Sashe 12
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba. Abubakar ya fita cikin tashin Hankali ya baarni cikin Zullumi. Zullumin da har na yi wata uku gidan Abubakar ina cikin shi. Da D'aya da D'aya komai na Abubakar ya ke karewa Wuta ba'a san ta ina ta ke fitowa ba ita ke lashe komai. Bayan konewar shagunansa Mahaifinsa ya Farfado masa da Shago daya shima ko wata bai yi ba wuta ta lashe komai. Kuma duk inda wutar ta tashi tsinke ba'a Fitar da shi. Dangin sa suka taso min caa akan ni ce sillar duk abunda ke Faruwa. Tun Abubakar na Boye min Damuwarsa har ta kasa boyuwa ta bayyana. Abubakar ya yi shaguna sama da Biyar Gobara na lashe su na karshen ya tafi kano siyayya a hanya bata gari suka masa dukan kawo wuka suka karbe kudin suka watsar da shi a bakin Hanya. Sanadin da Abubakar ya rasa komai na shi. sannan shima Mahaifinsa ba shi da shi, tunda shi ya rika tallafama Abubakar jari. Shigowar Abubakar duniyata yasa na aminta da Mganar Ammi na ba mai yi sai Allah. Ammh daga Lokacin da abubuwan suka yi ta faru dani na aminta da cewa ni Hasiyar Bakar tsiya ce. Tabbas na zama Sanadin Lalacewar arzikin Abubakar na yi kuka kamar raina zai Fita auran mu na da wata uku Mahaifiyarsa ta zo har gida ta saka shi Gaba sai da ya Rubutamin Saki biyu. Yana kuka ina kuka. Har kuma gobe ban kullaci Abubakar ba na san shi din mai sona ne duk mganganun da gari ya dauka a kaina bai taba aminta ba in nace ni ce sanadin komai sai yace ba ni ba ce daga Allah ne shi ke da Jarabawa da Kaddara. Rabuwar aure na da Abubakar da abubuwan da suka biyo baya. Sai Tambarin sunana ya amsa kuwwa a gari, Hasiya na da Farar kafa Hasiya Bakar tsiya ce, Hasiya ba Alheri ba ce. Ban isa na hana Mutane fadin abunda suka gani a kaina ba. Na san har na gama Idda ina kukan Rabuwa da Abubakar. Mun rabu rabuwar da har yau ban kara ganinsa ba. Na dai ji labarin ya bar zariya ya koma kano wajen yayan babansa ya na tayashi kasuwanci. Gama iddata ba Dadewa aka yi auran Ramatu, sun koma sabon gidansu da Sati d'aya aka yi bikinta da Nura sai Kadaici ya yi min yawa. tunani da mganganun mutane duk ya isheni ba'a waje ba acikin gidanmu ma ana yadamin mgana. daga kuma Lokacin sai jikin Amma ya rika rikicewa ba'a wata bata ziyarci asibiti ba sai karfin Sana'ar da duk wata Dawainiya ya koma kaina. Kayan aurena kuma Wata Dilalliya da ke kusa damu aka baiwa ajiya tunda ba mu da wajen Ajiya. Har ga Allah na cire rai da kara wani auran na Dauka kowa yasan me ke faruwa da ni in wani namiji ya Rabe'ni ma manta Allah ke yin komai a lokacin da yaso. Ba zato ba tsammani sai ga Salisu ya shigo Rayuwata. Da ya yi sanadiyar wanke duk wani bakin Fentin da Auran Abubakar ya shafamin. Salisu shima ya kaunace ni. Ya so ni da dukkan Zuciyarsa. A auran Salisu ban saki jiki ba. Nasan abubuwa da dama za su iya Faruwa ammh ban tsammace su yadda suka faru d'in ba. Aure na da Salisu ya zama kamar ba'ayi ba. Cikin lokaci Allah ya raba wannan auran da shi da kanshi ya Kulla shi. Ina tunanin tunda Rayuwata ta na cikin Tsaka mai wuya mafi al'ala na cire mganar aure a raina na tsaya na kula da Amma tare da Habiba. Ammh tabbas na Fara Tunanin na Lallashi Amma mu koma Wajen Adda Hari in da ba kowa yasan ni Hasiya Bakar tsiya ba ce. Na cigaba da Bautar Ubangiji da kula da Amma, har ta Allah ta kasance dani.