← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 69

Sashe 44

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsawa Amma ta dakamin da yasa na Fashe da kuka ina Fad'in"To miye amfanin Rayuwata tun bazan sama ma kaina sukuni da mutanen da ke Zagaye da Duniyata ba? Amma ki Fad'amin meye amfaninna? Ai gwara na Mutu ko kuma na yi nesa da ku gabadaya hankalin ku ya kwanta nima nawa ya kwanta.."
Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Juyowa na yi ina kallon Amma Lokaci D'aya ina nuna saitin zuciyata na cigaba da fad'in"Anan daidai wajen na ke jin kuna Amma. Jiya fa Tsirara a ka yi min ana kira na da sunan Maita. Amma ki fad'amin akwai Tozarcin da yafi wannan ne? Ki fad'amin ta yadda zan iya yaki da Tsaka mai wuyar da ni ke ciki? In ban yi tunanin kashe kaina ba, ban yi kuma yi tunanin shiga Duniya ba. To Amma ki bar ni na koma wajen Adda zan fi samun kwanciyar Hankali."
Kuka na ke yi har sai da na Durkushe Amma ta kasa tasowa itama jiri ta ke gani in ta mike cikin karfin Hali tace"Hasiya na ce miki ba zaki koma ko'ina ba ko? Tare zamu zauna Mutuwa ce ko aure kad'ai zasu Rabamu."
Cikin Ihu nace"Ni kuma in na cigaba da zama anan mutuwa zan yi Amma don girman Allah ki bar ni na tafi."
Amma na kuka ina kuka kafin tace"Sai dai ko mu tafi Gabadaya ammh bazan barki cikin wannan rayuwar ta tsaka mai wuya ke kad'ai ba."
Jin haka yasa na kasa mgana na koma na dora kaina kan akwatin da na cika da kaya ina ta kuka Halin da nike ciki yasa ko Danwake ban tuna da shi ba. ina ji da Safe ana ta zuwa Nema su maman Boy suna fad'in babu mai Danwaken ba ta da lafiya.
Bayan mangriba sai ga Ramatu da Nura sun zo Dubani ita tazo min da Su maltina da Madara sai kayan Marmari da magungunan jiya da Aka Rubuta suka siyomin.
Zuwan Ramatu yasa Amma tace duk yau ban ci wani abu ba Ramatu ta fara lallashina da Fad'in"Haba Hasiya kin san kina da lalura me yasa zaki zauna da yunwa.?
Hannunta na Dauka zuwa Saitin zuciyata ina fad'in"Daidai nan ne ke min ciwo Ramatu. Wlh na zabi mutuwata da wannan Rayuwar."
Da Sauri ta Rufemin baki ta na Fad'in"Ki daina fad'in haka Hasiya. Allah na sane da ke kuma shi ya zaba miki wannan Rayuwar. Fad'in haka kuma Daidai ya ke da nuna masa baki yarda da kaddaransa ba."
Kuka ya kwace min na kwanta akan Cinyarta na fashe da kuka ina Fadin"Kaddaran ne tamin nauyin Dauka Ramatu ya zan yi? Ki fad'amin ya zan yi? Wlh ina so na mutu mutuwa zan yi."
Na ke fad'a ina wani irin Gunjin kuka Ramatu ma sai kukan Nura ne ya ke ta lallashin mu ya karishe da kallon Ramatu ya na fad'in"Ke kuma miye haka? In kina kuka wazai lallashe ta.?
Jin haka yasa ta daina kuka,ni kuma kukan da Amma ke yi yasa na tsaigata nawa Ramatu ta had'amin maltina da Madara na sha ta kuma saka sai da na sha Kayan marmari,sannan ta bani magunguna na sha.
Amma ta kalli Ramatu ta na fadin"Ramatu ki kara lallasamin kawarki. Ta kafe Wajen Adda ta ke son komawa"
Ramatu ta kalleni ina Runtse ido kafin tace"Hasiya Amma ba ta son tafiyarki.  Kuma in kika duba duk in da kike je ba zaki samu sukuni ba in dai ba kina tare da Amma ba ne. Don Allah ki yi hakuri watarana sai Labari."
Kai kawai na gyada mata bawai don na aminta da mganarta ba.
Ai nasan Hanya Amma sai dai ta tashi taga na tafi bazan zauna ina Kara Rusa mata Rayuwa ba. Ga ciwo ga kuma jikin girma.
Haka Ramatu da Nura suka tafi akan gobe zasu dawo. Bayan sun tafi Amma ta zauna ta na ta min nasiha ina sharan kwallah itama ta na sharan kwallah acikin raina ina Tunanin ita Rayuwa meyasa ba ta cika ne sai da Kalubale.? Sai dai ni nawa kalubalen mai girma ne, mai tafiya cikin Tsaka mai wuya.
Na firgita ne Lokacin da Amma ta mike zata fita ta Dauro alwala jiri ya kwasheta saura kad'an ta fad'i sai da ta Dafa Bango ta na salati. Duk da nima ba jin dadin na ke yi ba. Sai dai Amma ce komai nawa gwara ni na Raunana da ita ta Raunana Haka na mike na rikota ina Fad'in"Amma. Me ya faru..?
Cikin Damke Hannuwana tace"Bansani ba, tun safe na ke ta fama da jiri ga ciwon kai"
Jikinta na taba na ji zafi sai gabana ya fad'i cikin wani yanayi nace"Amma Akwai zazzabi a jikin ki fa."
Tsoro daya kada ciwonta ya tashi zaunar da ita nayi, baho na samo da Ruwa a buta na yi mata alwala nace ta yi sallar a zaune Tunda ta na ganin jiri.
Mangariba da Isha'i ta had'a Lokaci daya Bayan ta idar na sakamata abinci taci na bata panadol ta sha ina Fadin"Amma ki kwanta ki Huta."
Kallona ta yi lokacin da na kwantar da ita ina lulluba mata zani a wajen kafafunta.
Hannuna ta rike guda d'aya lokaci d'aya ta na kallona cikin wani yanayi. Cikin sanyin murya nace"Amma menene..?
Cikin wani sauti tace"Don girman Allah kada ki je ko'ina Hasiya. Ina tsoron na kwanta barci ki aiwatar da Kudurin ki."
Sai Amma ta bani Tausayi da Sauri na jinjina mata kai Lokaci daya ina jimke hannunta kafin nace"in sha Allahu bazan je ko'ina ba Amma. Ina tare da ke."
Da Sauri tace"Kin Tabbata.?
Jinjina mata kai na yi ina Fadin"Na Tabbata Amma."
Sai taji dadi ta saki hannuna ta koma ta kwanta tana sauke ajiyan rai.
Ni kuma matsuwa sai ta kamani na Zuba ruwa a buta, na fita zuwa makewayi sanda na dawo har Amma ta samu barci sai nima na samu gefenta na kwantar da kaina Saman katifar jikina na kasan leda ina Tunanin makomar Rayuwata.

*******

*9:30pm*

Jiya bai ci Danwake ba yau ma ga shi bai ci ba, Jiya saboda wankin da ya yi ne yasa bai je ya siya ba. Yau kuma barci suka yi tayi dagashi har Tahir sai Sha daya na Safe suka tashi kuma yana da Tabbacin ko yaje Danwaken ya kare sai ya Hakura.
Gyada ya fita ya siya da rogo chan Babban Titi. Tahir kuma Taliya da wake ya Dafa mai kifi duk ya karnace musu Daki.
Shi kuma baya  Shiri da kifi kwata kwata in har abinci da kifi ba ya ci Tun yana yaro haka ya ke.
Ko yaya ya ci abinci da kifi to ranar yini zai yi amai ba sukuni. Kuma ko karnin kifi yaji yanzu sai zuciyarsa ya tashi. Kuma Tahir yasan da haka ammh Saboda ya saka shi mgana yasa ya kirkiri dafa Taliya da kifi.
Gabadaya Dakin sai da ya Dauki karnin Tsabar wulakanci irin na Tahir akwai nama acikin Miyan da Umma ta yi masa ya zo da shi da ya yi masa mganar ya yi amfani da shi cewa ya yi shi fa yau ji ya ke yi in bai ci taliya da kifi kamar dan cikinsa zai Zube. Sanin Halin Tahir na wulakanci yasa ya fita batun shi.

Yinin Ranar a rashin sukuni ya yi shi da Daddare zuciyarsa ta rika ta shi cikin Masifa ya kalli Tahir da ya gama cin taliyarsa ga farantin nan a gabansa da abun maltinan da ya gama sha, shi kuma yana ta faman Danna wayarsa cikin Nishadi.
Kai Tsaye yace'Tahir kasan me wannan abun da ka yi ya jawo min?
Dakin nan gabadaya sai karnin kifi ya ke yi kuma kasan yadda na ke da Kifi ko?
Kai Tsaye Tahir yace"Sorry Abokina  wlh yau da ban ci taliya da kifi ba, da kaga Hanjina ta waje."
Ran Sadiq ya baci yace"Na kasa cin komai yau a dakin nan  Tahir karni na shiga min ciki cikina."
Tahir ya Dago ya na kallonsa kafin yace"Is That Serious..?
Saboda Takaici Sadiq bai kara mgana ba jin garin akwai sanyi sanyi yasa ya mike ya nemo Jaket din sa ya saka saman Rigar da ke jikinsa.
Ya shuru takalminsa ya fice ya na jin Tahir na fad'in"Ina zaka kuma..?
Ko Tankashi bai yi ba  ya Fice karamar wayarsa ke jikinsa da ita ya yi amfani ya haska tunda ba wuta anguwan ta yi Duhu.
Chapter 44 · 0% Book details