← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 69

Sashe 60

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ramatu ta bud'e ido ta na fad'in"Assadiq kuma? Na ina?
Mikewa na yi jin Noor ta fara kuka ina jijjigata nace"ina wanda kwanaki ya taimaka ya kai Amma asibiti?
Ramatu ta yi shuru kafin ta ce da sauri"Na gane shi wannan Saurayi baki dogo ko?
Wanda ya rakamu dakin da ku ke ciki lokacin da aka kwantar da Amma?
Kai na gyad'a mata batare da na yi mgana.
Ramatu ko mikewa ta yi jiki na rawa ta iso kusa da ni ta na fad'in"Gayamin naji. Ya ce ya na son ki ne?
Ta fad'a lokaci d'aya ta na Dafa kafad'ata. Sai ta ba ni dariya da sai da na Dara cikin Dariyan nace"Wani irin so kuma Ramatu?
Ramatu ta harareni kafin tace"To in ba soyayya ba me yasa baki son nesa da shi? Kuma ma ban da abun ki Hasiya ai garin masoyi ba ya nisa."
Mirmishi na yi kafin nace"Ba fa soyayya mu ke yi ba. Tun bayan taimakon da ya yi mana sai muka saba yana zuwa gidanan sosai wajen Ammah. To cikin sati nan da ya fita ya zo ya yi mana sallama zai tafi kauyen su shine abun ya ke damuna zamu tafi bai sani ba Ramatu."
Ramatu ta kuramin ido cikin mamaki kafin tace"Sai ki kirasa a waya ku yi sallama"
Kai Tsaye nace"Ba ni da lambarsa."
Ramatu ta yi shuru ba ta yi mgana ba.
Ni ma na yi shuru na wani lokaci kafin nace"Ko Amma ta damu tace da ta san da tafiyar da ta yi masa sallama."
Ramatu tace"Ba a nan garin nan ya ke ba?
Kai tsaye nace"Eh shinkafi ko yace sunan garin su."
Ramatu tace"Bazamfare ne kenan"
Ban amsa mata ba ta cigaba da fad'in"Damuwarki akanshi ta ba ni mamaki kad'an Hasiya."
Kallonta na yi kafin na yi mgana ta yi saurin Tareni da cewa"Daga gani kina jinsa kusa da zuciyar ki ko?
Kamar wata gaula haka na gyad'a mata kai ina fad'in"Ban san meyasa ba. Ina yawan tuna shi sannan ina jinsa sosai a cikin wani lungu acikin zuciyata."
Ramatu yar dariya ta yi kafin taje ta zauna ta na fadin"Fata na Allah yasa shima ya na jinki a cikin zuciyarsa kamar yadda ke ma kike jinsa."
Sai alokacin na Fahimci inda ta Dosa da Sauri nace"Ke ba fa wannan ba. Kawai taimakon da ya yi min ne yasa na kasa manta alherinsa."
Ramatu tace"Nima na sani."
Daga haka bata kara mgana ba ta bar ni ina Tunanin mganarta.
Ramatu wai ta na Tunanin Ina son ASSADIQ Ne?

Tuna haka yasa sai da gabana ya fad'i Haramun ne na so wani acikin Rayuwata in dai zan yi duba da Halin da ni ke ciki to aure ko soyayya ta Haramta a gareni ni Hasiya.
Kawai girman Alherinsa na ke Tunawa tare da kirkinsa natsuwarsa da taimakonsa zuwa garemu yasa zuciyata ta bashi waje na musamman.
Ammh ni kaina nasan Assadiq ya fi karfina ko a kafad'an gwada tsara bazan iya tsayawa da shi ba.
Saboda na kauda Tunanin haka acikin Zuciyar Ramatu yasa na kalleta ina Fad'in"Kin samu Labarin Salisu kuwa? Ya jikinsa?
Ramatu tace"mun yi mgana da Musbahu kwanaki yace da sauki ya na tafiya da Sanduna guda biyu."
Kai na gyad'a a hankali kafin nace"Allah ya kara masa lafiya."
Ta amsa da Ameen. Daganan muka yi shuru kowa na ta sake sake, ita daga baya Mijinta ya kirata sai na fita na ba su waje suna mgana ta waya.
Sai Dare Ramatu da Inna Talatu suka tafi da Niyar sai jibi in zamu wuce za su zo sallama.
Gabadaya mun gama had'a kayan mu. Adda tace komai kada mu bari Isuhu zai dawo gobe ya samo mana motar da zata kwashe kayan duk da ba su da wasu yawa.
Habiba kuma aranar ta had'a kayanta Adda Fati da tazo suka tafi Tare sai Murna ta ke yi. Ammh da niyar gobe in zamu tafi za su zo mu yi sallama da Safe.
Matan gidanmu da makota sai jajanta Tafiyar Amma suke yi. Sabo shi a ke yi ma kuka daman duk sai suka ji ba Dad'i muma haka.
Mun kwana da shirinmu sai ga shi Allah mai sauya lokaci Da safen Isuhu ya kira Adda a waya yace matarsa na kan gwiwa zata haihu tun daran jiya ya kawota asibiti shuru har lokacin bata Haihuwa ba. Kuma ba kowa a wajenta  ba yar garin ba ce yar kwanar farakwai ne da ke nan kaduna.
Jin haka yasa sai Hankalin Adda ya tashi ta yi shirin tafiya mu kuma tace zata je ta gani in an sauka Lafiya Isuhu zai dawo ya tafi damu.
Har acikin raina ban dauka wani Shafin kaddara rayuwa zata kara Bud'emin ba.
Sai ga shi ko da yan Sallama su ka zo Adda ta kusa isa gida ma.
Mu kuma muna nan bamu tafi ba sai dai kawai su ka sha yinin su tare damu Ramatu na ta murna harda addu'an Allah yasa Adda ta fasa tafiya ta hakura ta barmu anan.
Amma kuma acikin ranta addu'a ta ke yi Allah ya sa wannan tsaikon da aka samu Mafitan da ta roki Allah ne ya fara sama mata ta yi ta addu'an Mafita a wajen Ubangiji ga Hasiya ba ta son ta tafi da ita ammh in har Hasiya ta samu inda zata zauna na Har Abada zata koma gaban Adda ta zauna cikin salama har mai kasancewa ta kasance tare da ita. Ba zata rika kwana cikin Fargaba da Damuwa ba.

Habiba dai tunda Adda Fati ta riga ta tafi da ita bata dawo ba sai ya rage daga ni sai Amma. Tunda nasaka tafiyar a raina sai na cire sana'ar Danwake a raina tun ballatana da Assadiq ba ya nan sai sana'ar ta fita raina. Sai dai ana ta zuwa neman Danwaken sai nace ma Maman boy ko zata fara yin Danwaken ne kada ma su siya su gudu.
Nan da nan ko tace zata had'a jari ta fara, ni na zauna na nuna mata Tsarin komai sannan na bata shawaran ba sai ta tara jarin ba. Ta fara da kad'an a sannu sannu dai zata ga jarin nata ya taru.
A rana sau d'aya na ke girki tunda dagani sai Ammah wani lokacin ma ba na yin girkin sai da Daddare da Safe ko Tea ko kuni mu ke sha sai Dare mu ke kara neman abinci. Tun tafiyar Adda ba mu yi waya ba tunda ba ni da waya sai da Adda Fati ta kira wayar maman boy mu ka yi mgana tace Adda ta ce a fad'a mana matar Jauro ta sauka mu duba Isuhu cikin Satin zai zo mu tafi tare.
Tunda naji haka sai muka zama cikin shiri daman kuma ba mu wargaze duka shirin kayammu ba tunda ba fasawa muka yi ba.
A daran muna zaune da Amma ina yanke mata farcenta tace"Hasiya ni ko kwana nawa Abubakar yace zai yi achan garin su?
Kai Tsaye nace"Ban sani ba Amma. Nasan dai yace zai kwana biyu kafin ya dawo."
Muka yi shuru dukkanmu ina ajiyar Zuciyar Amma sai kuma chan tace"Na so a ce yaron nan ya dawo ko godiyar irim Dawainiyar da ya yi damu na samu na yi masa. bazai ji dadi ba duk ranar da ya zo ya iske ba ma nan"
Shuru na yi ban yi mgana ba saboda abunda ke raina ne Amma ta fad'a.
Da safe mai gidanmu yazo Daman Amma ta aika a fad'a masa zamu tashi akwai ragowan kudin mu tunda bamu cike Shekara ba.
Da ya nemi ya bamu ragowan kudin sai Amma tace ya barshi kawai mutumcin sa a gareta ya fiye mata komai alokacin duk in da muka je neman haya a hanamu a ke yi saboda Hasiya ammh shi ya ba su wajen zama tagode sosai Allah ya jikan magabata.
Suka rabu cikin amimci ta na masa addu'a shima ya na yi mata Fatan alheri.

Na riga na Sadakar tafiya ba fashi sai na saki raina kawai Acikin raina na ke jin shima Assadiq ya na daga cikin Mutumen da na ke had'uwa da su a rayuwata ammh kuma na d'an Lokaci ne zasu fita daga Rayuwata batare na so ba sai dai nayi addu'an a duk inda ya ke Allah ya biyasa sannan ina Fatan Allah ya had'amu a Darussalam.
Ina da tabbacin a wajen Adda bazamu sha wahala ba tunda ta baro Rugga da jimawa domin isuhu ya gina gida acikin gari ya Daukota suka dawo.

Sannan daman ya'yanta duk maza ne tafi Amma yawan haihu. Matan nata guda Biyu ne Halima(Tumba) sai Fatima( Baddo') da itace Auta yanzu a gabanta. Shiyasa na cire damuwa Assadiq a cikin raina ammh na kasa daina jinsa a chan kasan zuciyata.

******

GUSAU.
Chapter 60 · 0% Book details