← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 69

Sashe 3

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da Fati ba. Ku yi mata addu'an da Fatan Allah ya Daidaita rayuwarta. Rokona shine kada ku yanke zumumci da ita ko bayan kasa ta rufe idona" Nasan ta zo ne ma da Safen gudun Fad'an Amma, ba sabo da ni ba. Gabadaya Hidiman auran nan Ramatu ne da mahaifiyarta sai Adda Fati kan lamarin ni ko sau d'aya ban ma sakata aciki ba. Ni fa ko ciwon Amma ya tashi bana jiranta tun kiran ta da na tab'a mata kan kan jikin Amman ya tashi ta fara min Fad'a da cewa komai ya ke faruwa ni ce Sila tun haihuwata Rayuwan mutane da Dama ba su wuta ba ciki har da su da Amma ni ce silar Cutar Amma da bata da mgani. Tun daga ranar na kiyaye mata, sai Amma ta sha ciwonta bata sani ba. Sai in taji daga baya ta fara kumfar bakin ba'a Dauketa bakin komai ba tunda Ba'a fada'a mata ba. Har tutiya ta tab'a yi a asibiti Lokacin da aka kwantar da Amma. Ban kirata ba Adda Fati na kira ta zo muka taho asibitin sai bayan an ba ma Amma gado ta kirata ta Fad'amata. Shine da tazo ta rika fad'an meyasa ban kirata na fad'a mata ba? Kuma a lokacin kai tsayen ta kalli Adda Fati tace"Naga kamar sun fi daukan ki wata Tsiya. Allah na tuba me kike da shi Ballatana shi Habibun? Ni dai da kuka raina ni nake da shi,kuma nake rufa muku asiri ni da Mijina" To me wad'anan kalaman ne kuma don in bata zo ba meyasa zan damu? Ina ta kokarin nuna yanayina ba komai ganin haka yasa sai Dakin ya Dauki shuru daga ni har ita ba mai wani mgana kowa na saka wasu abubuwan acikin ransa. Sallar mangariba ya Tada Ramatu ta fita tayo alwala tazo ta gabatar da sallaar tana cikin sallar ne kafin ta Idar, wayarta dake gefena ta Dauki neman Dauki. Ina dubawa naga Salisu ne sai da gabana ya Fad'i. A kasalance na dauki wayar ganin ya sake kira bayan kiran D'azu ya katse. Na latsa koren alamun Dauka na kara kunne ina jin muryansa cikin Shauki da murna yana Fad'in"Ramatu ga mu nan zuwa. Kada ku ji mu shuru mun bari mu yi sallar mangariba ne" Numfashina ne ya kwace min batare da na shirya ba, kuma da hakan ya fallasa ma da ni ce na Dauki wayar. Cikin Shauki da Soyayya yace min"Hasiya..! Hasiya. Numfashin ki Kad'ai ya isa ya shaida min da ke kika Dauki wayar nan" Sai na kara sakin Numfashin cikin Rashin Mafita tsoro nake ji kada wannan Shaukin da Muryan Salisun ta Rikid'e ta koma shaukin bakinciki da takaici. shiyasa na kasa mgana Dakyar na iya bude baki nace"Sai kun kariso. Allah ya tsare" Daga haka na yanke wayar ina jin kamar ana Saremin gwiwoyina. Daidai Lokacin da Ramatu ta Idar da sallar ko kafin ma ta nemi ba'asi tace"Salisu ne ko? Sun taso ne? Dakai na amsa mata sai ta mike Dakyar ta fice tana fadin bari tayi ma su Adda Fati mgana. Ni dai in da ta bar ni nan nake zaune wani Lokacin ina jin yayan mutane alamun ina cikin duniyarmu. Wani Lokacin kuma sai na tafi dogon zangon Tunanin da zan ji kamar komai ya tsayamin Dif! Bana jin yayar wannan duniyar tamu. Da mganar mu da Salisu an fi minti talatin kafin naji Hayaniyar cikin gidanmu tafi ta kowani Lokaci karfi. Tabbas ba Lafiya in dai hayaniyar gidanmu ta rika amsa kuwwa acikin Dakuna. Gabana ya yanke ya Fad'i ras!. Kaina ya saramin a lokaci d'aya, mikewa nayi da sauri jikina da gabbaina sai da suka amsa saboda karfin da na saka wajen tashi. Habiba ta fad'o dakin da sauri sai muka kusa cin karo da juna cikin Fitan hayyaci Tace"Salisu..Salisu ya yi hatsari.! Kamar saukan Aradu haka naji kalamanta,Shuu! Naji kunnuwana sun yi kafin naji Habiba na jijjigani, kafafuwana sun yi sanyi kalau din da suka kasa Daukata,sai ji nayi na tafi luu numfashi na tare da ji na da ganina suka Dauke gabad'aya. Ammh zuciyata harbawa ta ke yi da tunanin Ni HASIYA tabbas ina cikin TSAKA MAI WUYA..! Ba suma nayi ba,ina cikin Hayyacina sai dai ji nayi kamar na samu cutar shanyewan duka jikina, Tunda ina jikin Habiba ne, ammh gabbaina ba inda yake iya motsi wani irin mutuwar jiki ce ta kamani kamar wacce likitoci suka yi ma alluran kashe jiki. Naji mutane nata shigowa Dakin, a na ta maganganu a saman kaina ina jin Muryan Adda Fati tana Salati tare da Fadin"Mun shiga uku. Allah yasa ba abunda ya faru akan Abubakar ba ne zai maimaita kansa a kan Salisu ba" Shine ma! Naji na amsata a raina ai ba bu wani bambamci balle da naji Muryan Ramatu cikin Damuwa tana Fadin"Yanzu abokinsa Musabahu ya kirani cikin damuwa yana fad'amin. Ashe suna kokarin tahowa nan Daukan mu sai ga waya Shagon Salisu ya kama da wuta ga kayan mutane aciki. Shine a rud'e ya hau mashin din kaninsa ya tafi,to ya ce min bai ko karisa ba Mota ta tureshi ya Fad'a ma wani mai adaidaita suka yi fadin anrigizo tare" Sai salati ke tashi a dakin da Hayaniya. Muryan Inna talatu naji tana fad'in"Wani hali Salisun ke ciki? Ramatu tace"Yace suna Emergency har yanzu likitoci na kanshi ammh shi Direban adaidaitan ance nan ta ke ya rasu" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Su Adda fati ke ta faman maimaitawa. Gidan Gabadaya ya Hargitse har da makota masu shigowa jin gulma da ganin yadda za'a kaya. Muna nan ana ta maida zence ni dai tun bayan da Habiba ta jinginar da ni jikin garun Dakin Maman boy ban kara motsi ba, kuma ba Hawaye acikin Idanuwana. Ramatu ta zauna a gabana tana fad'in"Don Allah Hasiya kada ki damu Musbahun ya tabbatar min komai zai zo da sauki" Kallonta kawai nake yi ina jin kamar karo na farko da Naji kalaman Ramatu ba su burgeni ba. Tunda karya take Fad'amin babu abunda zai yi daidai karya take min. Na sani! Itama ai ta sani komai zai kwabemin ne kamar yadda ya kwabemin Lokacin aurena da Abubakar. Yana sona ina son shi ammh Kaddara da Tsaka mai wuyar da Rayuwata take ciki ta yanke aurena tsakanina da shi Har Abada. Daga kofar D'akin Maman Boy ma muna jin kururuwa da Muryanta, tare da mganan wasu suna fad'in"Ku rike ta mana" Ammh ina kururuwa take yi,kamar tsohuwar mahaukaciya, kamar an samin magad'isun mganin a jikina sai gani na mike kan kafafuwana, ko mutuwa nayi na dawo nasan muryan Sahura Matar Salisu, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha zuwa ta min kashedi kan mijinta. Ramatu na kokarin rikeni na Fizge jikina na fice,ina ratsa matan gidanmu da suka yi Dafifi kofar Dakin Amma. ba wuta ammh akwai hasken Farin wata ya haske tsukakken tsakar gidan namu Tarwai ana ganin komai. A gabanta na tsaya ana rike da ita, ihu take tana kuka tare da kuruwan ina nake sai ta kashe ni. Ba zato ba tsammani taji muryana a saman kanta ina Fad'in"Gani..Gani Sahura" Na fad'a cikin wani yanayi a muryata,gabadaya sai kallo ya Dawo kaina har da Ramatu da ta biyo bayana. Adda Fati a rude' ta riko ni tana Fadin"Ke Hasiya lafiyan ki kuwa? Amma na da cikin Daki tunda Labarin ya shigo gidan taji zazzabi mai zafi ya Rufeta ammh kiran sunana da Fati tayi sai ya tafi da kaso mafi girma na cikin sauran kuzarinta sai ga shi ta kife saman katifar da ta ke zaune tana makyarkyatan Sanyi. Adda Fati na kokarin janyeni Sahura ta kyalla ido ta ganni tayi kukan kura kwace rikon ta da kannenta mata suka yi mata,ta nufeni gadangadan tana zuwa ta shakemin wuya, shakar da har ina kakari da gaske take yi Halakani zatayi kuma Daman ta Dauki alwashi. Idanuwanta Jajir kanta ba ko Dankwali gashin kanta ya mike tsaye kamar mahaukaciya sabon kamu Cikin kuka ta jijjigani tana Fad'in"Daman sai da na ce kada ya aureki. Ga mata nan kala kala Dole sai ke? Ina zaman zamana da mijina zaki kashemin shi. Na rantse da Ubangijina in Mijina ya mutu sai nayi ajalin ki Hasiya ni zan kashe ki da Hannuna" Cikin ido na kalleta kafin nace"Nima zan so haka. Zan so ki kashe ni kamar yadda kika ce" Na fad'a cikin muryata mai cike da yakinin nima mutuwar ce ta Dace da ni. Kara makureni tayi tana ikirarin sai ta kasheni. Naji hannaye da yawa suna kokarin bambare hannayenta daga saman wuyana da kuma masu janyeni daga gareta. Ammh ni na kasa wani yunkuri na kwatan kaina. Na riga na gama sadaukarwa Rayuwa ta bata da amfani in dai zan rika zame ma duk wani mai sona Tashin Hankali da Bakinciki. gwara na Mutu kowa ma ya Huta.
Chapter 3 · 0% Book details