← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 69

Sashe 2

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye tace"HASIYAA."! ta kirani cikin muryan ciwo ammh cike da karsashi da Fata. Da Rarrafe na karisa gabanta ina mai riko hannunta guda d'aya, ganin haka yasa ta dora dayan hannunta nata Gabadaya ta jimke hannayena cikin nata. Kwallah suka cikamin kwarmin ido ammh ina kokarin maida su cikin yanayin muryanta tace"Allah ya albarkaci wannan auran naki Hasiya. Fitinar Duniya ya kare ki da shi, Allah yasa gidan zamanki ne Yasa mutuwa ce zata rabaku" Su na d'akin ne ke amsawa da Ameen koda bai kai zucci ba, ni kuma duk yadda naso kada hawaye su kawomin sai da suka zubo kar kan hannayen Amma, itama kamar zatayi kukan tace"Ba kin ce Allah ba? Ai shikenan Hasiya kin gama mgana share hawayen ki kin ji" Sai na zare hannayena cikin nata ina Share hawayen da suka faramin Tsere a saman fuskata. Kamar Daga sama naji wata mata na Fad'in"To an dai Daura auren Allah yasa zuwa anjuma kada mu ji wani bala'in ya afkama angon" Da rinanun idanuwana na kalleta Gambo ce a matsayin y'a take wajen Babanmu. Na kasa mgana to me zan ce? Gaskiya ta fad'a nima Fargaban dake damuna kenan tare da Tsoro. Kafin ma mganarta ta sha iska Inna Talatu Mahafiyar Ramatu tace"Da ikon Allah ba abunda zamu ji sai alheri" Sai kuma Dakin ya Dauka da Insha Allahu cikin yakinin da su kansu ba su Tabbas din hakan zai kasance ko abunda ya faru a baya ne zai maimaita kansa. Had'a ido mukayi da Amma sai ta gyada min kai cikin yakinin da nagani a kwayar idanuwanta, sai na jinjina mata kai Lokaci d'aya ina goge fuskata. Na mike a kasalance ina jan Kafa zan fice Inna talatu ta taidani da Fadi'n"Kada ki ga baki ga Ramatu ba Fati ta kirata suka tafi gidan Dilalliya Jummai, mganar sauran kayanki dake Hannunta" Da kai na amsa mata ina Ficewa, acikin jikina nake jin wannan karon kayan ba zasu dad'e kamar baya ba zasu sake komawa Dilalliya Jummai kamar baya dai. Wannan karon ba Dakin Maman Boy na koma ba,na maman Salihi na shige tunda shi ke kusa da Dakin mu. Kan kujerata na samu na Kwanta ina Numfarfashi. Rufe idanuwana nayi kamar mai barci nan ko ba barci nake yi ba,Tunani ne suka Daibaye Duniyata Gabadaya. In tunanin in na samu zama gidan Salisu Matarsa fa? Wacce tayi ikirarin duk abunda ya samu mijinta sai ta Kasheni. Na tuna labarin da Habiba ta bani da sukaje min jere ita da yan'uwanta haka suka taru suna zagin su da Tijara iri iri, Tunda gida D'aya zai Had'amu da Matarsa uwar ya'yansa. Tunanina ya tsaya cak da tuna in kuma Abunda ya faru da Abubakar ya Faru da Salisu fa? Jikina sai da ya Dauki Dumi da Tuna da Abubakar da abubuwan da suka Faru a baya, har kwanan gobe duk inda wani Dangin Abubukar ya ganni ko ya ga d'aya daga cikin yayyina ba'a rabuwar arziki ba irin sunan da ba su k kirani da shi ba, mugun bala'i kuma sun jima suna rokarmin shi, sun yi kuma ikararin yadda na nakasa Rayuwar Dan'uwansu nima sai sun nakasa ni. Tuna hakan da nayi bansan Dumin da naji a saman fuskata dumin hawaye ba ne, sai da naji digarsu har dogon wuyana da ko Sarka Babu. Yanzu in wani abu ya Faru da Salisu fa? Me zan ce ma mutane da suke kallona da Tabon kashin Tsiya?Da masu cewa Naman jikina ba shi da kyau kuma Rab'ata ma kawai in mutum ya yi da sunan neman aure na shi da arziki har Abada sai dai yaga anayi, ni da akayi min canfi dalilin Haihuwata ne karyar Arzikin marigayi mahaifinmu Alhaji Mamman Mammadi Kona. Ba kuma a bakin bare ba ne wannan mganar abakin Dangin Mahaifin mu ne. Har ciwon Amma da aka kasa gane kanshi an ce duk Sanadina ne, duk in da na zauna na Rayu wajen bazai kara zama mamaro mai amfani ba. A cewar su ni wutsiyar Rakumi ne gani na ba alheri ba ne. Bansan ina kuka ba sai da naji Shesshekan na fita sannan nasan kuka nake yi, ba zan iya hana kaina kuka ba shiyasa sai da nayi ya isheni sannan na hakura na share hawayena. Ba na sallah ina fashi shiyasa na kara gyara kwanciya Barci na neman saceni naji Muryan Ramatu na kiran sunana, daga cikin Dakin na kwala mata kira sai ta jiyo ta shigo. Tashi nayi zaune na matsa mata ta zauna a gefena labari take ba ni yanzu Daga gidan Salisu suke sun je sun kaimin sauran kayan da suka amso wajen Jummai Dilalliya. Kamar da mgana a bakinta yasa na kalleta ina fad'in"Me ya faru? Da sauri Ramatu tace"Babu abunda ya faru kinga Dakin ki? Yayi kyau sosai. Da ya ke kinsan kayanki ba su yi komai ba sai suka kara haska wajen gashi Salisu kamar ya sani ya yi mana Fenti kalan kayanmu" Ta karishe Fad'a cikin Dariya, kallonta kawai nake yi ban yi mgana ba ta cigaba da fadin"A kofar gida muka had'u da Salisu da abokan sa kin ga bakin Mutumin naki kuwa?kamar gonar Auduga" Sai a lokacin nayi mirmishi Da ya fito daga kasan zuciyata. Da gaske ina son Salisu domin kamar Abubakar sun so ni da dukkan zuciyan su, sannan sun toshe kunnuwansu da duk wata mgana mara kyau ko Dad'i a kaina. Lura tayi da Labarin Salisu na Farantamin rai yasa ta cigaba da bani Labarin shi tana fadin"Yana ganin mu ya fara washe mana baki. Ganin Adda Fati yasa bai kwafsa ba, sai da tayi gaba ya bini yana fad'in ki kularmin da Matata. Kin ji yadda yaja kalmar Matata kuwa? Tafad'a tana Dariya nima sai da na Dara, ba ni da waya a hannuna kwanaki ita na Saida da Jikin Amma ya tashi, Salisu ya so ya siyamin na Hanashi ganin Hidimar biki na kanshi, da niyar sai bayan biki zai kara siyamin wata. Daga mganar Salisu muka koma hirar Haihuwarta da zatayi watan gobe, Tana Fad'amin duk ta gama siyan kayan Haihuwa. Cikin karfin jiki da na Zuciya nace"Ai Nura ba daga baya ba. Akwai son kyautatama iyalansa Namiji ne samun kamar sa a wannan zamanin sai an tona" Tayi wani kayattacen Mirmishi kafin tace"Na ma manta ya kirani Dazu muna Hanya. Yace na yi miki Fatan alheri" A d'okance na amsa da Nagode. Domin kaf cikin layin masoyana bayan Iyayena da yan'uwana Ramatu ta Biyo baya wlh Nura na sahun su Salisu da Abubakar su din shakikan Masoya na ne da har addu'ata ina sakasu da Fatan Allah ya had'amu da su a aljannah Firdausi. Mun cigaba da Hira da yasa na saki jikina, muna tare da ita har yammah lokacin mun yi mgana da Salisu da wayar Ramatu yace ba da jimawa ba abokan sa zasu zo Daukana, da yake ba nisa gaban anguwan mu ne da Kad'an. Ramatu ta sanar da su Adda Fati suka fara shirin mika ni gidan mijina a karo na biyu. Da farko tsoro ya hanani sakewa ammh da naga har yammah tayi ban ji wani abu ya taso ba sai na saki jikina, ammh in na tuna na Abubakar shi har an kai ni gidansa. Ya shigo Dakina kenan da ledojin kajin sa na amarci aka kirasa a waya,wayar da ta tarwatsa duka farincikinmu har ma da auran Gabadaya. Wanka Ramatu ta matsamin na sake yi na sauya kaya zuwa wata Shadda milk, ita ta dinkama ni da ita da sunan in ta haihu mu saka ammh da auran nan ya taso sai tace mu yi amfani da shi. Ban yi kwalliya ba na dai shafa Hoda na saka man baki. zuwa Lokacin hayaniyar gidan ta ragu, Kayana na sawa Ramatu ta had'amin su a wata karamar akwatina tun na aurena da Abubakar ne. Dakin Amma a ka kaini bata tawaita nasihan ta ba, Albarka ta sakamin kamar yadda ta saba. kuka nake yi kukan da har ya fito ana jin Sautin shi Ina ji Gambo na sake fadin"Kuka kuma Hasiya? Ke da ba auran Farko ba? Ina cikin Babban mayafin da Ramatu ta sakani sawa, na ke kallonta tunda Shara shara ne ana ganin na waje,ban sa waye ya bata amsa ba tunda akwai muryoyi da yawa a dakin Har da Gabadaya matan gidanmu suna Dakin. Daga karshe naji Muryan Ramatu na Fadin"Ko ba auran Farko ba ne ai aure dai sunan shi Aure" Ni dai ina hawaye muka baro Dakin Amma zuwa Dakin Maman Boy, Adda Fati ta shigo tana fad'in"Ramatu ina ga dai sai bayan mangriba angayen zasu zo ko? Domin naji ana ta kiran sallah" Ramatu tace"To kila dai sai an yi sallar" Adda Fati ta fice tana fad'in"Gaskiya dai mu ma bari mu yi sallar kafin su iso" Tafad'a tana ficewa Daga Dakin sai alokacin Tunanin ina Adda Rukayya ya Fad'omin tun safe da na ganta sau d'aya ban kara ganinta ba. Ko ya'yanta ban ga ko D'aya ba, sai yaron Adda Fati nagani kuma shima zuwa ya yi ya gaisheni. Sai na kalli Ramatu da ke faman latsa wayarta ina fad'in"Ramatu wai ni ina Adda Rukayya ne? Ko ta koma gida ne? Tsam naga tayi kamar tana nazari ni ko na kafeta da ido ina nazarinta, taasan na santa sarai bata isa tamin alaye ba. Sai kawai nayi mirmishin takaici nasan amsar shurunta. Adda Rukayya ce fa ita ce jini na uwa d'aya uba D'aya ammh in ba'a fad'a maka ba sai kace bamu Had'a komai da ita ba. Cikin karyewar murya nace"Ba sai kin ce min komai ba Ramatu na Fahimta. Allah ya sa mu dace" Sai ta kasa amsamin, kallona take yi a sanyaye ni ko sai na kauda kaina. Adda Rukayya ce fa ta kalleni ido cikin ido tace'"Gaskiya Hasiya ki daina zuwa gida na. In wani abu kuke da Bukata ki kirani kawai. Baban su Amna ma baya so yace tsoro yake ji. Baya son zuwan ki gidan shi" Tunda ranar da ta fad'amin wannan mganar na san in da na sauke Matsayin Adda Rukayya a wajena. Ko Amma ta na fad'a ta kuma sha Fad'amin cewa"Hasiya ku yi hakuri da Rukayya. Kaf cikin ya'yana tana da Bambamci ba D'aya take da ke ba, sannan ba D'aya take
Chapter 2 · 0% Book details