Sashe 18
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Zumbur ta mike lokaci d'aya tana watsar da Remot din hannunta. Zata iya banzarta da kiran kowa ammh ba zata iya kyale kiran Innani ba. Uwar mijin da ta yi mata rikon uwar da ta rasa tun a zamanin baya.
Uwar da ta Fifita son da take yi mata sama da d'anta data haifa. Ita ko mai zata saka ma Innani? Ba bu ban da ta rika yi mata Biyayya da yi mata duk abunda take so har ma da wanda ba ta ce tana so ba. Da sauri ta fita daga Falon a kofar shigowa suka ci karo da Inanni ta fito tana dogara sandarta.
Kai wannan tsohuwa da Jaraba ta ke, ta tsufa har ta duke sai ma da taimakon sanda ta ke iya tafiya, Kanta gabad'aya ba baki sai Furfura. Fuska duk ta tamuke sai dai Fatar taushi da hutu tare da jin Dadi ammh mganar gaskiya Inanni zata bama Chasa'una baya.
Umma ta tsorata da taga Inanni na kuka yarkace yarkace. Da Sauri ta riko hannunta tana fad'in"Ga ni nan Inanni lafiya? Ko yunwa kike ji ne?
Domin a tunanin Umma, Hajiya mama bata kai ma Innnani abun karyawanta ba. Tunda yau lahadi megidan na nan kuma ba da wuri suke karyawa ba. Tasan Innani da abinci kamar mai tsotsan ciki.
Shashenta baya rabo da abinci har cikin Dare sai ta tashi in ba abinci ta fashe da kuka.
Innani jin Muryan Umma sai taji sanyi ammh jin Abunda tace ne yasa ta kwace hannunta tana fadin"Matsa ba ni waje. Hala bani da aiki ne sai cin abinci kamar wata tsutsa!? Ana ta rai mai Daraja wa ke ta abinci?
Umma ta sauke muryanta kasa tana Fadin"Yi hakuri Innani mu je ciki sai ki fad'amin me ke faruwa?
Ta fad'a tana kokarin kamo Sandan hannun Inanni, ganin haka yasa Innani ta turje tana fad'in"Ina naga ta shiga ciki Salamatu? Ina nan tsaye har sai Sulaimanu ya fito"
Umma ta kalleta cikin mamaki kafin tace"Wani abu ne ya faru Innani?
Sai kawai Innani ta kalli Umma ta faahe da kuka da karfi tana Fad'in"Ina zan iya fada miki. Ai sai hankalin ki ya tashi bari dai shi Sulaimanun yazo shi Tunda namiji ne ya na da Dakiya zai iya saurarana"
Kafin Umma tace wani abu Mallam Tajuddeen maigadi ya zo in da suke da Sauri yana fad'in"Subhanallah Hajiya lafiya kuwa?
Ya fad'a yana kallon Inanni cikin damuwa ganin tana kuka, duk da kukan Innani in dai kana gidan Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi to ya zame maka jiki. Innani ko kallonta ka yi in bai yi mata ta ga daman ta fashe da kuka.
Innani na jin muryan Mallam Tajudden ta watsake ta daina kuka Umma ko ce masa tayi"Bakomai Mallam. Koma bakin aikin ka kawai"
Har ya juya Inanni tace"Ya koma ina Salamatu? Ai gwara ya tsaya in Sulaimanu ya fito aji in dole sai an had'a da ayoyin Allah. Mallam Saju tsaya tsaya Sulaimanu ya fito"
Umma ta rike haba cikin mamaki kafin tace"Innani Abban Su siyama fa bai fito ba! Ko kin kirashi ne?
Innani tace"Na aika yarinyar taki Sulsana ta taso min shi. Ina ya ga ta barci Magajin gida gabad'aya ba'asan inda ya ke ba"
Umma ta bude baki, kafin ta rufe Mallam Tajudden ya kalleta ta kalleshi kafin ta juya tana kallon Inanni da ke fad'in"Wai ina Sulaimanun ne? Kaji min watsewa ni Dije ni uwarsa ma na taso kan kafafuna shi uwar me ya ke yi da bai fito ba har yanzu? Kada fa na zama uwar banza ne yasa ban je har shashen na shi na taddo shi ba, na tsaya a bangaran salamatu"
Sai da Umma ta Murmusa kafin tace"Innani wata Sultanan? Sultanan da ke cikin daki tun dazu?
Da wani kallon Innani ta bita da shi kafin ta yi kwafa tace"Lalle ja'irar yarinyar nan da ni take mgana. Tunda taki zuwa ke uwarta je ki taso min Sulaiman."
Umma ta yi kokarin riko Innani tana Fadin"Mu shiga ciki Innani. Magajin gida kuma lafiyansa kalau. Kin manta yana Zariya yaje makaranta?
Innani ta yi shuru alamun Nazari kafin tace"Tsakaninki ga Allah Salamatu kwananki nawa baki yi mgana da Magajin Gida ba?
Umma tace"Na yi mgana da shi jiya ma Innani"
Innani ta kalleta kafin tace"Sai kin Rantse zan yarda da ke Salamatu."
Umma ta yi mirmishi Tana kallon Mallam Tajuddeen. Wanda ya juya shima yana mirmishin Diraman Innani da mutum ba ya gajiya da Dariya.
Umma sai da ta rantse sannan Innani ta amince da ita ta shiga Shashenta.
Ta zauna kan kujera ta na share hawaye da Haban dankwalin kanta.
Umma ta zauna gefenta ta ja Haban zaninta mai kyau da Tsada tana Share ma Innani hawaye cikin Sigan lallashi ta ke fad'in"Ki yi hakuri Innani. Magajin gida yana nan lafiya zai zo ya ganki kwananan in sha Allahu"
Innani ta yi mirmishi kafin tace"Shikenan tunda kin tabbatar da yana lafiya. Ni daman rashin samun sa ta wayar zamanin nan ne ya Dagamin Hankali. Ammh tunda ke uwarsa kin tabbatar da yana lafiya ba ni da tacewa"
Umma ta yi mirmishi kafin tace"Yana lafiya Innani in sha Allahu. Zan kuma sa ya kiraki in sha Allahu.
Innani ta gyada kai batace komai ba. Umma ta mike tana fad'in"Innani me zaki ci in kawo miki?
Innani ta yamutsa fuska kafin tace"Na riga na ci goro salamatu zauna abun ki. Nagode sosai Allah ya shirya miki zuru'a, yadda kike kula da lamarina kema Allah ya shiga lamarin ki"
Umma ta mike ta na ta amsawa da Ameem Ameen.
Duk da yadda Inanni ta ke da Tsine Tsine akwai saka albarka da kyawawan addu'o'' a bakinta. Umma kitchen taje ta hado abun karyawan su,Ta leka da kanta ta kira Sultana wacce har ta yi wanka ta saka Doguwar riga baka. Kai tsaye tace"Kina Fiki fiki da ido. Sai ki fito mu karya"
Dakyar ta fito tana Tafiya sannu Sannu taki dagowa su had'a ido da Inanni, ita ko sai faman Hararanta ta ke yi tana kyafci. Umma na kallon su tana Dariya. Bata yi mgana ba sai da Innani ta tabe baki tace"Bar wani rabe rabe. Kiyuwa ko? Kin koyi bakar Dabi'a wajen yaran chan na Suwaiba kamar ni na aike ki ki k'i zuwa ko?
Sultana ta zauna ta rab'e bayan Umma tana fadin"ki yi hakuri Innani"
Innani ta washe baki kafin tace"Me kika yi min yar nan? Ke dai bari Uwar ki tace magajin gida na lafiya. Ni daman lafiyarsa ya dameni in ta ni ce ai Sulaimanu ya kwana ya na barcin asara Mutumin banza kawai zai ce duk koken koken da nayi bai ji ba ne Salamatu?
Umma na Had'a tea tace"Bai ji Ba Innani. In da yaji kinsan zai fito shi da baya son ganin ki cikin damuwa."
Innani ta tabe baki bata kara mgana ba, sai dai Umma na janta da mgana Jefi jefi.
Suna gama karyawan Sultana ta kwashe komai zuwa kitchen. Daganan tana fitowa ta koma Daki ta dauki aikin makarantarsu tana Dubawa. Umma da Innani na Falo sun tsinke da Hira.
daga dakin tana jin muryan Innani a sama tana mgana da Anty Surayya sai faman bude murya ta ke yi.
Sultana ta Dafe kanta a fili ta Furta"Innani Hayaniya da kanta"
*****