← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 69

Sashe 10

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

a Dogon gida ni kuma muka kulle da Diyarta Ramatu sannan tun dawowarmu sai gobara bata kara bin mu ba, Na samu na cigaba da makarantar gwammati Adda Fati ce gwammati ta biya ma Neco. Adda Rukayya daman ta gama ita. Amma bata kwanta ba tana sana'ar sai da Danwake da wake da shinkafa da wake da mai da yaji kuma tana samu tunda ga Adda fati na tayata,nima kuma ba ni da kiyuwa ina da son aiki. Da farko rayuwar ta juya mana baya ammh daga baya sai ta waiwayo mu. Adda rukayya ta samu miji mai hali ma'aikacin gwammati. Sai da mganar aurenta ne Amma ta nemi dangin su Babanmu suka shiga mganar, muna tunanin In Adda Rukkya tayi aure zata ji kanmu ashe ba haka ba ne. Shanun Adda aka saida akayi mata yan kayan Daki tare kuma da sana'ar Amma na ba dare ba rana. Adda Rukayya ta na da wani Hali bata da son yan'uwa kuma bata da Kulafacin uwa ballatana damuwa da Halin da muke ciki,bkomai daga bangaranta ba ma samu tun Amma na Damuwa har ta daina ni daman ban wani shaku da ita ba, tunda ta sha Hantarata da mai Farar kafa har tab'a ce min tayi"Wannan Farin fatar naki ba na banza ba ne. Yanzu haka na tsiya ne da Talauci." Sai da Adda Fati ta yi aure ne sannan muka san taimakon daga bangaran gidan surukai, Habibu mijinta Bakanike ne, kuma yana da Rufin asiri yana sonta,shiyasa mu ma ya ke rikemu da Daraja alherai kala kala yana yi mana sai godiya. Adda Rukayya kuwa ba ta ma Dauke mu da Daraja ba ballatana shima mijinta da Danginsa su darajamu. Mijinta ma kwata kwata zuwansa gaida Amma bai kai sau biyar ba. Kamar ma kyama muke ba shi. Ni ko daman Adda Rukayya ta sha fad'in ni ce na saka Baba ya rasa komai na shi muka talauce kuma kafin mutanen gari su fad'a masa ita ta gayamasa. Shiyasa bai taba amsa gaisuwata ba acewarsa irin mu ko mgana da Fatar baki ce sai ya bi mutum ya Lalace. Bazan ce ban da mu da karatun boko ba,ga yanayin da mu ke ciki yasa ban zurafafa ma kaina sai na yi karatun boko ba, Na san na iya karatun Hausa da Rubutu sannan na iya karanta Turanci iya inda zan iya, Karatun addini kuma ban zurfafa ba,na yi islamiya a anguwan Alkali bayan dawowarmu Samaru na shiga makarantar Dare ta mallam Habu tare da Ramatu na san addinina daidai gwargwardo. Sallah da yadda zan gyara ibada ta gabadaya da sanin hukunce hukunce tsarki da sallah,sanin abu mara kyau da mai kyau, sannan ina iya karanta bakin karatu a duk in da na ganshi. Tun tasowata bazan ce ina da Farinjini ba, ballatana ga yanayina ba kowa ne in ya ganni yake jin ina Burgesa ba ko kawa ban taba yi ba sai akan Ramatu shiyasa har gaban Abada na ke jinta a raina. Sannan na ke sakata cikin farkon Farkon jerin masoyana. Ko a cikin dangin mu ana Hantara na ballatana ga jama'ar gari shiyasa kasancewa ta, mai farin jini bai dameni ba. Ban san me ake kira Saurayi ba sai dai in ga ana zuwa wajen Ramatu ni kuwa bai dameni ba na fi damuwa da lafiyar Amma tare da sana'o'in da muke yi domin rike kanmu. Amma ciwon ta ba shi da suna ko sanadi, ta fara shi daga zazzabi mai zafi sai kuma karkawa da ciwon kai mai tsanani da abun ya yi girma sai ya ke had'a mata har da Ciwon duka gabbanta,kafa, Hannaye, baya da sauran su in ta farashi kamar bazata ta shi ba, sai an kai ta asibiti an mata allurai da ruwa sannan ta ke dawowa hayyacinta. An yi gwaje gwaje har an gaji an rasa gane sanadi ko ciwon, mgana D'aya ce Typoid da Maleria ne, ammh kowa ya ga yadda Amma ke jin jiki sai ya ce ciwonta ya fi karfin maleria. Ta rame ta Lalace ga ciwo ga wahalar rayuwa. Ni da Habiba mu ne karfin sana'ar Danwake da shinkafa da wake,sau biyu muke yi a rana da Safe da yammah, ni na ke yin na safe da yammah kuma Habiba in ba makarantar yammah sai ta kama mun, Amma kuma ba ta iya zama sai dai in ciwon ta ne ya yi tsanani. Mace ce mai kazar kazar da son kai da kawo ta na da karfi na Fulani acikin jikinta kamar yadda Adda ta ke, itama mace ce kamar maza a tsaye take kan kafafunta ta fi Amma Lafiya tunda ita har yau har gobe bata da wani ciwukan wannan zamanin.
Chapter 10 · 0% Book details