Sashe 41
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai bayan azahar su Adda Fati suka iso lokacin har an kawo abinci daga Gidan su Baban Amna cikin gari. Ba su da nisa da Babban gidanmu na marigayi Mammadi kona. Sun san mu kamar yadda mu ma muka san su. Abincin ma kula Hud'u ne suka Dauki Biyu suka ba ma Adda guda Biyu. Ni na zuzzuba mana muka ci muka sha Ruwa da lemu tunda Walima ce aka yi. Amna da Aslam na ta tsallen Murna sun yi sabon gidan. Yaran sun fi sabawa da Dangin Ubansu shiyasa ma suna tare da su. Ni dai tunda na Fahimci yadda na zama mujiya da abun nunawa sai na kama kaina acikin Dakin Adda ko Fitowa ban karayi ba tunda muka gama gyaran kitchen. Su Maman Salihi sai zaga gidan suke yi suna santi bayan sun gama ci sun sha abun mamaki har Kaltume da nasan gulmar da ta kawo ta ta fi wacce ta kawo su maman Salihi. Sai Gabda La'asar Baban Amna ya kira yace ga masu kawo kujeru nan da wasu kayanbA gyara waje jin haka yasa muka mike muka kara gyara Falon da Sauran Dakunan. Kawo kayan yasa Danginsa suka shisshigo mazan su suka rika shigowa da kujeru ne sai katifi da cafet sai tv bango guda Biyu da sauran tarkace. Sai Falon ya yamutse kowa na fad'in yadda Setin kujerun suka yi kyau da cika ido. Adda Rukayya sai faman washe baki take yi tana fadin"bangare na za'a fara gyarawa, na shi yace sai daga baya" Shagala da ganin abun arziki yasa na fito nima na Tsaya cikin mutane ana santin ganin kayan da ni. Noor ta tashi ta na Hannun Habiba. alokacin ba ni da Hijabi Domin Tunda na cire ban maida ba, sallah ban yi ba Tunda ina Hutu. Kamar Daga sama naji an kira sunana da Karfi "Hasiya.." Sai na juyo sai da Gabana ya fad'i ganin Jummai kanwar Abubakar ce itace Autar su. Kallonta na ke yi ina kokarin daidaita yanayina jin ban amsa ba yasa da ta shiga Tafa Hannu ta na Fad'in"Na shiga uku na lalace wa na ke gani haka kamar Hasiya Jaraba da Masifa da bala'i.? Jin mganarta yasa sai Hayaniyar ta Tsaya kallo da Hankali ya Dawo kanta. Ita ko kai tsaye ta shiga nuna ni ta na kuma kallon kanwar Baban Amna Tunda ta dalilimlnta tazo gidan. Ita jummai tana auran kanin mijin Kanwar Baban Amna ne su d'in Facalolin juna ne. Cikin mamaki tace"Me ye had'in ku da wannan Jarabar? Ta fad'a ta na nuni Kamwar Baban Amna mai suna Zainab tace"Wannan wai? Kanwar Ya Rukayya ce matar Yaya Adamu." Ai sai jummai ta Rafka salati tana Fadin"Me ya kai ku jawota nan wajen? To Allah ya kyauta mu gama taron nan lafiya wani bala'in bai afka ma dan'uwan ku ko wannan gidan ba." Duk na Tsure na kasa ko kwakwaran motsi kamar yadda su Ramatu suka yi. Da yake Abubakar suna da Tarin zuru'a a gidansu nima ba duka na san su ba su Adda Rukayya ba su san Jummai ba sun fi sanin manyan. Ramatu ce ta kalleni ta na Fad'in"Wacece wannan Hasiya? Dakyar na Hadiye miyan baki na kafin nace"Jummai ce k'anwar Abubakar.". Ramatu ta zaro ido Adda Fati na gefe tace"Subhanallah Allah yasa kada ta watse taron nan" Ai bata gama Rufe baki ba Zainab kanwar Baban Amna tace"Mun santa sarai Jummai ni kaina da na ganta tazo sai da nayi mgana to ammh gudun ka yi mgana ace ka tada Fitina yasa ban ce komai ba." Jummai ta ce"Kin ko yi kuskure. Wannan matar ba Mutum ba ce ina zargin Mayya ce." Su Adda suka saka Salati Inna Talatu ta shiga Tsakiya ta na Fad'in"Ashas. Wani irin maita kuma baiwar Allah? Kai Tsaye Jumma tace"in ba maita ba menene? In ta kama kurwan mutum sai ta Allah kawai. yaya Abubakar sai da zaman zariya ta gagareshi ya koma kano komai ya taba da sunan sana'a sai ya lalace ta gama lalata masa Rayuwarsa gabad'aya muma ta lalata mana Rayuwar mu tunda ta dalilinta Ubannu shima ya rasa komai na shi in ba Maita ba mene wannan? Ki sake mana kurwan d'an uwa don girman Allah Hasiya." Tun kafin ta gama mgana na Fara Hawaye cikin murya ta nace"Wlh ni ba na maita. Dangin mu kuma ba Mayu." Da sauri Zainab kanwar Baban Amna tace"Kina fa da Maita Hasiya. in ba maita ba menene? Ina ce a auran ki na Biyu ma abuunda ya faru kenan? An ce shima sai da aka rasa Dukiya sannan shima har tana neman ransa Tunda yana chan yana jinya da karaya uku ajikinsa ko'ina kika shiga Bala'i ne da Masifa zai faru to in ba Maita ba ne, sai ki fad'ama na uban me kike da shi..? Kalmar maitan da suke jefana da shi yasa na Fashe da kuka. Ramatu ta rikeni ta na Fadin"Wani irin maita kuma? Hasiya ba mayya ba ce in da mayyace da Tuni kun sani ai kunsan tushenta asali ma kusa kuke da su" Nan fa mganganu ya rika tashi kannen Abubakar suna ta cewa a bakin ya'yan Baba Saminu suke jin Labarin su ma sun ce maitan gareni. Adda Fati tace"Mu ba mu da Maita. Ba mu yi gadon shi ba. Da muna da shi da kunga Rukayya da shi." Kai Tsaye Zainab tace"Ai an ce ana siya kuka sani ko itama siyan tayi." Adda Rukayya da ta kasa mgana Tun dazu sai yanzu ta dakama Zainab Tsawa kafin tace"Ya isheki Zainab. Kina wuce gona da iri ya kuma isheki jifar yar'uwata da kalmar Maita." Zainab ta Saki gud'a kafin tace"Ku na kokarin Boye abunda bazai Boyu ba Yaya Rukayya. To in ba maita ba ce ku fad'a mana ko menene muna son ji." Adda Rukayyah sai ta kasa mgana Ramatu ce tace"kaddaran Allah ce. Hasiya ba Allah ba ce ba ta da masanin gaibu. Kuma wannan mganar da kuke yi kamar kuna Jayayya da Kaddaran Allah kuma Daidai ya ke da Baku yarda da Allah ba." Maganganun Ramatu yasa suka yi Shuru Jummai ta tab'e baki kafin tace"Wlh kada ku yarda da mganar su. Gwara ta tafi tun kafin mugun abunda ta tsara ya saukar mana." Jin maganganunta yasa kannensa suka fara cecekucen sai na bar gidan kada na jawo musu wata asarar. Kuka na ke yi da Bakina da zuciyata. Adda Rukayya ta ba ni mamaki yadda ta shiga ta na masifan sun zo sun tozarta ta tunda suka Tozartani. Tabbas jini jini ne, Dan'uwanka zai iya maka abu ammh shi bazai iya Daukan wani ya yi maka ba. Mgana taki karewa suna ta Tafka bala'i kan sai na bar gidan har suna Hakilon za su fita da ni ita kuma Adda Rukayya tace ba zan tafi ba ba su isa ba. Ganin abun na neman ya yi yawa yasa nace ma Adda Rukayya bari na tafi kawai. Idanuwanta jajir tace"Ba fa zaki tafi ba. Ko da suke tunanin nan gidan Dan'uwansu ne. Ni ma su yi Tunanin Ni matarsa ce ina da iko da komai na shi." Inna Talatu ta ga Hayaniyar ta yi yawa ga maza masu kawo kaya yasa ta ce ma Adda ta bari na tafi kawai ta kalli Ramatu ta na fad'in"Ramatu ku je gidan ki da ita." Ramatu ta gyad'a mata kai sai ta Rikemin hannu na koma Dakin Adda ina sharan kwallah na saka Hijabina Da takalmina Habiba sai kuka ta ke yi ta na fad'in"Adda Hasiya ki yi hakuri." Ban iya mata mgana ba. Ramatu ta karbi Noor ta goya muka fito ammh duk da Haka Rigimar bata kare ba. Kamar wasa zamu fita muka bangaji juna da bakin da suka shigo ni ban san yadda abun ya faru ba sai gani na yi d'aya daga cikin su ta fad'i a kasa tana ta faman birgima da ihu. Suna ganin haka wata mata ta kwalla kara ta na fad'in"Ku riketa ta tabatta mayyace ta kama Ladidi" Ta fad'a cikin karaji ni dai na juya ina son sanin meke faruwa ba zato ba tsammani naji an cakume an yo baya dani ana fad'in bazan tafi ba sai na Tsallaka matar dake kwance tana Fizga kamar mai aljanu. Ramatu na ja na ta na fad'in"Hasiya ba mayya ba ce don Allah ku bari mana.". Ta na yi su Adda na yi Inna Talatu fad'i take"Shed'an ya shigo gidan nan don Allah ku bari mana." Ba wanda ya Saurare su rikeni yan'uwan Baban Amna suka yi suna Rantsuwan sai na Tsallaka matar da ke kwance sannan zasu kyaleni. Na rude na Dimauce domin ban tab'a ganin wannan tashin Hankalin ba. Ganin su Adda Fati suma sun taso sun Tare ni yasa Zainab tace ma mazan da suka kawo kaya su Rufe kofa su zo su kama mu su ni. Innalillahi wa'inna alaihirraju'un Ban taba zaton haka Rayuwa ta ke cikin Tsaka mai wuya ba sai ranar. An ce sarki yawa ya fi sarkin karfi. Sun fi mu yawa su Adda baza su iya da su ba sannan ga Maza. Haka wani Namiji ya rikeni daman ni ba auki ba, Matan kuma suma kaimun duka ta ko'ina Hijabin jikina haka aka yagashi a ka yar, A na jamin Rigan jikina Dankwalina ko Tuni ya yi ta kan shi Gashina ya bazu haka suke jamin ga shi suna Tunkud'a ni su Ramatu na Faman tareni ammh sun fi karfin su. Bana so na tsallakata Saboda ni ba Mayya bace, gida ya cika da iface iface da Hayaniya wasu suka fita waje suka rika Ihun an kama mayya kafin kace me gida ya cika da Mata da maza. Sai da suka min duka suka yayyagamin kayana dagani sai siket sai Bra a gaban Mutane mata da Maza Ramatu ta rufanin Hijabinta suka Cire suka watsar Adda Rukayya na ta Ihu sai kiran Wayar Baban su Amna take yi baya Dauka. Su kuma sun yi Rantsuwan Wlh tallahi sai na Tsallakata ko su halakani,Tozarcin da ban taba ganin irin shi ba. Tsirara suka kusa yi min dagani sai siket. Haka na ke wani irin kuka zuciyata na zafi kamar zan Mutu Adda Fati kuka Adda Rukayya ma. Habiba ma kuka Ramatu kuka, duk wani mai imani da idon shi bai Rufe ba sai da ya