← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 69

Sashe 61

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da gaske Sadiq ya ke yi da yace Hutu zai je gida ya yi. Saboda tunda ya zo ko kofar gida bai fita ba iyakarsa cikin Shashensa ko Shashen Innani ko Bakin get wajen Mallam Taju in za su yi karatu ko yan'uwansa da suka Damu da ya kai musu ziyara bai je gidan kowa ba.
Ko bangaren Umma daman bai cika zama ba saboda su Sultana in ya na son mgana da ita ne ya kan shiga. Shashen Mama kuwa sai dai in ya shiga su gaisa.
Daman bangaren Innani ne wajen zamansa kowa ya sani ba shi da in da yafi nan. Har acikin ransa ya na kaunar Tsohuwar nan duk ko da Tarin Rikice Rikcenta.
Sai ko Shashen Abba in wani lissafin kud'i ya had'a su. Ko wata mgana da ya shafi Dukiyar Abba tunda komai Sadiq na da masaniya a kan su.
Duka kaddarorin Abba da Filayensa tsabar kudad'ensa., Akwai ma wasu kaddarorin da Alhaji Sulaiman da Sunan Sadiq ya siye shi daga shi sai Sadiq sai Lauyansa Barrister Tafida suka sani.
Ko Pin dinsa na akwatunan bankinsa duka Shekarar da aka haifi Sadiq ne mabud'in su. Yau ma tun safe Barrister Tafidan ya zo suna Shashen Abba suna lissafin kudade da zakkar da za'a cire wannan Shekarar.
Abba na gefe komai da Sadiq a ke yi Tunda shine Dan boko.
Wani Alfahari ke mukurkusan Abba in yaga yadda Sadiq ke sauya yare ya na Turance Barristet sannan ga Lissafi a kansa da kuma iya Sarrafa Na'ura.
Haba duk wanda ke gidan SS SHINKAFI bai iya sarrafa Na'ura ba ai yaji kunya tunda kowa tasowa ya yi ya gansu agidan tunda kasuwancin Abba ne na tun Tale tale ne.

Lissfin ya Dauke su har Yamma tunda Sadiq yasa Abba ya ware wasu kudad'e saboda yan'uwansa da ke kauye tare da yan'uwan Umma da Mama.
Bangaran abincin gida daman na Shekara suke ajiye sai wata Shekaran kuma ta zagayo.
Sai bangaran sauya motocin gida Umma da Mama suna da Motocin su sannan yara ma na da shi ta zuwa makaranta Abba kuma baya sauya Mota sai Sadiq yace ya kamata a sauya su. Sadiq kuma har yanzu ba shi da ko keke yace ba yanzu ya ke Ra'ayin Mota ba tunda shi ba mazauni ba ne.
In fita zai yi ya fi bin Abba wajen harkokinsa ko ya Tukasa ko kuma Direba ya tukasa. In kuma zai shiga gari ne sai ya hau ta Umma wani lokacin d'ayar ta Abba ya ke hawa Benz dinsa baka da bai cika Fita da shi ba.
Sannan yasa an ware ma ma'aikata na su albashin sai Hidiman makaranta su Siyama. Daganan sai aka cire Riban Shekaran sai kuma zakkar da suka fita Daman Abba yasan wad'anda ake ba ma Zakkar mabukata ne da takalawa yan'uwansa daman Sadiaq na so kason Dabam ya ke cire musu Abba bai isa ya ce Uffan ba.
In magajin gida yace haka za'ayi Abba jiki na rawa zai ce ayi haka d'in magajin gida.
Sai ana gabda mangariba suka gama Barrister Tafida ya tafi shi kuma yace bari ya koma Shashensa ya yi wanka saboda zuwa masallaci.
Abba ma yace wankan shima zai yi yinin ranar duk anan suka yi shi abinci ma sai dai aka shigo musu da shi.

Sadiq shashensa ya koma ya yi wanka ya saka Jallabiya bata kai masa kasa ba sosai sai ya saka wando baki. Tare da Abba suka tafi masallaci ba su dawo ba sai da aka yi isha'i.
A masallacin ma ana ta neman taimako gyaran speeker masallaci Sadiq ya ce ma Abba za su ba da na su Taimakon.
Abba yace ya ba da nawa yaga ya kamata yace Dubu ashirin za su ba da, Sadiq yasa Abba ya yi mgana da Liman suka ba da acct lamba za'a Tura musu sai godiya su ke yi daman in dai Sadiq na gari yaji ana neman tainmkon masallaci sai in da karfinsa ya kare.
Suna dawowa kai Tsaye Shashen Innani suka nufa suka isketa ta na sallah sai da ta idar suka gaisa.
Ta kalli Sadiq ta na fad'in"Magajin gida duk yau ban gan ka ba tun Safiyar Allah da ka shigo mun gaisa in jin dai lafiya ko?
Kai Tsaye yace"Lafiya ta kalau aiki muka yi da Abba."
Sai ta washe baki ta na fad'in"Au ho to Allah ya yi albarka."
Abba ne ya zauna yana karanta ma Innani abunda suka cire na kudade.
Ta na jin ance an cire ma Mama da yan'uwanta ta tabe baki kafin tace"Daman kwadayyayu ne ba domin Allah Suwaiba ta auri Sulaimanu ba."
Sadiq ya yi dariya kafin yace"Ke da ki ka ce d'an ki ba mai kudi ba ne Rufin asirin Allah ne,.Kuma wata mgana ki ke yi haka Innani.?
Kai Tsaye tace"Uhm to karya nayi? Ya na da kudin ne ba domin Rufun Asirin Allah ba, kaima kasan komai akan Suwaiba da Danginta yi shurun ka Magajin gida."
Sadiq ya gyara zama ya na fad"in"Koma menene wannan ya wuce innani. Mama matar Abba ce sannan sun tara zuru'a atsakani ya kamata ki iya bakin ki, Suma jikokin ki ne kamar yadda mu ke jikokin ki. Ba kyau ki na nuna wariya Hakan ba Daidai ba ne."
Innani sai ta yi shuru taki mgana. Ya na kallonta yace"Baki ce min kin bari ba yar kakata mai kyau?
Innani ta washe baki kafin tace"Na bari magajin gida mganar ka ai itace akan gaba."
Mirmishi ya yi bai ce komai ba karamar wayarsa ya ke dubawa d'azu Tahir ya kirasa bai dauka ba ya bari sai ya natsu sai ya kirasa.
Shigowar Umma da Mama ya katse Mganar da Abba ke fad'ama Innani.
Kasa suka zauna suna gaishe da Innani ta amsa kai tsaye.
Sadiq ya juya ya gaida iyayen nasa su kuma suka yi ma Abba sannu da gida.
Batare da damuwa ba Sadiq yace"Umma yaushe zaki je Gummi?
An ware mu su na su zakkar. Ke ma Mama har da na wajen naki."
Mama ce ta fara fad'in"Angode Allah ya kara girma."
Umma kuma cewa ta yi"Tunda kana nan sai kaje ka kai musu daman Mallam sai mganar ya ke yi nace baka dawo ba."
Innani najin haka ta yi Zaraf tace"Ni ma zani na jima ban je mun gaisa da Mallam Zakari ba."
Sadiq ya kalli Innani cikin mamaki kafin yace"Ba inda zan je da ke. Kalle ki fa tafiya ma dakyar kike yi ammh da kin ji zencen yawo jikin ki na rawa."
Innani na jin haka kawai sai ta fara Sharan kwallah ta na fad'in"Ai Shikenan sai na hakura. daman na so na sada zumunci ne."
Abba na jin haka ya kalli Sadiq ya na Fad'in"Magajin gida ka tafi tare da ita tunda ta na son zuwa."
Sadiq ya kasa mgana shi fa ba zuwa da Innani ba Fad'i ba'a tambayeta ba.
Innani na jin Abba yace a tafi da ita ta washe baki ta na Fad'in"Bari na kira Sulsana ta had'amin kayana a jakata kwana nawa zamu yi ne magajin gida?
Baki ya Bude kafin yace"Ba kwana zan yi ba. Sai dai ke in zaki Tsaya ki kwana."
Ya fad'a kai Tsaye Innani tace"Kaji min Sharrin yaran zamani. Ina laifin mun kwana dangin duk su zo su ganka ayi zumumci."
Sadiq ya mike ya na fad'in"Innani ba zamu kwana ba shikenan."
Innani rai ba dadi tace"Shikenan..salamatu Allah na gani na so na sada zumumci Magajin gida yace a'a."
Ta fad'a ta na wani gyara zama gilashinta kamar ta Allah.
Chapter 61 · 0% Book details