← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 69

Sashe 46

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar an yi ruwa an dauke ban ga kowa a waje ba shiyasa na Dauki Hanya ina tafiya gudu gudu tunanina na tafi Chemist din gaban gidanmu na nemo Taimako ba na ko ganin gabana jefa kafafuwana kawai na ke yi ina ji kamar zuciyata zata fashe.
Sai ji nayi na bangaji mutum da karfin da yasa ya yi baya nima na yi baya ina rawan jiki.
Sadiq da yaji ya sha bangaza kamar wasa ya ja baya cikin mamaki gabansa bai Fad'i ba sai dai ya yi kokarin kiran sunan Allah.
Ni ko yamayin da na ke ciki yasa ban ko Tsaya ba sa Hakuri ba na kama Hanya zan wuce da fitilar wayarsa yasa ya haske Fuskata daga sama har kasa ya ke bi na da kallo ganin kafafuwata ba Takalmi da kuma yanayin da ta ke ciki yasa da Sauri ya ce"Ke ke Baiwar Allah."
Jin ya kirani yasa na juyo ina kallonsa da idanuwana da suka Kumbura.
Cikin Wata irin murya naji yace"Lafiya kike tafiya ba takalmi?
Har zan wuce sai na Tuna Amma kawai sai na dawo gabansa na Duka ina Fad'in"Amma Amma ce. Don girman Allah bawan Allah ka taimakamin Amma ce ga ta chan. Kamar ta mutu bata Numfashi."
Na fad'a cikin gunjin kukan da yasa na Duka na Dafa kafafunsa ina Cigaba da Fadi'in"Bawan Allah ka taimakamin don Darajan Allah. Don Daraja da kaunar da ka ke yi ma iyayenka ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka. Ka taimaki mahaifiyata kada ta mutu."
Sadiq ya ja baya da Sauri cikin in ina ya ce"Kinga yi shuru yanzu ina mahaifiyar ta ki ta ke?
Ina jin haka na mike jikina na rawa nace"Ta na. Ta na gida."
Sai kawai yace"Mu je na gani."
Jin haka yasa na yi gaba da Sauri ina Tafiya ina Hardewa shi kuma ya bi bayana har acikin zuciyansa Lokacin da nake tafiyan nan ya Tsorata.
Wata zuciyar tace"To in Aljana ce fa Sadiq?
Tuna haka yasa ya rage tafiya har sai da na yi masa nisa sannan na juyo ina kallonsa ba na wani ganin Fuskarsa akwai Duhu daga nesa yace"Ina ne gidan?
Da hannu na nuna masa gidanmu ina Fad'in"Ga ga gidan chan."
Jim Sadiq ya yi kafin ya kad'a kai yace "Muje.."
A ransa yace Allah kaga Niyyata na Tausayi da taimako kada ka bari wannan yarinyar ta Cutar da ni in ta na da Niyyar haka.
Yadda da Allah da kuma addu'a yasa ya bi Bayan Hasiya har cikin gida saboda dare da kuma yanayin da Sadiq ya ke ciki yasa bai iya gane gidan da ya ke zuwa Siyan Danwake ba ne.
Bai ji hankalinsa ya natsu ba sai da Hasiya ta yi masa Jagora har cikin Dakin Yaga Amma kwance kamar ta Mutu.
Cikin kuka na Nuna masa Amma ina Fadin"Ka duba ta. Ta mutu ko?
Da Sauri ya isa gabanta ya rike hannunta na wani Lokaci kafin ya Dago ya na kallona cikin kuka nace"Ta mutu ko?
Da Sauri yace"A'a ta na numfashi sai dai muna bukatar kai ta asibiti da gaggawa."
Kawai sai na sulalle ina wani irin kuka bai Saurareni ba ya fice daga Dakin da sauri ni kuma sai na Dora Hannuna a saman kaina ina Fadin"Wayyo Allah na shiga ni Hasiya na lalace"
Na Dauka ya tafi ne shiyasa kawai na koma na zauna ina Rafzan kuka babu wanda zai taimake ni a wannan Halin da muka samu kan mu aciki.
Sai dai me sai ga shi Mutumin nan ya Dawo da Sauri ya na fadin"kama min ita ga adaidata chan na samo mu kaita aaibiti."
Ina jin haka na mike jikina na rawa na tayasa ya daga Umma sai ya Fahimci nima sai a Hankali Tunda jiri ya kwasheni na kusa Fad'i sai da ya Rikemin hannu da hannunsa Guda daya cikin Tausayawa ya ce"Ki na lafiya.?
Kai na gyad'a masa ina sharan Hawaye ganin bazan iya ba yasa ya ba  ni wayarsa ya na fadin"Rike min ki gani" da Sauri na karb'a sai ga ni nayi ya ciccibi Amma da dukan Karfinsa yana fadin"Ki biyo ni a baya ki rika haskamin hanya."
Da Sauri ko na bi bayanshi wai sai da muka fita ne sai ga matan gidanmu suna Bude kofa suna Fitowa ganin an Dauko Amma kamar ba rai yasa su Maman Salihi ke fad'in"Wayyo jikin Amma ce ya tashi?
Ko kallonsu ban tsaya yi ba daman shi Tuni ya yi gaba. Da muka fita mai adaidaitan ya taimaka muka sakata a adaidaitan shi gaba ya shiga ni kuma na shiga baya na rike Amma.
Mun fara Tafiya mai adaidaitan yace"Wani asibiti zamu je yallabai?
Juyowa ya yi ya na fadin"Wani asibiti ku ke zuwa.?
Cikin kuka nace"Kowanne muna zuwa."
Tsayawa ya yi kawai ya na kallona ina kuka ba haske acikin adaidaitan shiyasa baya ganin Fuskarta.
Cikin natsuwa ya maida Hankalinsa wajen mai adaidatan Lokaci daya yana Fadin"Asibitin da ya fi kusa ka kaimu chan."
Kukan ne baya so ya na da Raunin zuciya bangaran Tausayi.
Wani asibitin kudi da ke samaru ya kaimu muna zuwa ya fita ya kira Nurses suka zo da abun Daukan marasa lafiya suka Dauki Amma suka yi ciki da ita.

Mu kuma muna waje muna jira yadda bai zauna ba nima ina Tsaye ina Tsiyayan hawaye.
Kaina na rufe shi da zanin da Lallube jikina baya ganin Fuskata Tunda muka kawo Amma aka shiga Emergeny da ita ba su fito ba sai daya da wani abu na Dare shima ta agogon asibitin na Fahimci haka.
Mutumin suka yi ma bayani sannan shi naga ya na ta shi ya fita ashe  fita ya yi ya siyo mganguna da allurai a wani kwali suka amsa suka shiga ciki.
Ni ko ina Tsaye jiri na ke gani ammh na kasa zama sai da naji ina barazanar zubewa yasa na samu kujera na zauna ina kara Fashewa da kuka.
Bansan ya zo kusa da ni ba sai da naji Tattausan muryansa yana fad'in"Ki yi hakuri ki daina wannan kukan. mahaifiyarki na nan da Ranta bata Mutu ba."
Da Sauri na Dago Fuskata muka Had'a ido Hudu da shi.
Akwai haske a asibitin tunda akawai wuta da Farin kwai.
Tar fuskata ta haska shima haka tashi.
Kallona ya ke yi yana ganin Fari na da haske kamar wata zabiya ashe ma yarinya ce bai dauka haka ba.
Ni kuma ba ma shi na ke kallo ba Tunani na da ya ce Amma na da ranta ba ta Mutu ba.
Cikin Dashewar murya nace"Amma ba ta Mutu ba?
Kai ya gyadamin kafin yace"In sha Allahu."
Da Sauri nace"To ta na ina?
Kai Tsaye yace"Ta na ciki sun ce jininta ne ya yi kasa sai low sugar ammh sun samu nasaran ceto numfashinta."
Sai kawai na Rumgume hannuwana a kirjina ina fadin"Alhamdulillah.."
Hawaye na Diga bisa zanin jikina.
A jikina naji gir!
Har sai da na tsorata sai daga baya na Fahinci wayace na daga zanina na Dauko wayar bawan Allah nan ne.
Na mika masa lokacin shi kuma ya na kallon gefe na ya na Tsaye ya saka Hannayensa duka cikin Aljihun wandonsa.
Cikin wani yanayi na ce"Bawan Allah."
Kai Tsaye ya juyo sai na mika masa wayar ina Fad'in"Ga wayar ka ana kira."
Bai karb'a ba sai da yace"Sunana Abubakar Sadiq. Ba bawan Allah ba."

Da Sauri na kallesa jin sunan da ya ambata suna mai Daraja a wajena.
Shi kuma bai Kara kallona ba sai kawai ya juya ya d'an yi nesa da ni ya na amsa wayarsa.

*Wattpadian Family kuna da yawa masu karantawa, ammh kun rage comments da Vote*

*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332. mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*

*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA..!*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.

*14*
Chapter 46 · 0% Book details