← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 69

Sashe 32

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bai damu da ita ba kai tsaye ya kalli Abba kafin yace"Gaskiyan mgana Abba kudin da ka bashi ya yi kad'an kada ka manta ba shi da hali nomar ma da suke yi kai ka ke tallafa musu shima na iya ci da iyali ne. Y'a fa ya aurar Abba ta ina dubu talatin zatayi masa? Ya kirani yana gayamin yacci bashi Saboda haka zamu biya masa duka ba shin da ya ci Abba."
Abba sai ya kasa mgana ya na ta zaran ido,Innani ta yi galala galala kafin tace"Yau na ji tsiya da wasila ta ina zai fara biyan bashin da bashi ya ci ba? Sulaimanu fa ba bawan su ba ne ai ya na da ya'ya su biya masa ba shin mana."
Ran Sadiq ya baci yace"Innani kada ki kara  sakamin baki in ina mgana da Abba na."
Innani ta saki baki ammh kuma ta kasa mgana jin muryansa cikn kaushi yana Fad'in"Sai Baba Hassu ta kirani kan yaronta ya samu makarantar nan ta police acadamy wudil tana neman a tallafa masa Abba. Shima zamu taimaka mata."
Abba ya kasa mgana har yanzu Sadiq ya cigaba da fadin"Sannan Baba Husau ma ta kirani yarta zata yi jarabawan fita ba kudi tana son don Allah a tallafa mata.!"
Ganin Abba ya kasa mgana yasa ya ce"Abba dukkansu zamu taimaka musu.".
Da sauri Abba yace"Eh.. Eh zamu taimaka musu za'a taimaka musu."
Innani na jin haka ta fashe da kuka tana Fad'in"shikenan zasu talautamin Dukiyan yaro. Kai su Sammani dai ba su ji dadi ba Allah dai ya tsine musu albarka dukkansu. Tunda ba su da Godiyar Allah.".

Sadiq a fusace ya kalli Innani ya na fadin"Allah bazai taba tsine musu ba sai dai ke ce in baki gyara halin ki tun a duniya ba wlh ki ka je lahira tsinuwan Allah sai ta kamaki."
Sai Innani ta razana ta Dafe kirji tana Fadin"Na shiga uku ni Dije? Anya magajin gida ne wannan? ni ko me nayi da Allah zai la'ance ni"
Kai Tsaye yace"Kina hana alheri. Kin ba da taimakon wajen maida Abba haka. kinsan yana da halin taimakawa ammh sai ki rika hanashi meyasa haka Innani? Ka yi alheri a duniya ka tsince shi a lahira yau in Abba ya Mutu ni da ke da su Umma ko dukiyar da kike kareta bamu isa mu hana shi karban hukuncin Allah kan yadda ya tafiyar da Dukiyarsa ba. In za'a fitar da zakka ki rika masifan danki ba shi da kudun Rufin asirin Allah ne, in zai yi kyauta ki hanashi kice ba shi da shi haba Innani ki sani fa wannan abubuwan da na ke saka shi yana aikatawa Sune Zasu bibiyeshi acikin kabarinsa Ranar da ya Mutu. Ki sani wannan aikin Alherin shi zai zama gatanmu bayan ba bu Abba. Ki sani Akwai mutuwa zaki mutu, Abba zai Mutu Umma ma zata mutu mama ma haka nima zan mutu watarana duka bamu a wannan duniyan to gwara mu aikata alherin da zamu je kabari muna jin daman mun ninka aikin alherin da muka yi a duniya Saboda yadda Ni'imar Allah zata rika ziyartamu acikin kaburburan mu ki Sani wlh tallahi duk abunda ka aika na Alheri zaka girbeshi in na Sharri ne ma hakan. To ki gyara kada ki mutu cikin wannan Halin Tsinuwar da kike kira ma Mutane ta Sauka akan ki"

Ya karishe fad'a fusace Lokaci daya ya na mike ya kama hanyar barin Falon yana fadin"Zan kira su Abba. In na ji adadin kudad'en da za'a taimaka musu zan gayamaka."
A yadda ya ke mgana suka Fahimci ran Maza ya baci.

Jikinsu Abba duk ya yi sanyi sun kasa mgana Umma ta kalli Abba ta kalli Innani da ke sharan kwallah tana Fadib"Sulaimanu ka yi aikin Allah kaji ko ? Ka yi ta alheri da taimako ko na mutu, ba cikin tsinuwan Allah ba  duk wannan shekaran ka kai su Samnani Hajji kai duk ma su dawo nan gidan da zama wlh bazan kara mgana ba."
Umma da Mama suka kalli juna suna Mirmishi Abba ne ya koma ya na ta lallashin Innani.. daman Umma tasan mai gayya mai aiki in yazo to kamar zanen kaddara ne komai da yace a yadda ya ke so haka zai faru.
Duk yadda ka ke nakasun ta wani bangaren to Allah na haskaka ta wani Bangaran
Washegari fuskar cunkushe ya tashi sallama ma tsakaninsa da Innani sama sama ne, Sai faman ba shi hakuri ta ke yi tana fadin"Ai nace dukkasubsu dawo nan da zama an zama daya. To menene ma Duniyan nan Allah na Tuba magajin gida? Sulaimanu fa da ka ke gani ya na da arzikin nan duk su zo mu ci arzikin tare"

Kamar zai yi dariya sai dai ya fasa ta bashi kuli mai siga da yawa da ta samo a Shinkafi da gyad'a soyayya daman shi ta ijiyemawa ya karb'a yana Fadin"Nagode innani Insha Allahu zaki mutu cikin salama kuma ba bu tsinuwar Allah a kan ki."
Innani najin haka ta washe baki tana Fadin"Yauwa har naji Hankalina ya kwanta. To nace ba ka samu kun kebe da Sulsana ba? Kaga ina so nan da Bad'i Sulaimanu ya aurar da ku.".
Kai tsaye yace"Innani.."
Ta amsa ya cigaba da fadin"Innani ba Ruwan ki da aurena da Sultana. Ko da kuka zabamin ita Ra'ayina ya sa na karbeta saboda haka yaushe zamu yi aure wannan na Ubangiji ne ki daina katsaladan a Sha'anin Allah kada ki Mutu kasa taki karban ki.".
Hankalin Innani ya tashi ta rika Fadin"N shige su alqur'an na  bari. Wlh magajin gida bazan kara shiga ba."
Ya na mirmishi ya Rumgumeta yasan ya gama Firgitata Innani na Tsoron azaban Allah.
Direban Abba ya kaisa har zariya Tunda ya na da kaya. Har da lemuka duk daga gida Umma ta saka ya Dauko.
Ko da ya koma Daki duk ya yi kura. Da yake daga shi har Tahir suna da key a hannunsa.
Bayan ya gama shiga da kayan ya zage ya gyara daki tas ya tsaftaceshi. sannan ya yi wanka ya sauya kaya. Bai fita ko'ina ba yaci Nama ya kora da Ruwa ya koma ya kwanta yana barcin gajiya.

*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*

*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V

*10*

Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi haifaffan garin Shinkafi ne da ke Jahar Zamfara.
Asalin sunan Innani Dije ne kuma ta yi aure aure kamar uku kafin ta auri Abubakar mahaifin Sulaimanu, Innani Tun tana matashiyarta irin matan nan ne masifaffu tijararru an yi mata irin auran gida tun da fari ta rika guje guje auren ya lalace bai je ko'ina ba.
Iyayen Innani masu kudi ne, ko a baya Tunda suna Noma sannan suna da Tarin Dabobbi.
Innani itace Matar Abubakar ta biyu ko da akayi auran su taje ta iske shi da uwargidansa kuma uwar ya'yansa Barira. Wacce ta yi ta hauka sanda za'a auro mata Innani tunda a lokacin Mallam Abubakar ya nuna matukar kaunar Innani a Zahiri kuma ya ke nunawa da ya sanya tsananin kishinta a zuciyar Barira.
sannan sanda zata zo iyayenta sun yi mata kayan gata na alfarma tunda ita kadai suka haifa ga shi kuma sun kwana biyu a duniya. Shiyasa dukkan gata suka tattara suka ba ma Innani komai ta ke so ta na samu har da ma wanda ba ta so duka iyayenta na cika mata shi.
Shigowarta gidan Abubakar ya sauya komai saboda ta na son shi tunda ya na lallabata ya na kuma ji da ita. Sannan kuma ya na ji da Masifarta kuma ya na yi mata abubuwan da ta ke so. Sai sanadin haka ya kara hura wutar kiyayya da Tsakanin kishi a gidan Abubakar, komai Barira ta ga Innani da shi sai tace mijinsu ne ya siya musu sannan ta na zargin shi da Nuna bambamci a tsskaninsu.
Har kuma ta jawo ya'yanta cikin kishin ba su dauki Innani a matsayin uwa ba, sai itama kuma ta ce kowa ya yi ta kansa.
Haihuwanta ta farko Namiji ta Haifa aka samu Sulaimanu, bayan shi ta jima bata haihuwa ba,Sai daga baya ta samu mace mai suna Hauwa Kulu. Kuma har alokacin Barira da ya'yanta ba saa raba'ar Innani da ya'yanta duk ko yadda Abubakar ya so ya had'a kan zuru'arsa bai samu ba har ya bar gidan Duniya.
Ya tafi ya bar Barira da ya'ya Biyar,Sammani ne babba Gaddafi ,Sai Hassu sai Husai sai karamar su Zuwaira.
Chapter 32 · 0% Book details