← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 69

Sashe 49

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nurse tace min na zauna ammh kada na yi hayaniya ko Surutu.
Na gyada mata kai har zata fita ta dawo ta na fad'in"Ina yayanki da kuka zo jiya tare?
Kallonta na yi cikin mamaki kafin na Tuna wanda ta ke mgana da Sauri nace"Sun ta fi masallaci."
Sai ta gyada kai ta fice. Farar kujeran da ke wajen na ja na zauna ina kallon Amma cikin Dare daya ta rame ta Fita Hayyacinta ruwan da aka saka mata na rika lekawa naga yana tafiya ita kuma sai barci ta ke yi cikin sukuni da salama.
Shuru ba su dawo ba har gari ya waye sai na fara Tunanin ko sun tafi ne,sai chan sai ga su sun shigo again wannan Nurse din ta kawo su dakin. Suna shigowa na mike ina kallonsu yana rike da Leda baka a hannunsa shi abokin ya na daga baya kamar bai da son mutane.
Ni ya mikama ledar na saka hannu na karb'a lokaci daya ya na fadin"Ashe sun bata daki"
Kai na gyad'a masa batare da nayi mgana ba.
Cikin natsuwarsa da lura ya na dashi Tun jiya yace"Waina ne sai ruwan zafi ki samu ki sha tun jiya baki ci wani abu ba."
Kai na gyad'a masa kafin nace"Nagode sosai Allah ya saka da Alheri."
Bai amsa ba sai ma ya karisa gaban Amma ya na kallonta kafin yace"Allah ya bata lafiya."
Na amsa da Ameen.
Tahir daga chan baya yace"Zamu makara fa Sadiq."
Jin haka yasa ya kalleni sai kuma ya Duka ya cire silifas din kafarsa da ya siya a waje ya mikamin ya na fadin"Saka wannan shi zai fi yi miki daidai."
Da Sauri na cire na kafata na saka Silifas din, lokaci daya ina fadin"Sannu da kokari nagode.".
Ya jinjina kai kafin yace"Zamu tafi. In da wani abu ki kirani kin ji ko?
Ina so nace masa ba ni da waya ballatana ma lambarsa.
Ban samu damar mgana ba Abokinsa ya kara fad'in"Sadiq."
Da Sauri ya juya ya na Fadi'n"Mu je Tahir sai mun dawo."
Kokarin Biyosu na yi har wajen Dakin da Sauri ya juyo ya na fadin"Ki koma ciki."
Ya fad'a ya na kallona sai na kasa masa gaddama cikin ladabi nace"To."
Na juya na koma sai da yaga shigata sannan ya wuce ya bi bayan Tahir.
Har suka samun abun hawa ba wanda ya yi mgana sai da suka kusa Sauka sannan Tahir yace"Wai yarinyar nan wani irin fari gareta? Albinion ce.?
Sadiq ya yi kamar bai jisa ba sai da ya kara maimaitawa sannan yace"Ina zan sani Tahir. Me yasa baka tambayeta ba?
Tahir ya tabe baki kafin yace"Ina ruwana da ita  wai a ina ka had'u da su? Na ganta ne kamar buzayen nijar masu gudun hijara."
Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Bansani ba fa Tahir nima jiya na fara ganinta."
Daganan ya fara ba shi labarin yadda ya Had'u da Hasiiya jiya..
Ya karishe da fad'in"Ni ko sunanta ban sani ba jiya na fara ganinta."
Tahir ya rike baki kafin yace"Sadiq anya ba gamo ka yi ba?
Sadiq bai bashi amsa ba sai da suka Sauka sun fara takawa sannan Sadiq ya ba shi amsa da cewa"Nima na yi tunanin haka da farko, sai daga baya na gane mutane ne"
Dariya suka saka gabadayansu. Tahir yace"Ni dai ina fatan kada garin wannan Shegen son taimakon nan naka watarana ka kai kanka da kanka a saida ka."
Sadiq yace"To Ameen"  yana mirmishi,
Koda suka isa Dakin su Takwas saura a gurguje Tahir ya kunna musu gas ya dora Ruwan zafi, Shi kuma Sadiq ya saka a kettlo tunda akwai wutar nepa.
Saboda suna Sauri Tea suka sha Tahir sai Kunkunin ya ke yi Sadiq ya ja masa kwanan wahala ga shi yanzu maimakon ya huta zai kara fita kuma. Sadiq dai bai tankasa ba Tahir ya rigasa fita shi ne karshe ya kulle dakin na su saboda ya makara yasa  ya hau mashin Saboda ya isa akan Lokaci.

Ko achan wajen aiki yarinyar na yawon fad'o masa arai. Sai biyu ya taso daga wajen da ya ke Hidimar kasa. Saboda yanayin da ya kwana aciki yasa bai tuna da Danwake ba.
Ko da ya dawo ya iske Tahir na ta sharan barci zafi ya ke ji yasa ya Dibi Ruwan sanyi ya yi wanka ya Sauya kaya ya iske Tahir ya Dafa Farar shinkafa shi Tahir da kifin gwangwani yaci ya rasa me ya ke had'a Tahir da cin kifi.
Shi kuma sai ya Dumama miyar da Umma ta yi musu akwai saura ya ci da Naman sa.
Sai da ya koshi sannan shima ya bi lafiyan gado ya kwanta sai la'asar ya tashi ya Bugi Tahir ya na fad'in"Sai ka tashi an yi la'asar."
Tahir yace"ni ka kyaleni bayan duk kai ka kai ni in da nagaji."
Sadiq bai kulasa ba ya tashi ya fita waje ya kama ruwa ya yi alwala ya tafi masallaci Tahir sai ana Tahiyar karshe ya shigo masallacin
Da suka idar shi ya tsaya addu''a Har Tahir ya gama na shi Sallar suka fita tare.
A hanya Sadiq ya kalli Tahir ya na Fadin'"Sai yanzu na tuna. Dazu nace ma yarinyar nan ta kirani in suna bukatar wani abu ammh Kasan me?
Tahir yace"Sai ka Fad'a.?
Sadiq yace"Ban ko karbi lambar wayarta ba. Itama ban bata nawa ba."
Tahir ya kallesa kafin yace"Allah yasa ma ta na da wayar."
Sai Sadiq ya yi shuru kafin yace"Kuma fa domin ni dai ban ganta da waya ba. Ko kuma zai iya yuyuwa rudewa yasa ba ta zo da ita ba."

Tahir ya jisa ammh bai tankasa ba.
Suna komawa yaga  Sadiq na shiri har da saka manya kaya cikin mamaki yace"Ba dai asibitin zaka koma ba?
Sadiq yace"Eh ai tare zamu koma?
Da Sauri Tahir yace"Wlh tallahi ba in da zani. Kai dai da ka siyan ma kanka Allah ya kiyaye Hanya."
Sadiq yace"Ameen addu'ar da ka yi ma ta wadatar."
Shigan manyan mutane ya yi har da Hulansa kube mai kyau zanen aikin jikin Shaddarsa mai ruwan madara ya yi ma Tahir sallama ya fice.
A hanya ya kira Abba ya ce ya na son kudi Abba yace to zai turo masa.
Kai Tsaye yace"Abba wasu bayin Allah ne ke bukatar taimako na lafiya shi ne na ke son na taimaka musu."
Abba yace"Shikenan Magajin gida a taimaka musu."
Sadiq yace"Nagode Abba. Allah ya kara girma ina Innani.?
Abba yace"Sun tafi Shinkafi ita da Sultana tun jiya."
Sadiq yace"Abba Innani fa ba ta da wani karfin jiki ga Tsufa Tsakani ga Allah tafiye tafiye ai ba nata ba ne."
Abba yace"Kasan Innani da Kafiya. Ta kafe kuma kasan ko nace ta zauna bazata zauna ba. Da ma kai ka yi mata mgana to da zata ji maganarka."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Allah ya dawo da su lafiya."
Abba yace Ameen tambayan Su Umma ya yi da su Salima  sun d'an taba hira da Abba sannan suka yi sallama.

Ya isa abitin Biyar Daidai,
Shi bai yi tunanin siyan komai ba, kai tsayensa ya shiga har Dakin sai dai abun da ya basa mamaki ta nan zaune ita kadai kamar yadda ya barta.
Bata ma san ya shigo ba sai da ya yi sallama sannan taji shigowarsa.

Zumbur na mike ina kallonsa shima ni ya ke kallo sai naji nauyi na dukar da kaina ina Fadin"Ina yi ni."
Cikin Natsuwarsa ya amsa da Lafiya lau ya mai jiki?
Na amsa da sauki cikin kulawa ya karisa gaban gadon Amma kafin yace"ba ta tashi ba ne?
Da sauri na ce"Ta tashi dazu, sai dai kuma ba dadewa ta koma."
Kai tsayen shima yace"Bata ci wani abu ba kenan?
Da kai na amsa masa kafin nace"Ruwa kawai tace na bata tasha sai kuma ta koma."
Jinjina kai ya yi lokaci daya ya na harde hannayensa saman kirjinsa.
Ya na kuma bin nazarin dakin da kallo daga alamun dai ba wanda yazo.
Ga sauran wainar da ya siyo mata da Safe nan ta rage. Sai ruwa wanda ya ke tunanin kila siya tayi tunda shi dai bai siyo musu har da ruwa ba.
Cikin mamaki yace"likita ya zo ne?
Kai Tsaye nace"Eh ya zo ya dubata ya tambayeka nace ka je ka dawo. Sai ya ba ni wata takarda yace na baka."
Na fad'a ina dauko masa Takardan saman dirowan da ke wajen na mika masa.

Karb'a ya yi ya duba magunguna ne shiyasa kawai ya fice bayan yace yana zuwa Phamarcy yaje ya siyo mgangunan Atm dinsa ya ba da aka cire akwai sauran kudi kafin Abba ya Turo masa daganan ya fita waje ya siyo katan din ruwa da maltina ya had'o mata da kayan marmari sannan ya Dawo daki.
Yana shigowa na taso na karbi' kayan hannun nasa ina masa sannu. Ledan mganin ya sakarmin shi kuma sauran ya karisa ya sauke da Hannunsa.
Sannan ya juyo ya na fadin"Mgangunanta ne in likitan yazo ki nuna masa."
Sai na gyad'a kai kaina a kasa ina fadin"Allah ya saka da alheri."
Ya amsa da Ameen.
Gefe ya koma ya jingina da Bango ni kuma sai na koma na zauna Shuru na wani Lokaci kafin yace"ba ki kira gidan ku ba ne?
Kaina na kasa nace"Ba ni da waya ne shiyasa."
Bai yi mamaki ba illah wayarsa da ya fito da shi ya na fadin"Ga wayata in dai kin haddace lambar."
Da Sauri nace"Eh na haddace."

Mikewa na karisa na karb'a ina fadin nagode ya amsa min da gyad'a kansa.
Gefe na koma na saka lambar Adda Fati na kirata har ta katse bata Dauka ba. Sai na kara kira sannan ta Dauka ina jin Hayaniya ta cikin wayar kai Tsaye nace"Adda ni ce Hasiya."
Dagachan bangaran tace"Hasiya. Hasiya kuna ina ne? Ga mu nan hankula tashe tun safe Maman Boy ta kirani tace Amma ba lafiya kun tafi asibiti ga shi bamu san asibitin da kuke ba kina ina ne yanzu!? Ina Amman ta ke?
Cikin Sanyin murya nace"Adda muna asibiti tun jiya. Amma kuma an bata gado."
Da Sauri Adda Fati tace"Kuna wani asibiti ne? Ga ni ga Inna Talatu ga Ramatu zamu taho."
Kallonsa na yi shi kuma hankalinsa na kan tagar dakin.
Tunani sunan da yaji ta ambata ya ke yi.

"Hasiya.?
Chapter 49 · 0% Book details