Sashe 29
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tahir dai ya mike ya jawo kwandon gabansa Ferfesub kayan ciki ne, Sai Ruwan Zafi soyayyan kwai da buredi sai Ferfesun kaza yana Turiri.
Shi ya zuba ya ci har ya na Dankwale da Buredi bayan ya gama ya sha lemun kankana mai sanyi. Ya koma ya kwanta ya na Hamdala.
Tun yana kallo sama sama har barci ya kwashe shi wayarsa ba chaji ne sai ya sakata chaji cikin Bedroom din Sadiq.
Ba su suka tashi ba sai Azahar. Shima din Sadiq ne ya tashe shi sun makara sai jam'i suka yi a daki.
Suna cikin sallar a ka sake kawo musu wani kwandon abincin na safe ya Tadda na rana kenan.
Sadiq ne kadai ya ci Jallop din shinkafa Tahir ya ce sai anjuma.
Ashe suna barci ba su sani ba Innani ta saka Sultana ta yi ta kiran mata yan'uwan Sadiq ta na fadin kowacce tazo Magajin gida ya zo.
Ko da suka sauya kaya suka isa Shashen Innani cike da ya'ya da Jikoki daman sun kosa su gansa Innani ta Hana su zuwa Shashensa tace yana barci kada adamar mata jikanta.
Suna shigowa Dakin Innani ya Dau Sowan ga Bros.
Har da Abba da Umma da Mama yau Shashen Innani suke tunda daman in dai Sadiq na gida wajen zamansa Shashen Innani ne. In yaje shaahen Umma sai domin kebewa ta uwa da Abunda ta Haifa, shashen Mama kuma yana shiga su gaisa su yi hira da Kannensa Shashen Abba kuma yana shiga in mganata sirri ta had'a su ko yana son ayi wani abun.
Hajiya Surayya ce ta fara tasowa itace babba a dakin Hajiya Umma.
Cikin Annuri tace"Autan Umma ya zama Saurayi"
Tafada tana Dariya. sadiq sai mirmishi ya ke yi ya nufi yan'uwansa.
Surraya ce da Sadiya,Sajida,da Sa'adatu.
Subai'atu da Saddiqa ba'a garin Gusai suke aure ba.
Sai bangaran Dakin Umma Sa'ima Sakeena,Shahida na Umra Saliha ta raka mijinta Seminar a lagos.
Tsakiyarsu ya zauna suka yayyameshi suna sa kawai ke tashi.
Tahir kuma na gefe shima cikin Farinciki suka karbeshi suka gaisa a Mutumce da Tambayan mutanen gida.
Sai ya juya suka gaisa da Mama, Umma da Abba daman sun gaisa tun dazu, Innani ko na gefe sai Taunar ayarta take yi da ance Innani mu ji ayan sai ta fara masifa tana Fadin"Ba zan bada ba. Ba wacce ta siyo ta kawomin. Sai kakar Yaron nan Attahiru saboda haka ba Shegiyar da zata ci wlh"
Sadiq ya kalleta kafin yace"Innani ba na hanaki zage zagen nan ba"
Da Sauri Innani tace"yi hakuri Magajin gida raina ne ya baci. Haba duk abunda yaran nan suka ganni da shi sai sun yi kokarin rabani da shi.. nima D'an nawa ba arzikin garesa ba Rufin asiri ne kowace ta na da Miji taje mijinta ya siyamata mana"
Kai tsaye ya juya yana kallon yan'uwansa kafin yace"To kun ji. Kada wacce ta kara rokar Innani abunta. Kowacce ta na da miji ya siyamata itama d'an nata da ke siyamata ba shi da wani kudi sai Rufin asirin Allah"
Innani na Dariya da Hakoranta tace"Allah ya tsaremin kai Jikana."
Dariya aka saka gabadaya Falon na Diraman Innani an samu dai bata Fashe da kuka ba ko ta yi tsine tsinen da ta saba ba.
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.
*09*
Kowa kokarinsa ya faranta ma Sadiq rai, maganganu kawai ke tashi kowa kokarinsa ya fad'i bukatunsa Sadiq ya cika masa.
Ga Abba zaune ammh kowa ya tashi sai dai yace Yaya Sadiq ina son abu kaza. Ina son a chanzamin kaza don Allah.
Salima cikin Shagwaba ta ke fad'in"Bros wayata duk ta tsufa don Allah a sauya min wata."
Ta karishe fad'a cikin Shagwaba. Siyama ko gefen hannunsa na hagu ta makale kamar wata yarinya fuskar nan a tabe kamar zatayi kuka tace"Ya Sadiq mu ko wayar ba mu da shi. A siya mana ni da Sultana"
Dariya ya yi yana shafa kanta kafin yace"ba yanzu kuka ka gama Jsce ba? Ku bari in kun shiga SS1 sai a siya muku ko? Nakwa nakwa ta yi da Fuska ganin haka sai ya ja kumatunta yana Fadin"Haba Autan mu Smile mana. Za'a siya muku waya wannan cewar Magajin gida ne"
Jin haka yasa ta saki mirmishi ta juya tana kallon Sultana kafin tace"Sultana kin ji mu ma mun kusa zama manyan yara su Yaya Salima a daina mana wukalamci kan waya.".
Ta fad'a tana nuna ta da baki Salima ta zaburo ta na fad'in"Ni sa'arku ce da kike gasa da ni?
Yaya Sadiq ya kalleta kafin yace"Salima.."
Ta kallesa sai ya girgiza mata kai. Ta gefen idanuwansa Sultana ya ke kallo da har lokacin ko Tarinta bai ji ba.
Yarinyar nan ta na da aiki.
Innani na jin su bakam kawai tayi bata kara mgana ba.
Umma kuma da Mama suke taba Hira Abba kuma an kira wayarsa ya fita.
Tahir na gefe ya na duba wayarsa ammh kacokan hankalinsa na kan Sadiq da yan'uwansa da irin kauna da Gatan da suke nuna masa a ransa yana jin Dama ace Dama ace, Dama ace Shine Sadiq da Duniya ta jima da Shaida wannan gatan da ya ke da shi.
Big sis Hajiya Surayya ta kalli kaninsu kafin tace"Autan Umma sati na sama Muhsin zai dawo"
Kallonta ya yi yana nazarin waye kuma Muhsin ganin haka yasa tace"kanin mijina mana da na so ku tafi waje karatu tare."
Sai alokacin ya tuna da shi cikin Mirmishi yace"Oh Allah Sarki. Sai yanzu ya gama karatun na shi?
Hajiya Surayya tace"Eh ammh zai koma ya samu kwarewa kan bangaran da ya karanta. Da yanzu ka tafi da muna nan muna shirya maka kyakyawan Tarba Shalelenmu"
Kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya yi mirmishi kafin yace"Big sis. Sunaanshi Muhsin ni kuma sunana Abubakar Sadiq. Ba zai zama Dole Ra'ayina ya zama na shi Ra'ayin ba. Shima ba lalle nawa Ra'ayin ya zama iri d'aya da na shi ba. Shi kanin mijin ki ne ni kuma kanin ki ne akwai bambamci Tsakanina da shi."
Sa'ima ce ta yi karaf tace"To gaskiya in zaka yi masters dinka waje zaka fita ka zabi duk kasar da kake so kaji?
Sadiq ya kalleta kafin yace"Yaya Sa'ima.".
Da sauri tace"A'a mun gaji da ganinka kana gararanba a tsakanin Zariya da gusai kamar wani mara gata.".
Sadiya tace"Kuma Alhalin ina Tunanin kaf set din su ba wanda ya kai shi gatan ba".
Shahida ma ta saka bakinta gabadayansu suka yi masa caa da zencen zaman da ya ke yi a zariya.
Sajida tace"Ni abun haushin ma haya fa ya ke mganar ya kama a chan wani gida suna zaune. In da ya yarda ba sai Abba ya siya masa gida achan ya zauna ba."
Sakeena ta karbe da Fadin"Autan Umma mu dai ka dawo gida don Allah wlh muna kewarka ka bar garin nan sam ni Hankalina bai kwanta da zaman ka achan ba."
Hannayensa ya Hard'e a kirji yana kallonsu yana faman mirmishi. Salima ta karishe mganar da cewa"Big bros kawayen mu duka yayyensu a kasar waje su ke karatu ni in suka Tambayeni rasa ma me zan fad'a musu na ke yi"
Ta fad'a kamar zatayi kuka Dariya ya yi har Fararan Hakoransa na bayyana kafin yace"sai kice mu su a zariya ya yi karatu kuma yana chan yana Hidimar kasa."
Salima ta Zaro ido kafin tace"Bros..".
Kai ya gyada mata alamun eh hakane sai ta jime fuska ta yi mgana su Sakina suka saka Dariya.
Tahir na gefe ya tsoma baki karo na Farko kafin yace"Sai ma kunga ire iren abincin da ya ke ciki.."
Tahir bai tsaya ba ya shiga ba su labarin irin cimar Sadiq ke yi a zariya harda Danwaken da ya ke siya yana Tafiya da shi wajen aiki.
Gabadayansu suka Bude baki suna kallon Sadiq shi kuma ko ajikinsa.
Tahir yace"Abun haushin ma masu saida abubuwan ba su da Tsafta wani abun ma baisan da ga ina aka Sarrafashi ya siya yana ci ba. Ko ni ba na irin Rayuwar da Sadiq ya ke yi kamar wanda ya fito daga Daji."
Sadiq ya kallesa kafin yaace"Daman daga ina na fito.?
Surayya ta kalli Sadiq kafin tace"Why Autan Umma?
Nan fa suka taso masa suna ta mganan gaskiya gwara ya dawo gida ya yi Bautar kasarsa. Su ka gama mganganunsu bai tankan su ba sai daga karshe Umma ta shigar masa ta na Fadin"Ku kyalemin Auta ya yi irin Rayuwar da ya ke so haba. ai ba kauce ma Hanya ya yi ba Ra'ayi ne kowa da irin na shi"