Sashe 23
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*10/09/2023*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.
Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.
Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus
*07*
Shi Sadiq a kan Quantity Surveying ya samu shaidar Degree d'insa na farko.
Ma'ana sani kan harkan shimfid'a Titina da sauran su.
Shiyasa ya ke bautar kasar sa a Dismento Nigeria limited Old Sokoto Road, Samarun Zaria.
Shi kuma Tahir Politcal Sciences ya karanta wato harkan abunda ya shafi Siyasa. Ya na bautar kasar sa ne shima a wata goverment secondary na cikin Samarun zaria.
Yau litini tun bakwai da Rabi ya fita ya bar Tahir a gida ya na faman nuku nukun sa, Sai da ya biya in da ya fara siyan Danwake mai d'an karen Dad'i ya mika karamar kularsa da ya ke zuwa da ita ga yaran da ba'a rabasu da wasa a kofar gida suka shiga suka amso masa.
Dashi ya tafi wajen aikin nasa. ya riga ya saba tunda ya samu Danwaken nan da shi ya ke tafiya wajen yana karyawa har kuma wani Lokacin ya yi ragowa ya dawo da shi gida. Watarana kuma wani wanda suke aiki a wajen shima hidimar kasar ya ke yi suke ci tare.
Karfe biyu saura ya baro kamfanin kamar yadda ya saba adaidaita ya hayo zuwa anguwar Tsamiya aka sauke sa a bakin Titi ya gangaro da kafarsa.
Yasan Tahir na rigashi dawowa tunda makarantar sa ta fi kusa gida. Sannan ba tsayawa ya ke a tashi ba da ya gama Darasinsa ya ke gudowa gida Tahir dan Shiririta ne ba komai ya ke ba ma Muhimmanci ba shi dai wayarsa kamar tafi komai muhimmamci a rayuwarsa.
In kaga ciwon da Tahir bai Dauki waya a hannunsa ba to kila sai dai ciwon Ajali mutun ne mai mu'amala da kafafen yad'a zumunta sosai ba irin Sadiq da waya ko hawa irin kafafen nan ba su dame shi ba, Shi dai barsa da kallon Fina Finan korea da turkish Drama suna nan cike a Laptop dinsa ko Tab dinsa. Sai kuma sanin kan Na'ura mai kwakwala wannan tun yana karami ya iya sarrafata tunda ya taso ya gansu ne shima agidan su.
Dakin a bude Tahir ya barshi Saboda Sabon Iskanci har da su Dage Labule sama a dakin na Fuskantar waje, ga shi cikin Anguwa mai cike da Mutane sai wucewa ake yi ana ganin musu asirin dakin
Ba wannan ya fi bata ma Sadiq rai ba sai ganin yadda Tahir ya yi kaca kaca da Dakin Alhalin kafin fitarsa da Safe sai da ya kimtsa dakin shara ne kad'ai bai yi ba yace sai ya Dawo.
Tun kafin ya shigo ya gimtse fuskarsa Sanye ya ke da Riga da wando,Rigar mai Dogon hannu ce mai ruwan Ash da layi layin blue. Wando kuma jeans ne mai ruwan kasa sai Rufaffen baki takalmin da ke kafarsa bayansa Rataye da Jakar laptop d'insa sai karamar kular da ke hannunsa.
Yana shigowa ba domin sanin Darajan Sallama ba, da ba zai yi ba sai dai yasan Darajanta tunda shi Musulmi ne Murya ba Dad'i yace"Assalamu Alaikum.."
Bai ko jira Tahir dake kwance kan Katifa da ya yi wani da'i da'i ya amsashi ba cikin Fusata yace"Haba Tahir. Haba Tahir meye haka?
Ya fad'a yana kallon Tahir din cikin Takaici.
Tahir da ke kwance daga shi sai dogon wando ko Riga ba bu ajikinsa wayarsa na Hannunsa yana Dannawa ya yi matashi da d'aya hannun na shi Cikin kosawa da irin ka katsemin aikin gabana ya Dago yana kallon Sadiq kafin yace"Miye wai? Kai dai baka raina abun korafi wlh. Zafi ne ya isheni ga shi ba wuta shiyasa na bude kofar na kuma D'age labulen mu samu iskar Duniya ya shigo mana"
Daga haka ya koma ya cigaba da Dannan wayarsa yana ta faman mirmishi. Sadiq ya tsaya kawai ya na kallon Tahir bakinciki ya chuse ranshi. Kai tsaye ya sauke jakar hannunsa tare da kulan ya dago cikin Zaro ido yana nuna Dakin da kallo kafin yace"Au baka san me kayi ba ko Tahir.? Ba ka san ma me ka yi ba ko Tahir?
Tahir Hankalinsa na kan wayarsa yace"Me na yi kuma?
Da muryan ko ajikinsa.
Sai kawai Sadiq ya yi kwallo da Takalmin Tahir da ya cire nan tsakar dakin sai da ya Daki bango ya Dawo Tahir ya Dago yana kallonsa baki Bude kafin yace"Me ya yi zafi Alarammah?
A fusace Sadiq yace"Ban sani ba. na gaji da kazantar ka Tahir na gaji. Kai yaro ne? Komai sai an gayamaka zaka yi? Bakina kullum akan mgana d'aya ne ehe?
Ya karishe fad'a har jijiyon kansa na tashi alamun ranshi ya baci ganin haka yasa Tahir ya ijiye wayarsa nan saman gado ya mike yana fadin"Yi hakuri to. Kasan gajiyan da nayi yau? Daman fa ina da shirin na mike na kwashe na share dakin ne ka shigo"
Ya na fad'a lokaci d'aya ya duka yana kwashe kayansa da ya cire watsar da su anan.
Sadiq sai faman Hararansa ya ke yi kamar idanuwansa za su fad'o kafin yace"mgana d'aya ba zaka Dauka ba Tahir. Shikenan ka cigaba"
Daga haka ya karisa gaban Fridge ya Bude ya Dauko ruwa ya sha anan duka ya shanye ya fita waje ya jefar da Goran sannan ya dawo.
Tahir dai dole ya kwashe duka kayansa ya kimtsa wajen saboda yaga Ran Sadiq ya baci yasan Halinsa haka ya ke ba shi da Saurin fushi ammh kuma ya tsani ya rika maimaita mgana Daya.
Sai ga Tahir har da Shara, sai bayan ya gama ne ya yo alwala ya zo ya yi sallah Lokacin da ya idar Sadiq na kan katifa barayin da yake kwanciya tunda Kafitar tsakiya Dakin suka sakata kowa farko ya ke so ba Lungu ba, sai suka raba Gardama suka sanyata a Tsakiyan Dakin.
Ya na sallame sallan yaga Sadiq da ke danna laptop dinsa har ya sauya kaya zuwa saukkaku na zaman gida. Yanayin kallon kad'ai da ya gani ya sha jinin jikinsa da Sauri yace" kana wani kallo na kamar na yi sabo? Lalurin sallar azahar har sai la'asar ta gabato."
Sadiq kamar ba zai yi mgana ba sai kuma ya jinjina kai kafin yace" kai dai ka sani. Kai ba yaro ba ne in daidai ka aikata ma ai ka sani Tahir ba ruwan Sadiq aciki ni dai tsakani ga Allah na fita hakkin zaman tare"
Daga haka ya cigaba da kallon allon Laptop dinsa shi kuma Tahir ya mike yana Hamma kafin yace"Abokina yunwa na ke ji. Kuma miyar nan fa ta kare ita kenan jiya na yi mana shinkafa da Miya."
Banza da shi Sadiq ya yi ganin haka yasa ya nufi kular da ya shigo da shi ya jawota yana fad'in"Wai miye a kulan nan ne da ko da yaushe ka ke fita da ita kuma ka dawo da ita?
Sai dai me? Ya kasa mgana da ya ga Sauran abunda ke ciki Danwake da wake da Manja an chakud'a an ci an rage kad'an.
Da sauri Tahir ya kauda kansa kafin ya Dago yana kallon Sadiq cikin Jin haushi yace"Haba Sadiq. Tsakani ga Allah abunda ka ke yi yanzu ka kyauta kenan?
Ba tare da Sadiq ya kalleshi ba yace" me na ke yi?
Tahir yace"Gidadanci mana. Eh mana Gidandanci mana ban da haka miye ribarka na zuwa da Danwake wajen aikinka Tsakani ga Allah? maganar gaskiya wannan dabi'ar taka ta katon bagidajen Kauye ne"
Mirmishi Sadiq ya yi kafin yace"To miye bambamcin Tahir? Ai bagidajen kauyen ne ko baka sani ba?