← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 69

Sashe 22

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wani abu na gargajiya Sadiq na Cinsa su ne cimarsa ma tun zamanin suna Hostel a Cikin Abu zariya. Tunda daga shi Tahir nan suka samu Shedar Degree din su na Farko. Ko da ya koma Daki Tahir na zaune in da ya barshi da waya a hannunsa ammh ya gama shan lemunsa da Cake dinsa ya kuma watsar da ledojar da goran anan bai kwashe ba. Ko mgana Sadiq bai masa ba ya tattara dattin ya fita waje ya watsa cikin Abun shara.
Yazo ya Dauko Filet karami ya juye awaransa da yajinsa tana tashin Tiriri ya samu gefe ya shimfid'a Darduma ya zauna. Daman ya wanko Hannunsa da ya fita waje ya yi bismillah ya fara cin awaransa Hankalinsa kwance.
Tahir na kallonsa Jefi Jefi shuru dakin ya Dauka na wasu mintina kafin Tahir ya kauda shurun da cewa"Jb na gaisheka."
Sadiq ya jinjina kai bai yi mgana ba sai da ya cinye awaran bakinsa. Sannan yace"kun had'u ne?
Tahir ya ce"A ina? a Chart muka yi mgana da shi."
Daganan Sadiq bai kara magana ba sai da Yaji cikinsa ya kusa cika, sannan ya mike ya isa ga Fridge ya Bude ya Dauko Ruwan gora guda d'aya yana juyowa yaga Tahir gaban a waransa ya Dauka yana Fad'in"A ina ka siya awaran nan? Allah ya sa ba wajen kazaman masu awaran nan na bakin Titi ba ne?
Sadiq ya tsaya kyam yana kallon Tahir bai samu masa mgana ba illah ya Duka ya ja Filet din awaransa yana Fad'in"Ko ma nan ne ina ruwan ka?
Baka ce ka koshi ba?
Tahir yace"kamshinta ne ya yi min Dadi. Mu ji Allah ya sa da Dad'i"
Sadiq ya Daure fuska kafin yace"Kasan Allah? Bazaka ci ba."
Tahir ya yi dariya ya tura na Hannunsa baki ya tauna yana lumshe ido Kafin yace"Kai..Wow. da'di k'aramin don Allah"
Sadiq ya ce" ka fita ka siya in ka matsu"
Tahir yace"Ga shi ka siyo mana. kasan Allah? Nima sai na ci"
Tahir ya mike Sadiq ya mike suka Fara kokuwan awara Tahir na sai ya ce Sadiq na bazai ci ba.
Suka Fara Zagayen Dakin da gudu Tahir na Bin Sadiq a baya. Daman so ya ke ya gajiyar da Sadiq din ya yi fushi ya ba shi awaran ahakan ce ta Faru daga karshe ya dungura masa Filet din yana Fadin"Tahir.."
Da Sauri Tahir ya katse shi da Fadin'"Nagode Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi."
Karamin tsaki yaja ya koma saman katifa ya kwanta ya juya ma Tahir baya. Yana jinsa yana Fad'in"Awaran nan ta yi dadi a ina ka siya hala?
Yasan bazai tankasa ba shiyasa yace" ina Tunanin me yasa aka haife ka a zamfara ba'a shinkafi ba? Kafi dacewa da gayun kauyen nan abokina."
Da Sauri Sadiq ya juyo yana Fuskantar Tahir cikin mirmishi yace"Da Sauki tunda ba'a Daura za'a Haifeni ba."
Tahir ya fashe da Shegiyar Dariyarsa. Sai kuma me? Kawai sai ya shake ya fara Tari Sadiq ya yi kwafa kafin yace"Tahir Allah ya kara"
Tahir idanuwansa Jajir ya Dago yana Fadin"Ruwa Sadiq. Ruwa.."
Sai da yaga Tahir ya ji jiki sannan ya mike ya Dauko masa ruwa ya mika masa ya bude ya kwankwad'a kusan Rabi, sannan ya koma ya kwanta a kasan cafet din dakin yana maida Nunfashi cikin azaba. Shakewar yaji ba ta da kyau ko kadan Tahir har ya Fita Hayyacinsa
Yana jin Mirmishin Sadiq yana Fad'in"Nan gaba ka koyi ladabin cin abin Tahir."
A wahale Tahir ya ce"To ya Alarramma Abubakar Sadiq."
Sadiq yace"Ba gatse ba ne Sunana kenan"

*******

Yanzu kam ba abunda zance ma Allah sai godiya, Rayuwa ta yi mana kyau da inganci, Ciniki mu ke yi sosai na kan sana'o'in mu, musamman ma Danwake na Safen nan  shinkafa da wake ne cinikin sai a hankali.
Sai muka dawo da yin Danwake tare da Daffafen wake, Sai man kuli da manja duk wanda ka ke so a saka maka.
Matasa sun gane ma Danwaken da yan makaranta sosai a ke siya. Ayyukan sai suka maidani mai yawan Aiki ya kasance na kan jima ban Tuna Tarin kaddarorin Rayuwata ba. naa kan manta cewa Rayuwata ta na cikin Tsaka mai wuya ne.
Amma jikinta ya yi kyau bata kara ko Zazzabi ba, ni ne karfin duka ayyukan Habiba Saboda makaranta, Sai dai ta na taimakamin in tana gida sannan ita kan Shiga kasuwa in bukatar haka ta taso, duk da ina Fita ammh ba kasafai ba na tsame kaina da shiga Cikin mutane saboda Gudun gori da Habaici.
Ko acikin gidanmu ban tsira ba haka ko yan'uwan su suka zo a fito ana nuna ni ana mgana kasa kasa. To menene sabo a abunda suke Fad'a kaina duk abunda zasu fad'a an riga su Fad'an sa.
Yau ni kadai ke ta aikace aikace ne, Habiba bata nan tana gidan Adda Fati tun jiya. Ita ta kira tace Habiban ta zo bata jin dadi suna ta Fama da zazabi ita da yara.
Sau tari Mutanan gidanmu na yawan Fad'in ina ba su mamaki. a yanayin jikina kamar bazan yi kuzari ba ammh kuma ni macece mai zafin Nama ko aiki ne mai wuyan Ban fara ba, da na fara shikenan cikin Lokaci kad'an zan gama shi. Amma ta na yawan fad'amin cewa yanayina yanayin Adda Hari ce itama mace ce mai zafin Nama da komai cikin Hanzari da Kazar kazar.
Sai goma na Safe na gama Saka Danwake kuma ya kare duka bayan na gama ana ta aikowa na ce babu,Bayan na gama kankanta abubuwan da na bata na kawowa Daki na kawo na wankewa na wanke,Sannan na shiga daki na samu Amma na Sallar Walha.

Zama nayi gefen katifarta na Bude kwanon shan da ke cike da koko, ni da Dama mata da Safe, na saka karamin kofin da ta gama sha na zuba na koma gefe ina sha tas na shanye tunda ba tsami bazai min matsala ba.
Daidai Lokacin Amma ta Idar da addu'anta ta Dago tana kallona kafin tace"Ki kara mana in bai isheki ba"
Kai na girgiza mata kafin nace"ya isheni Amma kwarnafi na ke gudu. Don ma naji ba shi da Tsami ne na sha da yawa"
Amma ta jinjina kai kafin tace"To ai baki ci komai ba Hasiya?
Cikin Tabbatarwa nace"Na ci wake da mai da yaji Amma"
Amma ta kuramin ido kafin tace"Kin tabbatar? Kin san kina da lulura kuma ki rika wasa da cikin ki"
Dariya na yi kafin nace"Amma kada ki damu a koshe na ke"
Bata kara mgana ba ta fara jan Casbahan da ke hannunta ni kuma na isa ga jakar da nake tara kudin ciniki na Dauko na zube su a tsakar Dakin ina Kirgawa bakina har kunne na ce ma Amma Danwaken ana samu da shi Sosai.
Amma ta gyada kai kafin tace"Sai mu godema Allah"
Sai da na gama kirga kudin na ware na wanda za'a je kasuwa ina cewa"Amma garin Danwaken mu ya kare ga Habi bata nan"
Amma tace"Ki je da kanki mana. Tunda baki da tabbacin yau zata dawo kada ki jirata kuma gobe babu garin a hannu."
Da shawaran Amma na yi amfani sai da nayi wanka sannan na yi shirin Fita. Tunda Amma tace sai anjuma zatayi wanka ni na fara yi tunda fita zan yi, Hijabina na saka har kasa akwai Nikab na Habiba ne shi na ara na saka bana son a samu wata matsala ne.
Amma na gefe tana kallona har na Soke yar wata jaka mai igiya ta Habiba ce na ara saboda saka kudi nayi ma Amma sallama tayi min fatan Dawowa lafiya na fita.
A tsakar gida na ci karo da Maman Boy da maman salihi nasan sun yi da ni Saboda naga suna nunani da baki ban damu ba na fice ina Fad'in"Zan shiga kasuwa"
Da Sauri Maman Boy ta mike tana Fadin"Tsaya Hasiya. Daman ina son Citta da kunafari nawa sun kare"
Dole na Tsaya,Ammh Maman boy sai da tayi min taron mutane sako wajen na mata biyar suka hadamin ga shi kuci kuci hakanan na karb'a bani da Mafita.
Har na kai bakin Titi ba bu wanda yaa ganeni bakina alaikum na shiga kasuwa wajen masu had'a garin Danwake naje na fad'i iya adadin za'a hadamin sai na shiga cikin kasuwa na siyo wayan murhu da gawayi.
Sai na siyo wake da mangyad'a da Borkonu sai kayan maggi da kayam kamshi, sai sakon su maman Boy na jima a kasuwar sannan aka gama Had'amin komai tunda sai da na jira akayi nika. Aka had'amin komai cikin wani karamin Buhu mangyadan ne kawai na rike a hannu kada ya fashe.
A bakin Titin Tsamiya na Sauka Tunda bazai shigo dani ba. Na Dauki Buhuna a saman kaina mangyada kuma yana Hannuna Lokacin Rana tayi Biyu har ta wuce.
Ta layin da zai kai mutun har gidanmu na bi inda masu awara ke layi wajen su biyar suna ta siyan su har da masu Dankali da kosan manja.
Da zan wuce naga matasa a wajen tunda daman wajen zamansu ne. Naji muryan wani Saurayi yana Fad'in"Ke mai awara nan barayin ina ake saida Danwake mai Dad'i da Safe haka?
Na ji sanda wata yarinya tace"Nan dogon gida ana Danwake da Safe mai Dad'i Da wake in mutum na so, sannan mangyada ko manja sai wanda ka zab'a".
Na wuce acikin raina ina jin dadin ko bakomai akwai jin Dad'i a yabi sanar mutum, har na isa gida bakina yaki Rufuwa ina ko sauke kayan saman kaina na fara gayama Amma.
Tayi dariya kafin tace"Hasiya manya.."
Ina Dariya nace"Amma baki ji dadin da naji ba"
Ammh ta yi mirmishi. Sallah nace zan yi sannan na warware kayan na mikama su Maman boy sakon su har sun fara lekowa suna Fadin"Hasiya nace dai baki manta da Sako na ba ko? Tafarnuwa da ungurnu ne ni dai Sakona"
Har sai da nace musu Sai na yi Sallah zan  Fito da sakon su na basu, sannan suka shafamin lafiya.
Chapter 22 · 0% Book details