← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 69

Sashe 66

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Tahir ya fara tsorata ganin bai yi motsi ba sai kuma yaga ya juyo idanuwansa suna rufe bai bude su ba sannan bai yi mgana ba.
Da sauri ya kara kiran sunansa ya na fad'in"Kana jina?
Sai alokacin Sadiq ya bude idanuwansa da suka koma gauta saboda ja.
Cikin Tsoro Tahir yace"Baka da Lafiya ne?
Sai Sadiq ya samu kansa da Dagamai kai Lokaci d'aya ya na fadin"Ba ni da lafiya Tahir. Ba ni da lafiya."
Cikin wata irin murya da ta kara Tsorata Tahir da Sauri yacr"Me ke damunka Zazzabi?
Ya fad'a lokaci daya ya na Tattaba jikin Sadiq.
Shi kuma sai ya kara mulmulawa saman kafita cikin nishi yace"Rufamin abun rufa sanyi nake ji."
Jiki na rawa Tahir ya mike ya Dauko Bargon Sadiq ya lulluba masa ya na fadin"Maleria ce inaga. Ka dan huta zuwa anjuma sai ka tashi ka sha magani bari na fita na karbo maka a wannan chemist din"

Bai jira cewar Sadiq din ba ya mike bayan ya zare ma Sadiq din takalmin kafarsa ya maida ma'ajiyar takalman sannn ya dauki kudi a jakarsa ya fita Lokaci d'aya ya na jawo ma Sadiq kofar dakin
Sadiq ya dago ya na bin kofar da kallo kansa ya Dafe da hannu bibbiyu lokaci d'aya ya na fadin"Dama ace.  Dama ace. Daman tun farko na fad'i gaakiyata  da duk ban shiga wannan halin na Tsaka mai wuya ba."
Ya karishe fad'a kamar ya fashe da kuka.
A lokacin tunani da Hankalinsa ne ya ke jin ya rasa gabadaya.

FAA'ALUL LIMA YURID
LAIN YUSIBA NA
ILLAMA KATABALLUHU LANA.

Kuyi hakuri an samu kuskure a shafi na sha bakwai wajen Rubutawa, keyboard d'ina ke sauyamin Haruffan rubutuna.
Da masu ganin Gusai suna tunanin wani gari ne, suma su kula Gusau ne ba Gusai ba.
Nagode.

*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*FATAN ALHERI DA SAKON GODIYA ZUWA GARE KU*

*AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH)*
*MARYAM JUMARE*
*NANA HALIMA(MASOYIYA)*
*HAFSAH HAFNAN(SAHIBATU)*

_*Nagode muku bisa yadda kuka yi ta Hidima da wannan littafin, HasiyarAssadiq tace ta gani kuma ta yaba, Innani kuma tace dukkan ku Allah ya yi muku albarka Amin*_

*20*

Sai bayan Fitar Tahir yaji wani mugun zazzabi ya kara rufeshi.
Nan da nan ya fara rawan Sanyi Hakoransa na had'uwa waje d'aya.
Kansa kuwa kamar zai Tsage gida Biyu Tsabagegen yadda ya ke sara masa, jijiyon kansa sun mike gabadaya Rad'au a saman kansa saboda Halin da ya ke ciki.
Idanuwansa biyu Tahir ya dawo da magangunan da ya siyo masa.
ba domi  Tahir ya taimaka ya tada shi zaune ba ji ya yi kamar bazai iya ma tashi ya zauna da kansa ba.

Tea mai kauri Tahir ya had'a masa yace bazai sha ba , shi kuma ya lallabeshi kan ya samu ya sha saboda ya samu sha mgani.
Dalilin haka yasa ya sha kad'an ammh ji ya yi ba dad'i kamar ya na shan mad'aci saboda bakinsa da ya zama wani takaf kamar wanda ya yi shekaru cikin jinya.
Tahir ya ballo masa magungunan Paracetamol ne sai maganin maleria d'in nan mai warin kudin cizo. Shi ba ya son magani ya fi shiri da Allura ammh Bala'in Tahir yasa sai da ya sha magungunan gabadaya sannan ya kyalesa ya koma ya kwanta Lokaci d'aya ya na kara taba goshinsa jin har lokacin da zafi.
Ya dad'e barci bai daukesa ba ya na jin Tahir bi ni bini sai ya lekosa ya na masa sannu tun ya na daga masa kai in yajisa har wani wahallalen barci ya Daukesa mai cike da Tararradi da zullumi.
Bai san haka ya yi barci sosai ba sai da ya farka cikin ikon Allah yaji zazzabin jikinsa ya sauka sai dai sarawan kan kad'an. lokacin da ya yunkura ya mike sai yaji ba jirin Tunda ga shi har ya iya mikewa da kansa batare da taimakon kowa ba.
Tahir ya kallah da ya kwanta a kasa wayarsa na saman cikinsa kila wajen Dannan wayar ne barci ya Daukesa bai sani ba.

Yasan ba shi da laulayin yawan ciwo sai ya jima bai yi ciwo ba, in ko ya yi Ciwo sai dai ko ciwon kai in ya yi Tsanani ne zazzabi shi Allah ya Tsare shi da ciwukan zamani irin su Ulcer ko Typiod.
Jin ya samu karfin jiki yasa ya dibi Ruwa a buta bayan ya Dauki karamar wayarsa ya kunna Fitila.
Ruwa ya zuba a karamar buta sannan ya yi addu'a ya bude kofa ya fita daidai lokacin da karfe uku na dare ta cika a wayarsa. Ba shi da tsoro daman Tahir ne ke tsoron Fitan Dare ba Sadiq ba shi da ko a gida ko karfe nawa ne zai iya fitowa Haraban gidan su in yaji wani motsi to anan ma shi ke raka Tahir in lalura ya tashe shi cikin Dare.
Kai Tsaye makewayi ya haska ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito a tsugunna a kan damdamali ya yi alwala sannan ya koma Daki har Lokacin Tahir na ta barcin bai ma san ya tashi ba.
Darduma ya shimfida bayan ya cire kayan jikinsa ya saka wata farar Jallabiya ta mutanen Saudiya. Yasan akwai sallar mangariba da isha'i da ke kansa ba shi su ya fara yi kafin ya mike ya yi salla raka'a Biyu ya jima acikin Sujjuda ya na ta addu'a sannan ya Dago ya yi tahiya ya sallame nan ma d'in ya jima ya na kirga da hannunsa kafin ya daga hannunsa sama ya na addu'a na tsawon wani lokaci sannan ya shafa.
Bai koma kan katifar  ba sai ya kishigid'a saman darduma ya na jin Kwakwalwarsa ta na shiga wasu Tunane Tunanen da a dazu kwata kwata ta tsaya cak. Iya hangen nasa ya gama Hango masa aikata Rokon Amma daidai ya ke da rasa goyon bayan wasu daga cikin Ahalinsa.
In yace kuma ya shawarce su ya bata komai domin ba bu wanda zai rama masa baya acikin wannan Halin da ya ke ciki.
A cikin zuciyarsa ya cika da Tausayinsu kuma ya na so ya taimaka musu ammh bukatar Amma ta yi tsauri ta kuma saka masa wani irin Dabaibayi ne mai wuyan fita. Ga shi ya riga ya furta tun farko shi maraya ne babu yadda za'ayi kuma daga baya ya sauya mgana.
Tunanin mafita kwakwalwarsa ta Zurfafa aciki ammh sai dai har barci ya kwashe shi bai samu wata mafita mai kyau ba duk Mafitan da ya hango sai yaga bazata bulle da shi ba.
Acikin barcin nan da ya koma sai ya yi mafarki ko nace kamar Allah ne ya nuna masa sakamakon zabin da ya mika garesa.

Ganinsa ya yi a wani Daji ba gida gaba ba gida a baya. Shi kad'i ya na ta faman bulayi ya rasa hanyar da zata fitar da shi Kamar daga sama yaji an kwala masa kira ya na juya sai ya ganta wata Doguwar mace ammh kuma ta saka mayafinta ta yane Fuskarta ba ya iya ganin kamaninta sai dai kwayan idanuwanta.
abun mamaki kuma da Tsohon ciki a jikinta.
Ya na ganinta sai ya yi Saurin karisa gareta ya riko hannunta suka fara tafiya tare. Ba zato kawai sai ga Sultana ta sha gabansu ba ta tsaya ba ita ta saka karfinta ta raba Hannunsu waje daya ma'ana ta raba tsakaninsu ita ta shiga Tsakiyarsu ta jimke hannunsa ta ja shi suka cigaba da Tafiya.

Waiwaye ya ke yi ya na kallonta ta na kuka ta na nuna masa bata da kowa da ita da abunda ke cikinta sai shi kada ya tafi ya barta. A cikin mafarkin yaga sanda ya kwace hannunsa acikin na Sultana ya ruga a wajenta ya riketa gam! Sultana na ganin haka sai ranta ya baci ta kara Dawowa zata rab'asu sai ba ta yi nasara ba, shi baisan ko daga ina ba ne? Yaga dai gabadaya yan'uwansa sun yi layi a gabansa da taimakon su suka raba hannayensu suka saka masa a na sultana shi kuma sai ya had'a da hannun wacce bai ga Fuskarta ba ya rike tare da na Sultana.
Umma ce ta bayyana gabansa ta kwace hannun Sultana ta fara tafiya da shi sai sauran yan'uwansa suka mara mata baya.
Yaga har da Abba shima bai bi bayansa ba ta karshen itace Innani ita ta jima a tsaye ta na kallonsu sannan ta juya ta bi bayan su Abba suka bace masa daga Daji nan da ba kowa daga shi sai wannan yarinyar da bai ga fuskarta ba.
Gudu ya ke yi ya na ta kiran sunan Abba da Umma ammh ko me kama da su bai gani ba Sai yaji wata murya da ya na jinta yasan ya santa ta kira shi da karfi.

"ASSADIQ.."

Yana juyowa sai idanuwansa ya gane masa itace. Abunda ta yane fuskarta da shi ya yaye da kansa ta bayyana a gabansa ta na masa mirmishi. Har gabansa ta kariso ta dauki hannuwansa guda d'aya ta Dora saman cikinta sai yaji motsi kamar abunda ke cikinta ne ya motsa a fizge yaji kalaman ta" Ni da abunda ke cikina ba zamu taba barinka ba. Zamu zauna tare da kai sannan zamu tayaka dawo da sauran Ahalin ka."
Hasken Fatar ta ya haske masa ido da yasa ya farka a firgice gabadaya jikinsa ya jike da Zufa.
Cikin Fitan Hayyaci ya Furta

"HASIYA."
Chapter 66 · 0% Book details