Sashe 15
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ma Amma zencen Lokacin ina waje ina Hidimar danwake, Habiba da Baddo suna taimakamin da Zubawa suka yi mganganun su adaki da yar'uwanta sai da muka gama na koma Daki sannan Adda Hari ta kirani nazo gabanta na zauna Kaina ta Dafa kafin tace"Ki kwantar da Hankalin ki Hasiya. Babu wani farar kafar da kike da shi, sannan ke baki gaji Maita ba. Watarana sai labari haka Allah ya Tsara" na kalleta ina gyad'a mata kai Duk da tana cikin Rugga Adda tana da iliminta daidai gwargwardo. Sun cigaba da mgana da Amma duk a kaina ni ko ina chan gefe ina gyara kayana, ina ji Amma na fad'ama Adda Hari mganganun Adda Rukayya. Adda tayi Dariya kafin tace"Kyaleta Jari. duniya ce zata gayama Rukayya gaskiya. Mganar Hasiya kuma ni kin ki min ne Jari da Tuni ta na hannuna." Amma tace"sai dai ki dauke mu gabad'aya" Inna Hari na Dariya tace"Duk zan iya da ku kin sani. Tun yaushe na ke hakilon ki dawo wajena? Amma ta kad'a kai kafin tace"Saboda yaran nan ne Hari" Inna Hari tace"Yara suna ina? Fati na gidan mijinta Rukayya ma haka. Hasiya da Habiba ne kuma na ce dukkan ku zan iya rike ku jari zaman ki anan bai da wani amfani ga shi ba ki da ishashiyar Lafiya. Hasiya ce kuma kinga ga irin jarabawarta in zaki amince duka sai mu tattara mu koma da ikon Allah Hasiya zata yi auranta achan ta kuma zauna lafiya" Amma ta yi shuru ba ta yi mgana ba ni kuma saboda ba da ni ta ke mgana ba yasa ban saka musu baki ba. Ammh ni kaina zan so mu koma chan da Rayuwarmu kila Hankalin mu zai fi kwanciya. Adda Hari sati tayi mana sannan ta koma, kafin ta koma na rakata gidan Inna talatu ta yi ma Ramatu barka da yar Dubunta tace a siyama Noor kwalli, Sannan har gidan Adda Fati mun je itama tazo ita da mijinta sun gaisheta Adda Rukayya ce bata zo ba kuma bata kira waya ba, sannan ba wanda ya damu da ita. Cikin Dubi biyar din da Nura ya ba ni na cira 1k na bama Baddo, Adda Fati ko 8k ta kawo ma Amma tace a bama Adda Hari tayi na Mota sannan ta siyama Baddo kayan kwalliya da Hijabi. Adda Hari ta koma akan Amma tace in ta shirya zata kirata tace ita ba ta da matsala. Sauran Dubu hudu kuwa saka na ba ma Kultumen gidanmu tunda sana'arta ne, ta sakama Noor Huluna guda hud'u masu kyau, da ta gama naje da kaina na kaimata duk da sai da ta yi min Fad'an me yasa na kashe kud'ina? Na harareta ina fadin"Bansani ba" Dariya ta yi har kuma a ranta taji Dadi, shi alheri komai kankantar shi yana da dadi sosai. Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji, Har Ramatu ta gama jegon arba'in ta koma gidan ni naje na yi mata kwana biyu na tayata gyaran gidan,sai da Nura ya dawo sannan na koma gida Amma jiki ya yi kyau tunda in ba na nan ita ke Danwake,da yammah kuma ta yi shinkafa da wake, Mganar komawar mu wajen Adda Hari kuma ta sha ruwa tunda har Haya naji Amma ta yi ma Adda Fati mganar sake biyan na shekara. Wannan D'akin dubu Talatin muke biya duk shekara. Tunda naji haka sai na cire ma raina Sauyin muhalli na kuma san dalilin Amma na kada ace da gaske zargin da ke kaina Shiyasa muka bar gari, tana danne komai ne saboda ni. Adda Rukayya sai bayan Tafiyar Adda Hari tazo ita da ya'yanta kuma ma aranar sai da ta kara yi ma Amma mganar nan dai Amma ta kalleta ido cikin ido kafin tace"Ke Rukayya ki fita idona. Na ce ki fita idona na rufe ina ruwan ki da Hasiya ko akan ki take? Kina ci da ita ne ko kuwa akwai abunda kika Dauke mata ne da kika Kwazzabi kan ki sai ta bar miki garin nan ne? Sai Adda Rukayya ta Fara kame kame Ran Amma ya baci ta nuna mata kofar fita tana fadin"Daga yau sai yau in dai kin san mganar Hasiya zata kawo ki to na gode ki zauna gidan ki ba sai kin zo ba, da ke ko baki zamu cigaba da Rayuwa Rukayya shi ruwa cikin cokali ya isa mai Hankali wanka"