Sashe 48
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tahir ya kallesa cikin jin haushi takaici duk ya ishesa ya ma kasa mgana Saboda haushi.
Sadiq ne fa sanda suna makaranta ya sha kwana da Dalibai in ba su da lafiya a Clinic din makaranta, ya na mamakin wata irin zuciyaa Allah ya ba ma Sadiq.
Zuciyarsa ba irin ta kowa ba ne ya na da zuciyar Tausayi Imani da jinkai, zai yi maka wahala da Aljihunsa sannan ya taimake ka da karfinsa shi kam bazai iya wannan aikin ba. Bai kuma taba Fatan ya kwatanta ba ai aikin Allah suna da yawa.
Shuru suka zauna kowa na saka abunda ya ke sakawa a ranshi Tahir ya gaji da latsa wayarsa bayansa ne har ya kage yasa ya kalli Sadiq kafin yace"To a ina zamu kwana?
Sadiq bai kallesa ba yace"A bayana zaka kwana Tahir"
Tahir ya hararesa kafin yace"Dole kace haka mana. Yanzu nufin ka anan kan wannan kujeran zamu kwana?
Sadiq yace"Sai ka sauka kasa duka zabi ne"
Tahir ya kule kamar ya yi kuka ya gyara zamansa kan kujeran yadda Wuyansa bazai samu matsala da Safe ba yace"Wlh baka kyautamin ba ina zaman zamana ka taso ni zan kwana cikin Takura. Wannan ko Sultana ce zata haihu sai haka"
Sadiq na jinsa bai yi mgana ba sai da ya Murmusa. Tahir ya rigasa yin barci sai faman buge bugen sauro ya ke yi yana Tsaki shiko daman ba ya iya barci a asibiti ko ya ci wani abu ko ya sha wani abu.
Ya dad'e bai yi barci ba har wajen uku na Dare sannan barci ya kwasheshi sama sai biyar da rabi ya farka shima Tafiya ya rika ji ashe Nurses suka fara Zirga zirga shi ya tada Tahir wanda ya tashi yana Faman soshe soshe da Taba wuya alamun dai kwanciyar ba ta yi masa Dad'i ba. Fuskar nan ta shi kamar Buredi saboda kumburi.
Sadiq ya kallesa kafin yace"Mu tafi masallaci."
Tahir ya mike yana fad'in"Wash baya na ya 'kage."
Sadiq yace"Daman kai ai ba Namiji ba ne"
Tahir yace"Dole kace haka tunda ka Halakani da kwanan asibiti. ni dai ina Fatan wannan zuciyar taimakon naka ya yi sanadiyar Shigan ka Aljanna Sadiq."
Sadiq yace"Ameen tare da kai da ka ke taimakamin wajen kwanan asibiti."
Ya fad'a ya na Dariya Tahir ya Tureshi yana Hararansa har zasu fita sai ya ja ya Tsaya ya juya ya na kallonta barci ta ke sosai abun mamaki a yadda ta kwanta ko motsawa ba ta yi ba ta na nan a yadda ta Dunkule.
Tahir ya juya ya na kallon in da ya ke kallo kafin ya samu zarafin mgana yaga kawai ya fara tafiya har zuwa gabanta mamaki bai barsa ya yi mgana ya bi bayan shi yana Taba wuyansa da yaji ya sage.
Sadiq kujeran ya duka ya na Dan Bubbugawa ya rasa da wani suna zai kirata Tunda bai san sunanta ba. Daman barcin nawa a cikin tsoro na ke yin shi mai cike da mafarkan Amma, shiyasa ina jin ana Buga gefena nayi zaraf na tashi.
Kai na D'ago cikin Firgici Fes sai acikin idanuwansa na kallesa shima ya kalleni.
Mikewa ya yi kafin yace"Armm ki tashi ki yi sallah."
Kai na gyad'a masa kafin na Sauko da Siraran kafafuna a kasan Tayels din Asibitin kamar yadda na bi kafar tawa da kallo haka shima ya bi ta da kallo kafin yace" Kada ki yi yawo haka ba takalmi acikin asibiti"
Cikin sanyin murya nace"ban zo da takalmin ba ne."
Na fad'a daidai ina ta shi Tsaye kuguna ya amsa da bayana jikina ya yi tsami na cije baki ina kara Daidaita natsuwata tare da gyara Lullubin zanin jikina ko D'anwali ba bu a kaina Tarin suma na ko gyara babu shi ya saka kan nawa ya cika.
Ba tare da Tunani ko shawara ba Sadiq ya cire takalmin kafarsa ya mika min ya na fadin"Zaki iya saka nawa?
Yadda na dago kumbararun idanuwana na kallesa haka Tahir shima ya kallesa cikin mamaki da Al'ajabi lalle Sadiq kullum cikin yin abubuwan ban mamaki ya ke yi.
Ni kuma na kasa mgana Alherin bawan Allah gareni mai girma na kalli Takalmin har ya ciresu ya Turomin gabana kafin nace"sun yi min yawa."
Kai Tsaye yace"Ki saka hakanan in na fita sai na siya miki ko silifas ne.".
Dago kaina nayi na kalleshi idanuwana cike da kwallah nace"Nagode sosai Allah ya jikan magabata."
Bai amsa ba ni kuma sai na zura kafafuwana cikin takalmin ina Ruwan Sauro ko kwatan takalmin ban ci ba, Ina da Doguwar kafa sai dai ba kauri ne ina kallon kafata sai da dariya ta kamani cikin mirnishin nace"Kafata karamace ka ga ni ban ci ko Rabi ba."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Nagani."
Sai alokacin da na kara Dagowa na kula da Tahir ya kafeni da ido ya na kallona cikin mamaki na kallesa na kuma kallon Sadiq ganin inda na ke kallo yasa ya juya ya na fadin"Abokina ne Tahir."
Sai na jinjina kai cikin sanyin murya nace"Ina ina kwana."
Tahir ya amsa da Lafiya lau. Ya na kara kallona daga sama har kasa.
Hasken Fatata sai ya fara kashe masa ido ballatana ga hasken fararan kwai sai Fuskar ta yi wani 'Dau da ita.
Sadiq yace na samu wata Nurse in tambayeta in da zanyi sallah.
Sai na amsa masa suka fice suka barni kamar yadda yace haka nayi d'in wata Nurse na tambaya ta nuna min bayi na shiga na kama ruwa na yo alwala. Duk da ba na sallah gwara na wanke jikina da kafafuwana da suka yi min tsami.
Dawowa na yi na zauna in da na tashi Amma na ke son gani kamar sun sani sai ga shi wata nurse tazo tace na biyota da Sauri na tashi na bita zuwa wani Daki akwai gadaje uku ne adakin Guda d'aya akwai mutum Ashe Amma ce har an kawota dakin da zata Huta.
Ba ta dai Tashi ba ta na barci na karisa kusa da ita ina kiran sunanta jikina ya na rawa Nurse din da ta kawoni tace"Alluran barci na tare da ita saboda ta samu hutu. Jininta ya yi kasa ne sannan akwai low sugar"
Bayanin da mutumin nan ya yi min kenan au Abubakar Sadiq yace sunan sa daman ma su suna Abubakar masu Tsausayi ne da jinkai.