← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 69

Sashe 47

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tahir ke kiransa ya na Dagawa yaji Muryan Tahir cikin Firgici yana fad'in"Sadiq ka na ina ne? Har daya saura na dare baka dawo ba?
Wlh na zata ka dawo gida barci ne ya kwasheni sai farkawa na yi naga baka dawo ba."
Sadiq ya shafa kansa da Hannunsa guda d'aya kafin yace"Eh ban dawo ba."
Cikin Tashin Hankali a muryan Tahir yace"Sadiq ba ka dawo ba? To ka na ina ne?
Kamar bazai yi mgana ba sai kuma dai yace"Ina asibiti ne."
A firgice Tahir yace"Asibiti? Innalillahi me ya faru da kai?
Tahir ya fad'a gabansa na fad'i saboda Matukar Razana ya razana da rashin Dawowar Sadiq abunda bai taba Faruwa ba ne.
firgicinsa kada wani abu ne ya samu Sadiq din ya shiga Uku.
Sadiq yace"Eh ina asibiti ne nan cikin Samaru."
Tahir yace"Baka da lafiya ne? Sai da ya juya ya kalleta ta na zaune ta had'e kai da gwiwa daga ganinta ta na son mahaifiyar nan nata shiyasa ta ke cikin Damuwa da kuka.
Kafin ya yi ajiyar rai ya ce ma Tahir"ba ni  ne ba ni da lafiya ba Tahir."
Tahir cikin kosawa yace"Ka na so ka kasheni da Zullumi ne Sadiq? Waye ba shi da lafiya.?
Sadiq yace"Taimako na yi Tahir. Wata baiwar Allah ce."
Tahir ya jinjina kai kafin yace"Zaka dawo ne?
Shuru Sadiq ya yi Kara kallonta ya yi ita kad'ai ne bai kamata kuma ya tafi ya barta ita kadai ba. Ga ta karamar yarinya ba bu mataimaki a kusa da ita.
Kai Tsaye ya ce"An ya? Ban tunanin haka."
Tahir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Wani asibiti ne? Sai na zo na same ka."
Sadiq yace"Ka yi zaman ka Tahir lafiyata kalau fa."
Tsaki Tahir ya ja kafin yace"Dilla ka Turomin sunan asibitin gani nan zuwa.."
Daga haka ya kashe wayarsa.
Sadiq ya Sauke wayar daga kunnensa shi kanshi bazai iya fad'an sunan asibitin ba. Sai da ya fita daga Haraban Asibitin ya ga sunan asibitin sannan ya Rubutama Tahir ya tura masa.

Dawowa ya yi cikin asibitin ya isketa har ta yi barci ta d'ago kanta saman masagin kujerun da ke wajen domin zaman masu jinya.
Daga gani a wahale take numfashin ma nata a wahale ya ke fita, kauda kansa ya yi ya na kallon gefe. Bayan ya zura duka hannuwansa a aljihun wandonsa yana nazarin wasu abubuwan.
Kudad'en hannunsa gabadaya sun kare, Allah yasa ma ya na yawo da Atm dinsa da baisan yadda zai yi ba kudin bankinsa sun yi kasa akwai bukatar ya kira Abba ya sake Turo masa kudad'e.
Jiya ba su yi mgana ba Shekaranjiya  ne ya kirasa da kansa saboda Matsalan Innani tsohuwar nan matsala ce mai zaman kanta a gidan Abba.
Wai sultana babanta ke son taje shinkafi ta yi hutu tunda ta gama Jss3 zasu shiga Ss1 ita da Siyama. Umma ta shirya mata Tafiya Abba kuma daman bai da matsala, Ammh Innani naji ta fara Tsine ma Mahaifin Sultana ta na kawo Labaran da bata san Tushen su ba ballatana makamar su ba.
Akan Sultana bazata je wajen Mahaifinta ba, ban da Innani da Shegen kafiya da Rikicin Tsufa ta ina zaki raba y'a da mahaifinta? Duk da Sultana yarinya ce tasan Mahaifinta kuma ta na son shi tare da Sauran yan'uwanta.
Umma ta kirasa ta fad'a mai Abba ya ce Sultana ta zauna Tunda Innani ba ta so taje. Shi kuma sai ya kira wayar Innani ba ta shiga sai ya ce ma Umma ta kai ma Innani wayar zai mata mgana Umma tace ya Rufa mata asiri kada Innani ta ce ita ta kai kararta wajen Magajin gida.
Dalilin haka yasa ya kira Abba ya ce in ya shiga wajen Innani ya kirasa zai yi mgana da ita. Innani dole ta yi shuru da bakinta Tunda ya ce mata Sultana zata tafi Shinkafi taga Babanta da yan'uwanta Dole Innani ta amsa, ammh kuma jiya sun yi mgana da Umma tana fad'a masa Innani ma ta shirya kayanta tace kafarta kafar Sultana kada shitu ya cuta mata ya ganta marainiya.
Shi ko kara bi ta kanta bai yi ba innani case ne mai zaman kanta a wannan gidan in ka toshe nan ne sai kaji ta kara balle wata kofar, yasan zuwa zatayi ta yi ta rashin Mutumci sannan ta hana yarinya sakewa a gidan Ubanta tare da sauran yan'uwanta.

Ga shi ya lura Mahaifin Sultana Tsoron Innani ya ke ji in ta zaunar da shi ta na ta zage zage Har Allah ya isa ta sha masa ammh iyakarsa ya ba ta Hakuri ammh Tsohuwar nan har yau ba ta Saduda ba. Kila sai ranar da Ciwon Ajali ya kamata ba, ammh ki na Tafiyar da kyar ga makanta kice sai kin je, Haushi ma yaji yasa ya ce ma Umma ta barta taje din taci abunda zata ci achan.
Fitowar Nurse shi ya katse masa Tunanin da ya lula. Ta na gayamasa jikin Amma da Sauki nan da zuwa anjuma zasu kawota dakin da zata Huta.
Ni kam mafarki na yi naga su Adda Fati sun zo asibiti suna ta kuka sai na Farka a firgice ina kiran sunan Amma.
Sai na hange shi yana mgana da ma'aikaciyar Jinya. Daidai lokacin da na mike baya na ya amsa na duka ina wash ita kuma Nurse din ta tafi,da Kyar na karisa gabansa ina dingishi kallonsa na ke yi da Kumburarun idanuwana Tun kafin na yi magana da Sauri yace"Ta na samu sauki. sun ce zuwa anjuma zasu dauko ta zuwa Dakin da zata Huta."
Sai da yaji karfafan ajiyan zuciyan da na Sauke kafin hawaye su gangaromin ban damu da Sharewa ba na kallesa ba ni ya ke kallo ba na Fahimci ba shi da Dabi'an yawan kallo shi,cikin Shakkiyar muryata nace"Nagode sosai. Allah ya saka da Alheri Allah ya jikan magabata."
A hankali ya amsa da Ameen kafin kai tsaye ya kalleni ya na fad'in"Ki je ki zauna naga kina dingishi ne"
Da kai na amsa masa kafin na juya ina Tafiya sannu kafata ba takalmi sai lokacin ya lura da haka.
Da wani irin kallo ya bi ni, kallon da ko Sultana da taso a cikin gidan su a gabansa bai taba mata irin shi ba.
Kallo daga sama har kasa, Tabdijam ya dad'e ya na mamakin sirantarka Sultana sai yau da ya ga wannan yarinya ya san Sultana gwaiwa ce kafafunta ya kalla kanana sirara kamar na yara kanana.
Ta ya mutum zai rika yawo ba takalmi kuma ta na mace? Macen ma acikin asibiti kafarsa ya kallah yaga takalminsa mai hanci ne sannan in ma ya bata bazata iya sakawa ba.

Yana da Babban kafa da Tsawo da Tudu lamba arba'in ne ya ke sakawa.
In ta saka takalminsa saboda Siranta bazata iya daga kafarta ba ma.
Har taje ta zauna ya na kallonta ta gefen ido yana kiyasatawa a tunaninsa bazata wuce sa'ar Sultana ba. Yarinya karama a barta  da mara lafiya haka? Ina babansu da sauran yan'uwanta?
Shi kadai ya ke ta wannan Tunanin a ranshi, ya na kallonta ta na ta share hawaye daga gabanta ya matsa saboda baya son kuka barin ma na mace Raunana masa zuciya ya ke yi saboda shi mai Tausayi ne.
Kujerun da ke gefe chan da shigowa babban falon asibitin kusa da ma su ba da kati ya samu kujera ya zauna yana jin sanyi sanyi yasa ya saka hannayensa cikin Aljihun Jaket din da ke jikinsa.
Ita ya ke kallo yaga ta kara Dunkulewa cikin zanin da ta yi mayafi da shi ta Dauki kafarta ta dora saman kujeran ta dunkule jikinta waje daya daga alamu itama ta na jin Sanyin da ya ke ji.
Muryan Tahir yaji ya na Tambayan ma su ba da kati. Sai ya saka baki ya kira sunan shi ya juyo ya na kallonsa kafin ya yi mgana da su kila ya na fad'a musu ga wanda ya ke nema chan.
Wajensa ya zo ya na fad'in"Ka ji ni shuru ko? Kasan dare ne na jima ban samu abun hawa ba."
Sadiq ya matsa masa gefensa ya zauna ya na fadin"Ai sai da nace ka yi zaman ka ba sai ka zo ba."
Tahir ya kallesa lokaci daya yana kara bin asibitin da kallo. Har bangaran Hasiya dake dunkule waje daya cikin Sigar Tambaya ya kalli Tahir kafin yace"wannan ce mara lafiyam?
Ya fad'a ya na nuna Hasiya, Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Mahaifiyarta ce.".
Tahir ya jinjina kai kafin yace"Uhm Allah ya sauwake."
Sadiq ya amsa da Ameen shuru na wani Lokacin Tahir ya gaji yace"Yanzu ina mara lafiyan?
Sadiq yace"Ta na ciki sai anjuma zasu kawota dakin da zata huta suka ce."
Tahir yace"To ai shikenan ma sai ka tashi mu tafi gida. Tunda ga yarta sai ta zauna da ita."

Wani kallon baka da Hankali Sadiq ya yi ma Tahir kafin yace"Sai mu tafi mu barta ita kad'ai a asibitin nan? Baka ganin yarinya ce karama"
Tahir ya ce"To mene? Ba taimakonsu kayi ka kawo su asibiti ka kuma biya musu komai to me ya rage Sadiq?
Sanin Halin Tahir yasa ya yi masa Banza Tahir yace"Ba dai tunanin kwana a asibitin nan ka ke yi ba?
Sadiq yace"Shiyasa nace maka ka yi zamanka ba sai ka zo ba."
Tahir ya bude baki ya Rufe saboda mamaki kafin ya sake budewa ya na fadin"Nufinka anan zaka kwana Sadiq?
Sadiq yace"Anan zamu kwana dai. In ma ka fita yanzu bazaka samu abun hawa ba."
Takaici yasa Tahir ya kasa mgana Sadiq ya kallesa ya na Danne Dariya kafin yace"Allah yasa a mizani Tahir Yusuf Daura."
Chapter 47 · 0% Book details