← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 69

Sashe 58

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Galala Tahir ya yi ya na kallon Sadiq ganin ya na dariya kamar wanda ya fad'i wani abun dariya.
Tahir ya shaka da yasa a fusace yace"Sadiq abun dariya ne wannan?
nace abun dariya ne wannan?
Sadiq ya tsagaita da Dariyan ya na Fad'in"Gaskiya abun dariya ne Tahir. Ta ya ya zaka yadda da wannan mganganun kamar almara?
Daman mutum ya isa ya yi ma wani mutum wani abu batare da Allah ne ya yi masa ba?
Ya tambayi Tahir Lokaci d'aya ya na kallonsa. Tahir yace"Ba wannan bane, Ka fara tunanin janye jikin ka daga wannan yarinyar Sadiq in dai ba sonta ka ke yi ba."
Sadiq yace"Wlh tallahi ba sonta na ke yi ba. Mganar kuma na janye jikina bai taso ba ban fara domin na daina ba Tahir."
Tahir yace"Sadiq ka na jin fa an ce ga abunda ke faruwa a rayuwar yarinyar nan. Daman ni tunda naganta ba ta min ba tsoron ganin Fuskarta ma na ke yi farin ta ya yi yawan da zai iya zama matsala."
Sadiq ya kara Bushewa da dariya kafin yace"ina ruwan ka da farinta. Fari ko baki wani hallita ne na ubangaji. Kada ka danganta haka da yanayin da Allah ya halliceta."
Tahir yace"Sauran mazajen da ta aura fa? Me zaka ce a hakan haka.?
Sadiq ya gyara zama kafin yace"Ni ban zan ce komai ba. Saboda ni musulmi ne na yi imani da Allah da Annabawansa tare da Sahabansa da Littafansa. Sannan na yi imani da Tauhidi da iklasi  na kuma san akwai kyakyawan kaddara da Mummuna shiyasa bazan ce komai kan mganganunka ba Tahir,  Basu da ma Tushe ballatana makama kai ma ban yi tsammanin jin irin wad'anan maganganun daga bakin ba Tahir."

Ya na gama fad'in haka ya karb'e laptop dinsa ya na fad'in"Ni ga Allah na Dogara nasan kuma shi ke aikata mai kyau ga bawa da akasin sa ba Mutum ba."
Tahir ya saki baki kawai ya na kallon Sadiq bai taba zaton zai iya Ture wannan mganar ba.
Sai yanzu da ya maida abun wasa yasan raba Sadiq da wannan yarinyar nan aiki ja ne.
Tahir bai hakura ba yace"Sadiq ba Rayuwarku d'aya ba. Ku na da tarin bambamce bambance don Allah ka bar su ana su Duniya kai ma ka koma taka Duniyan."
Sadiq ya amsa shi cikin Sakewa ya na Fad'in"musulmi dan'uwan musulmi ne Tahir. Kuma taimako ai ba laifi ba ne ni ban ga wata matsala ba aciki."
Cikin kumfar baki Tahir yace"To aure auren nata ka san da shi?
Ka daa garin Taurin kanka ka siya ma kanka wahala Sadiq."
Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Abunda ya shafe su sai nace sai na sani? Nima ai ba su san komai a kaina ba, Kaga Tahir plz ka kyaleni da wannan mganar bata da asali ballatana Tushe."
Sadiq ya fad'a ya na cigaba da Sarrafa Laptop dinsa Wani Turkish Drama ya ke kallo shi ya ke kokarin kunnawa, sanda Yaji Tahir na fad'in"Ammh kasan akwai farar kafa acikin mutane ko?
Kamar Sadiq bazai yi mgana sai kuma ya Ture Na'urar gabansa ya na kallon Tahir na wani Lokaci kafin yace"babu Farar kafa a cikin Mutane Tahir. Kuma babu Farar kafa a musulumci Duk canfi ne kuma Canfi karya ne addini baizo mana da shi ba kai ko Maita ma Annabi bai sanar damu ba kambun baka kad'ai Annabi ya sanar damu akwai shi a acikin musulunci."
Ya fad'a cikin Tarin natsuwarsa. Tahir ya yi kasake ya kasa mgana.
Sadiq ya cigaba da fad'in" Babu wanda yasan gaibu sai Allah Tahir.
Allah Fa'alim lima yarud_ shine mai aikata abunda ya ke so alokacin da ya so. babu Canfi ko farar kafa a musulumci, lamyasiduna_ Babu abunda zai same mu a wannan rayuwar Illama katabullahi lana_ sai Abunda Allah ya Rubuta zai faru same mu.
Wahuwa maulana_ kuma Allah shine majibancin dukkan lamuranmu.
Wa'allallahi falyatawakkalu mu'uminun_Ga Allah kad'ai ne mu mumumai ne zamu dogara."

Sadiq ya karishe fad'a ya na kallon Tahir kafin ya Dora da fad'in"Saboda haka ka kiyaye irin wad'anan mganganun. Ko wani kaji ya na yi ka fad'a masa Allah shine masanin gaibu ba Mutum ba."
Daga haka ya cigaba da abunda ya ke yi ya bar Tahir ya na kallonsa.
Ba domin wa'azin Sadiq ya wani Shigesa ba. Dole fa akwai ayar tambaya acikin Rayuwar yarinyar sai ace haka kawai komai ke faruwa kai ina da walakin Goro a miya. Dole sai ya yi kamar ya na yi Ko saboda abotan da ke Tsakaninsu da Sadiq ba zai taba bari ya saka Rayuwarsa acikin Tsaka mai wuya ba.

Tun daga ranar bai kara yi ma Sadiq mganar ba saboda yasan ko ya yi masa bazai Sauraresa ba.
Sai ma karin wasu ayoyon da za su biyo baya da tarin Hadisan da Sadiq zai rika gayamasa ya na fassara masa.
Kuma ya na gani Sadiq bai fasa zuwa gidan ba sannan bai fasa zuwa siyan wannan munafukin Danwaken da ya ke Tunanin koma wani Mugun abu ne ciki ta saka ma Sadiq din domin ta ja Ra'ayinsa a kanta.
Har so ya yi ya kira Umma ya fad'a mata sai kuma ya kasa. Ba sa taba irin haka da Sadiq ba duk da shima kamar dan gida ne bazai kyautu ya kai karar Sadiq gidan su ba.
Ya na cikin neman mafita ne Makarantar da ya ke Hidimar kasa su ka yi Hutu yace ma Sadiq zai tafi gida ko shima zai tafi Gusai? Bai tab'a zaton Sadiq din zai ce za shi ba. Ammh sai ya ce masa shima zai tafi gida ya yi sati biyu sannan ya dawo.
Tahir ya ji dad'i sosai tare da Fatan Allah yasa kafin Sadiq ya Dawo ya manta da zabiyar yarinyar.
Rana d'aya suka tafi kuma abunda Tahir bai sani ba Sadiq a daran ana gobe Tafiyarsu sai da yaje ya yi ma Amma sallama a kan zai je kauye zai jima kafin ya dawo.
Har Amma na fadin ko dai in ya tafi bazai dawo ba ne? Yace mata in sha Allahu zai dawo ai bai gama hidimar kasar ba.
Hasiya ta rakosa har waje in ba idanuwansa suka ga masa karya ba yaga damuwa da kewa acikin Idanuwantaa.
Ya na cikin motar zuwa Gusai ya ke tunawa da mganar ta cikin sanyi in da ta ke cewa"Ammh zaka dawo ko?
Kai ya gyad'a mata kafin yace"In sha Allahu SIYA."
Sai ta d'aga masa hannu alamun bye bye kafin tace"Allah ya kiyaye hanya. Ya kuma dawo da kai Lafiya ASSADIQ."

"ASSADIQ.."

Sunan ya daki zuciyarsa har sai yaji ya amsa acikin jikinsa. Lumshe ido ya yi ya na kallon siraran hannunta lokacin da ta ke d'aga masa hannu da Sanda ta juya siraran kafafuwanta ta koma cikin gida.
Sake Bude' idanuwansa ya yi yana jin wani iri aransa In da gaske ne auran Hasiya Biyu me ya faru da ita ta yi aure aure a kananun Shekarunta? Tabbas akwai wani abu shi kuma mutum ne da ba ya cika Takura ma Mutumin da ke tare da shi akan sanin wani abu na fanni Rayuwarsa.
Ammh zai so ya ji garin ya ya da kananun Shekarunta ta yi aure har Guda Biyu kuma ta na fitowa?
Ya tuna kwanaki har Amma ya taba ma tambayar Ko Hasiya Sikila ce?
Amma sai da tayi dariya kafin tace"Hala sirintar ta ka gani ko?
Haka na Haifeta lafiyanta kalau Abubakar."
Abun mamaki har ya kai Gusai duniyarsa da Tunaninsa akan Hasiya ne.
Acikin ransa Tausayinta ya ke ji tun kafin yaji me ya faru da ita. Tausayin yadda ta na karamar yarinya ta Fuskanci Kalmar Saki har sau biyu.
Da rana ya sauka agida.
Murna wajen iyalan gidan Alhaji Sulaiman ba'a mgana.
Kada su Innani ta ji labari ta kasa zama ta kasa tsayuwa Magajij gida ya dawo. Abba baya nan sanda ya dawo ya gaji shiyasa shashensa ya wuce ya yi wanka. Kafin yaci abinci Tahir ya kirasa yace shima ya sauka gida Tun dazu ba su jima suna mgana ba suka yi sallama.
Salima ta kawo masa abinci ya ci ya sha sannan ya kwanta ya na warware gajiya."

******

Tafiyar Sadiq da kwana Biyu Adda ta zo Dalilin ta kira Adda Fati ta na tambayan lafiyan Amma. Ita kuma ta gayamata Ciwon da Amma ta yi kwana Biyu tsakani sai gata tare da d'aya daga cikin ya'yanta Isuhu Jauro.
Chapter 58 · 0% Book details