Sashe 64
Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Surayya ta lamgwabar da kai kafin tace" mu dai kada garin tsayuwa da kafafunka wata ta zo ta yi ma kanwarmu kafa fa Autan Umma."
Dariya ya yi har sai da Hakoransa Farare suka bayyana.
Cikin Tattausan lafazi yace"Baku yarda da kan ku ba kenan?
Surayya ta bushe da Dariya kafin tace"Wa ya fad'a maka? mun yarda da kanmu shiyasa muka ce a bari sai kanwarmu ta kara girma mun koya mata komai ta yadda zamu kama Autan Umma a hannu ba wacce kuma ta isa ta nuna mana yatsa."
Shi dai dariya kawai ya yi bai yi mgana ba ita kuma ta cigaba da fad'in"Ni fa tsoro ma na ke yi kada wata yar zariya taga dogo autan Umma Shalelen Innani ta lafe maka mu muna nan hamgame da baki."
Sai a wannan karon yace"To miye? In naga ta yi min sai na aureta."
Surayya ta bude baki kafin tace"Ka aureta kuma? Kai Sadiq fita daga idon mu."
Ya na yar dariya yace"To ai naga ni ba Mijin Sultana ita kadai ba ne. Ni sadiq mijin Mace ne har guda Hud'u."
Surayya tace"Uhm ai fa."
Ta fad'a ta na mele baki. Mirmishi ya yi kafin yace"Yes kin ga ko bayan kanwar ku akwai wajen mata uku so gwara ku bi a sannu."
Surayya tace"Mu zamu cike gurbin wajen mata ukun in sha Allahu."
Sadiq yace"Zaku iya?
Surayya tace"Sosai ma."
Sadiq na dariya yace"Shiyasa ki ka hana Dr kara aure ko? Ke kadai ki na wahalar da shi ko?
Fari ta yi da ido kafin tace"ni ban hana shi kara aure ba. Gurbin sauran matan ne na cike masa kaga kenan baya bukatar kara auran"
Nan fa suka fara musu ya na cewa ta sakar ma Dr. Kanbun da ta daureshi ya kara aure ita kuma ta na rantsuwan cewa ita bata hanashi kara aure ba ya yo auran ya gani ko a jikinta ita dai Tunda tasan kanta kishiya in dai ba ta karkashin kasa zata bi bazata taba kada ita ba.
Da ta ga ya dage ne kawai sai ta karkace baki ta na kallon shi kafin tace"Tsaya Tsaya. Wai ko ka samu wata ne a zariya ka ke min sharan Fage?
Wannan karon sosai ya yi dariya kafin yace"In na samu wata a zariya ai ba na bukatar wani sharan Fage Big Sis. Ina ce ni ne mai auran kuma naga shi auran Sunna ne da Ra'ayi ba na Tunanin in ina Ra'ayi wani zai iya Dakatar da ni."
Surayya ta kura mishi kafin tace"Ka tabbatar ba wata ko Sadiq?
Kai Tsaye yace"Wlh ba wata Bigs Sis in da ita da tuni kun sani."
Sai alokacin ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Yaushe zaka baro zariyan nan ne?
Kai tsaye yace"Nan da wata shidda. Ko kilama na yi masters dina achan."
Surayya ta zaro ido kafin yace"A'a wlh bamu yarda ba. Tunda bakasan waje ga BUK ta garin kano"
Kai Tsaye Sadiq yace"Ni kuma Duk wata makaranta bayan ABU ne a wajena Big sis."
Cikin mamaki tace"Na rasa me ka ijiye a garin nan ne Sadiq baka san barin shi ko sultanan ma chan zamu kai ma maka ita?
Sadiq ya yi shuru kafin yace"A'a."
Tabe baki ta yi kafin tace"Allah yasa da gaske ka ke yi."
Dariya Sadiq ya yi kafin yace"Da gaske na ke yi ma in nagama abunda ya kaini dawowa zan yi nan ne asalina Big sis. Sultana kuma in da na samu aiki nan zan ijiyeta."
Jin abunda yace ne yasa Surraya taji dadi suka cigaba da Hira.
Yana gidan har bayan La'asar ya na ma shirin tafiya sai ga Dr ya shigo.
Sai ya tsaya suka gaisa har ya rika jansa da Hira da yasa ya bata lokaci sai gabda mangariba ya fita.
Da d'aya motar Abba yaje ya shigo anguwan kenan aka kira sallar mangariba sai da ya tsaya ya yi sannan ya karaso gida.
Akwai sakon Umma Dambun kaza ita da Mama sai na Abba kuma yamball ne.
Shi kuma na shi pepe chicken ne abunda ya fiso tace in zai koma ya gayamata ta yi masa kayan Fulawa ya tafi da shi.
To a daran Tahir ya kirasa yace gobe zai dawo Zariya. Ganin shi bai shirya ba yasa yace ya fara yin gaba shi sai jibi sai ya dawo da haka suka rabu.
Sai da Safe da yaje shashen Umma ya gaisheta ya sanar da ita gobe zai koma
Ita ta kira yan'uwansa ta sanar da su tafiyarsa.
Zuwa Dare sai ga sakonnin su dukkansu har Sajida ita Dambun nama ta yi masa mai yawa sauran kuma kayan Fulawa ne soyayyan Nama tunda susan ya na so. Umma kuma ta yi masa miya mai yawa daman ita ta saba yi masa mama ta saka Salima ta yi masa Cookies da yawa na tafiya tunda yace in ya tafi zai jima bai dawo ba.
Innani dai bata dawo ba har ya tafi Abba 100k ya saka masa ta acct dinsa bayan Direba ya kaisa har zariya.
Da kaya niki niki tunda harta kayan abinci da su Ruwa da Drinks da su ya ke tahowa daga gida tun baya Dauka Umma ke matsawa ya ke tafiya da shi.
Wasu kayan maggi mangyada Duk Umma ke sakamai sai ya je ne ma in Tahir na duba kayan sai yace abu kaza ne da kaza ne shi tunda ba Dubawa ya ke yi ba.
Ya dawo zariya daidai ya yi kwana sha shidda baya nan ya iske Tahir da yadawo ba abunda ya yi sai ma Datti da ya karama Dakin dole ya Tube ya gyara Dakin sai Dare ya gama wanka kawai ya yi ya kwanta.
Koda ya tashi Tahir ya dafa musu Farar shinkafa sai suka ci da miyar nan da Nama. Sai da suka je sallar Isha'i suka dawo sannan suka zauna saman Hira.
Tahir na ba shi labarin yadda yaji dadin zuwa gida hutu da sakon gaisuwarsa Sadiq daga Hajjo da Sauran yan'uwansa.
Tahir ne ya tambayi Innani shi kuma ya fad'a masa ta na Gummi gidan su Umma har ya dawo bata dawo ba.
Ranar raba dare suka yi suna Hira kafin su kwanta da gari ya waye kuma da wuri suka tashi suka yi shirin fita wajen aiki.
Sadiq ya zo da sabbin T.Shirt da Jeans daga gida harda Sabbin Yadika dikkaku da Shaddodi kayan da ya tafi da su bai dawo da su ba Shinkafi ya tsinta yaje da su ya bama su Goggo Husai yace ta bama ya'yansu tunda kayan su chan sai a hankali.
Sabbin da ya zo da su rabi ya raba rabin kuma ya ba ma Tahir daman ya na masa haka ya karb'a ya na ta godiya.
Tare suka fita saboda sun makara yasa suka hau mashina kowa ya nufi inda za shi. Sadiq ya riga Tahir dawowa yau shiyasa har sai da ya yi wanka sannan Tahir ya shigo.
Shi ya Dafa musu macaroni da wake suka ci da Miya suka kora da lemu da Safe Tea suka sha da Cakes har kuma Diba Suka yi da za su fita.
Sadiq ya fara d'iba Tahir ma ya gani shima yace tunda zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai bari shima ya D'iba.
Sai da sukaje masallaci suka yi sallar la'asar suka dawo sannan Sadiq ya sauya kananun kaya jikinsa zuwa wani yadi mara nauyi.
Tunda Tahir yaga haka ya sha jinin Jikinsa kai tsaye ya kallesa ya na fad'in"Ina zaka je?
Kai tsaye yace"Gidan su Hasiya"
Tahir ya yi shuru batare da ya yi mgana ba jin haka yasa Sadiq ya juyo daidai ya na fesa Turare ya ke fad'in"Ko zaka rakani ne muje tare?
Sai da Tahir ya ja karamin Tsaki kafin yace"Allah ya tsareni."
Sadiq ya yi dariya bai ce komai ba ya gama fesa Turarensa ya zura Hula sannan ya zo wajen ma'adanan takalmansa ya Dauki wani baki Budade ya saka lokaci d'aya ya juyo ya na kallon Tahir Kafin yace"Sai na dawo."
Har ya fice Tahir bai ce masa komai ba ammh ko dannan wayar da ya ke yi alokacin ya dakatar.
Har ga Allah ya dauka Tafiyar su gida yasa Sadiq ya manta da wannan zabiyar yarinyar ashe ashe bai manta da ita ba.
Har Sadiq ya fice ya na chan ya na saka Tunanin yadda zai raba Sadiq da wannan yarinyar da ya ke tabbacin mayyace daga labaranta marasa Dad'i.
*******
Har acikin raina na cire rai tare da Tsammani zan kara had'uwa da Assadiq.
Shiyasa har acikin raina ban kawo ma tunani zan kara ganinsa ba.
Na riga na sakama rai na zan bar wannan muhallin zuwa wani waje na dabam.
Duk da har lokacin Isuhun bai zo ba bamu kwance shirin mu ba Tunda Adda Ta tabbatar mana da cewa zai zo kuma zai taho damu.
Musan yanayin Rayuwa ballatana kuma da ga shi an masa haihuwa akwai tarin Hidima a gabansa.
Adda ta sake kiranmu tace mu zama cikin shiri ko gobe ko jibi Isuhu zai zo mu tafi satin chan da ya fita abunda yasa bai samu zuwa ba matarsa suka mayar asibiti daga baya jini ya balle mata ammh taji sauki har ta koma gida Adda na kula da ita.
Tunda Habiba ta koma wajen Adda Fati ni kuma na zama shuru shuru tunda ba Danwake na ke yi ba. Sai ya kasance ba na fita tsakar gida sai in ko zan yi girki ko kuma zan Dafa mana Ruwan zafi gabadaya komai na Rayuwar ne ya daina min dadi.
tuni Maman boy ta fara sana'ar Danwake ni na fara kwaba mata ranar farko ga shi har ta kware. Kuma mutane na siya duk da wasu in akace musu na daina Hakura suke yi saboda sun fi son nawa. Ammh duk da haka ta na samun Ciniki daidai gwargwardo.