa a layi sai ka rantse bai taba ganin Mota ba. Muryan Sadiq dai ta katsesa sanda ya ke fad'in"Kaga fa Tahir akwai baki a gidan nan. Wacan kamar Motar Yaya Sa'im" Tahir dai sai dai ya kallah baya mgana suna tafe suna bangazan kafad'an juna kuma suna tafiyan wahainiya. Tahir ya juya baya ya kara kare ma girman gidan kallo da girman Shashe shashe na gidan da irin kayan alatun da ke cikin gidan sai ya koma ya bi Sadiq da kallo da ke tafiya zuwa Shashen Innani. Kawai sai ya girgiza kai ya kara d'an gudu ya cimmasa lokaci daya yana Fad'in"kamar ba daga gidan nan ka fito ba" Sadiq sai ya murmusa kafin yace"Mutane da yawa haka suke dauka" Tahir ya kallesa kafin yace"Dama ni ne kai Sadiq" Da Sauri Sadiq yace"Tahir ka zama mai godema Allah da Ni'imarsa sai ya kara maka." Tahir ya yi mirmishi kawai bai yi mgana ba. Sun kusa isa kofar Shashen Innani kenan sukaji mganarta fad'i take yi"Kai Mallam Saju ba'a san malamai makada Annabawa da karya ba. Ka Rantse Kwarankwatsa Magajin gida ne ka gani" Sadiq ya kalli Tahir shima ya kalleshi suka fashe da Dariya. Da sauri sauri suka nufi Shashenta suna shiga suka isketa Tafe da Sandarta ga gilashinta a Fuska Mallam Tajudden na gefenta. Daga bayanta kuma Siyama ce da Sultana sai yaran Sa'ima su Abadallah. Daman suna Shashen nata ne Tun Safe da Abba da Umma tare da Mama suka shiga gaisheta bayan Taba Hira sai suka tafi Shashen Abba suka barta da Sultana Daman yar gidanta ne ko Innani bata ga kowa ba bata cika Damuwa ba. Tafi damuwa da in bata ga Sulsana ba acewarta ba. Sa'ima ce tazo tafiya da yaranta da tazo gaishe da Innani suka zo tare da Siyama shikenan ta bar su nan ta koma Shashen uwarta. Ko da Mallam Tajuddeen ya shigo da akwatin Sadiq yana ma Innani albishir ga Magajin gidan ne sai Masifa take yi da faman tambayan ba Sa'imar ta zo ba? Ta kwashi ya'yanta ta tafi mana sun gaji da su. Siyama yarinya ce sa'ar Sultana sun riga sun san Halinta ba su bi ta kanta ba. Innani duk son ta da bako to in yazo gidan Sulaimanu kada ya wuce kwana uku komai mutumcinku da taga ka share kafa zata fara sakin Manganganun an zo an dora ma Sulaimanu nauyi Allah na Tuba shima Rufin asirin Allah ne ba shi da shi. Ko da kuwa jikokinsa ne tace ai suna da Gidan Ubansu su zauna chan mansa. Innani ba ta yarda da Mallam Tajuddeen ba shiyasa ta mike kamar ta kifa tana ya rantse dai da gaske Magajin gida ya gani. Ko a yanzu din ma bata lura da shi a gabanta ba, sai Faman fadi ta ke Mallam Saju ya rantse kada yazo karya ya ke mata. Sultana ta bayan Innani ta ke lekowa tana kallon Yaya Sadiq shi kuma Hankalinsa na wajen Innani yana ta mata mirmishi Siyama ta Buga Ihu ta nufesa tana Fadin"Wlh Innani da gaske Yaya Sadiq.." Ta fad'a jikinsa cikin Tsananin murna Su Abdallah ma suka nufesa suna fadin"Uncle.." Rikesu ya yi gabadayansu yana Dariya Innani sai ta rikice ta fara fadin"Ke don uwarki Siyama Ina magajin gidan" Sadiq ya saki su siyama ya karisa ya rike Sandar innani ya saka Hannu ya ciro glass din idonta ya goge mata sannan ya maida mata Lokaci daya yana Fadin"Ga ni nan fa Tun dazu a gabanki Innani ko dai har yanzu Idanuwan naki da sauran gyara bakya gani Innani" Ai jin muryan Magajin gida ya Rikita Innani ta rikesa gam cikin Lalube tana Fadin"Allahu Akbar Abubakar Saddiqu dai a gabana."Sai ta fashe da kuka tana fadin"Yau dai ga magajin Sulaiman ya dawo. Dole na damu kwana nawa bamu yi mgana ta wayar zamanin nan ba. Sulaimanu fa kai kadai garesa magajinsa Dole na shiga Damuwa in ban jika ba" Rumgumeta ya yi yana Fadin"Innani ina nan lafiya. Ai na gaya miki Hidimar kasa na ke yi achan Zariya ko..? Innani tace"Eh haka kuma kace to yanzu daga chan Zariyan ka ke? Kai tsaye ya juya yana kallon Tahir wanda ya Dauki Afiya. Ya nuna mata Tahir kafin yace"Daga Daura muke. Tare da Tahir muke" Innani ta yi shuru
Chapter 27 · 0% Book details