← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 69

Sashe 14

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban ji me Amma ta ce mata ba sai dai naji Muryan Adda Rukayya a harzuke tana fad'in"To shikenan Amma ni mafita daman na kawo ai shikenan" Ban tsaya jin sauran mganganun ba na tashi daga wajen zuwa wajen ma zubar ruwa na wanke shinkafa, acikin raina ina ta kokarin karfafa kaina, sanda ta fito ina zuba shinkafan ne cikin Tukunya. Tunda waken Dabam mu ke dafa shi,Haka ta wuce ni Fuu ko kallo ban isheta ba ni ce na bita da cewa "A sauka lafiya" Ina mirmishin takaici, matan gidanmu suka bita da kallo tunda duk suna waje ana hada hadan d'ora na dare, Masu d'orawan kenan irin su Maman Boy sai zaman gulma da yi da mutane tana fita suka fara kuskus ana kallona ana mgana, komai za su Fad'a bazan damu ba tunda sai bango ya Tsage kadangare ke samun wajen shiga. Sai da Ramatu ta leko ni Daga awo take tazo Dubani, a bakinta na ke jin Salisu an yi masa aikin an daure inda ya samu karayan Musbahu ya kirata ya ke Fad'amata kuma yadda ya ke Fad'a jikin Salisun da sauki tunda yana cin abinci sannan kuma yana mgana. A raina na yi Hamdala a fili kuma nace"Allah ya kara masa lafiya" Ramatu ta amsa da Ameen sai yammah ta tafi, Muna ta zencen haihuwanta tunda ta shiga wata na Tara, Har ina mata Fad'an ta daina Fita hakanan kada ta haihu a Hanya. Muka yi wasa da Dariya na Saba Rakata har bakin Titi ta samu adaidaita ko mashin, ammh yau ban fita ba saboda ina kauce ma idanuwan mutane a kaina. Itama sanin haka yasa ba ta damu ba Habiba na saka ta rakata har bakin Titi, tunda Ranar ba islamiyan yammah jumma'a ce. Ba mu da matsalan abinci Tunda muna ci cikin sana'ar mu, dagani sai Habiba Amma ce ta kan bukace koko ma wani lokacin amm ni in na ci Danwake na da Safe sai wani Daren kuma inna ci sauran Shinkafan da na kan rage mana ni da Habiba, Amma koko na kan Damata da Daddare ta sha, da Safe kuma wani Lokacin Add Fati na kawo mata kayan tea. Bata cika sha ba, in dai ba duka Zan had'a mana mu sha ba. Ranar asabar da Safe ina Hada had'ar kwabin Danwake sai ga kiran Adda Fati ta wayar Maman boy, sai da gabana ya fad'i da Maman boy ta kawomin sai dai Hankalina ya tashi da naji ta na Fad'amin Ramatu ce ta kirata taje asibiti tun jiya maranta ke ciwo to sun Riketa sun ce Haihuwa ne, tana asibitin Abu na Tudun wada naje na sameta. Ina jin haka na ruga Daki na Fad'a ma Amma cikin Sauri tace"Maza ki hanzarta ki je ki sameta. Allah Sarki Ramatu Allah ya raba lafiya" Cikin Saurin na Sauya kaya ko wanka ban tsaya yi ba, Habiba na bar ma kwabin Danwaken tunda ta iya cikin kudin Ciniki na Dauki 1k na mota na Zurma hijabina har kasa mai ruwan kasa,Fuskata Fuskata kozai kozai haka na fita Maman boy har ta gama yee kuwa da mganar sai fad'i suke yi Allah Sarki Ramatu Allah ya Raba lafiya. Sai ga shi har na kai bakin Titi ina ta Faman rufe fuskata da Hijabina, adaidaita na samu zuwa Pizzet, Dagachan na samu na Tudun wada,na sha wahala kafin na gano Ramatu. Haihuwa ce ammh sai zuwa Dare sukace sun dai riketa ne tunda Maran na Damunta nayi mata sannu ta amsani cikin yanayin ciwo. key din gidanta ta bani tace na je na kwaso kayan haihuwan da ta had'a acikin karamin akwatinta,vsai zannuwa da zan Dauko mata. Sai Fulas da Filo da kayan tea duk ta ce na Dauko. Sauri Sauri ko na sake hawa mashin naje na Dauko mata komai da komai na iske Fulas din cike da ruwan zafi Daukowa kawai nayi, kayan tea din kuma a kitchen dinta na gani na kwaso su duka. Tunda Nura kam ba abunda ya Rage Ramatu da shi. Sanda na dawo naguda gadan gadan,ina asibitin Inna talatu tazo bata jima ba tatafi, tunda kannen Nura da mahafiyarsa sun zo duk muna tare da su,bRamatu ta sha wahala sosai Nura baya nan sun tafi aiki Abuja Hankalinsa duk ya tashi yana ta kiran kannensa a waya domin jin ko ta haihu? ba ita ta samu bud'e ido ba sai Dare misalin goma. Ni Daman ban ma yi tunanin komawa gida ba,hankalina bai kwanta ba sai da Nurse ta fito tace Ramatu ta sauka an samu y'a mace sannan ni da kannen Nura muka saki Hamdala. Cikin lokaci kalilan Labarin Haihuwar Ramatu ta yi Tambari ni dai ba waya a hannuna ammah na san Inna talatu ta Kira Adda Fati, ita kuma zata sanar da Amma ko ta wayar Maman Boy ne. Ni nace ma Kannen Nura su tafi gida ni na kwana da Ramatu ,sai Daukan bby na ke yi farinciki ya cikani Yarinyar mai kyau da ita, gaskiya jarirai na da ban sha'awa Ramatu sai Faman dariya ta ke yimin, duk ta rame Lokaci d'aya lalle Haihuwa yakin mata. Ranar asibitin ya cika da Mutane Dangin Nura, shima adaran ranar ya Dawo, Bakinsa har kunne ni kuma ina masa tsiyar angon karni yana kwasar Dariya,komai da zamu bukata Nura ya siyama na. Sannan abinci daga gidansu Nura ake kawo mana Tunda suna Wajen Danmagaji ne. Ramatu tayi ta yi naje gida na yi wanka nace mata bazani ba sai ta kyaleni, Washegari sai ga su Inna talatu har da Adda Fati da Amma, bakina ya ki rufuwa ganin Har da Amma akazo. Zuwa chan kuma sai ga mutaan gidanmu Maman boy ce Jagoran su. Sun jima sai yammah suka tafi Amma ta zo min da kaya kala Biyu da Hijabi tunda tasan gidan Ramatu zan wuce,vkamar ko ta sani a daran aka sallame mu muka koma gidanta,Sai bayan suna zata koma wajen Inna talatu ta yi jegonta. Ramatu ba kawa ba ce a wajena yar'uwa ce shiyasa komai na yi mata ban Fad'i ba, kan jikina na ke Hidima da ita ko ruwan wankan ta Safe da yammah na Dauke ma Kannen Nura ni nake yi girki ne suke taikamin wani Lokacin, ammh har wankan Bby na iya sai dai Kanwar maman Nura ke zuwa da Safe ta yi mata wanka Ramatu kuma Amma ce yakamata ta zo ta yi mata to bata da lafiya sai aka Dauketa mata,wata abokiyar wasan Ramatu ke zuwa ta yi mata Safe da yammah. Ni kuma na ji da yan wanke wanken kayan Ramatu da baby, Nura kam ya shirya ma Ramatu sunanta daidai karfinsa, Shinkafa aka Dafa da wake Jalop,har da zobo Ramatu ashe ta yi mana Dankin wata Atamfa Cinghamvi, iri d'aya sai dai na yi hawaye,ita na saka na ci suna ba ni da Dan kunne da Sarka nata ta bani na akwatinta da ya rage guda d'aya bata yi amfani da shi ba. Na fito tsab da ni nima ina walwalina ni ce kuma kan komai na abincin, Adda Fati tun Safe tazo nan ta kwana ita da kanwar Inna Talatu Rahane daga Soba tazo. An yanka Raguna Guda Biyu Yarinya taci sunan mahaifiyar Nura, Khadija Ramatu tace zamu rika kiranta Noor haske. Washegari su Adda fati suka yi soye aka raba naman gida uku kashi Daya na dangin Nura D'aya kuma na Nura da Ramatu,D'ayan kuma na danginta, duka Ramatu tace kashi d'ayan a kai ma Inma talatu ta ba wa wad'anda suka kamata cikin na su ta Dibarmin nawa, sai da ta kwana Goma ta koma sabon gari gaban Inna talatu sai na rakata har chan sannan na wuce gida da sha tara na arziki daga Ramatu da mijinta. Atamfa ta bani tare da su manshafawa, kayan kwalliya takalmi Sabulan wanka da na wanki, Hijabai kala biyu sabbi,ta kuma had'amin da kayan abinci tace na kaima Amma tunda gida zata koma kuma daidai gwargwardo sun fi mu rufin asiri. Nura kuma Dubi biyar ya bani nayi ta godiya har ina kwallah da na koma na nuna Amma itama tace an kawo mata nama mai yawa da yajin jego har da Fallen zani da Omon wanki. Amma ta kalleni bayan ta gama Daga kayan da na zo da su Habiba ta Dauki Hoda da Jan baki tana fadin"Adda Hasiya ni dai ina son kayan kwalliyar kin ji don Allah" Ina mirmishi nace"Ke daman nace zan ba ma wa dauka Habi" Ta fara tsallen Murna muna yi mata Dariya ni da Amma. Dubi biyar d'in da Nura ya ba ni na mikama Amma ina fadin"Amma sai mu kara a jarin shinkafa ko? Amma ta ki karb'a Lokaci daya tana Fadin"A'a kudin ki ne, ki rike a hannun ki Hasiya" Ban samu zarafin mgana ba mukaji Ana maraba a tsakar gida, kamar Muryan Adda hari na rika ji sai da Habiba ta fita sai ga ta ta shigo da Buhu a hannunta bakinta har kunne tana Fadin"Adda ce da Badd'o' Amma ta washe baki tace"Harin ce da yamman ne? Maraba da Hari ta Jari" Hakan ta kan Fad'a daman Saboda chan Gada kowa da haka ya san su,in aka ga Amma ace mata Jarin Hari, in kuma aka ga Inna sai ace mata Harin jari. Adda Hari bakinta har kunne Saboda Murna ni kaina murna duk ta cikani Yarta autarta Badd'o kuwa haka ta nade jikin Amma ta na mata oyoyo da Gurbattacen Hausanta,Tunda su sun fi jin Fullanci hausan na su sai a hankali ko Amma da zama ne ya yi zama bakinta yaji Hausa, ammh duk da haka akwai fullanci a harshenta mu kam mukan ji iya sunayen abubuwa da baza'a rasa ba. Amma ta kasa zaune ta kasa tsaye,Sai da suka yi sallah suka natsa Ruwan zafi na dafa musu suka sha Tea da Buredi sannan aka zauna saman Hira bayan Inna Hari ta kwance Buhun tsarabanta,su Daddawa ne sai Fura da Nono da manshanu,sai garin kuni da yawa,Amma nata godiya ina tayata Habiba da Baddo na gefe suna ta shan Hira. Adda Hari bata sako mgamar aurena ba ko kad'an ba Duk da Amma ta kirata ta wayar Adda Fati ta fad'amata mutuwar aurena da Salisu. Daman tace tana tafe in ta samu dama sai da Safe ta yi
Chapter 14 · 0% Book details