← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 112

Sashe 99

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali yake tuƙa motar, tana manne ajikinsa,  ji yake kamar ya maidata cikin jikinsa, wani irin sabon ƙaunarta, yakeji na huda fatarsa, yana shiga cikin jikinsa.  

"Me zakici na saya miki my lovely na?" ya tambayeta, cike da kulawa.

Harshe tasanya, ta tanɗe bakinta, haɗe da cewa  "Ni gurasa kawai nakeson ci, sai kuma shaka, amma gurasan, nafison wanda, aka yanka masa tomatoes, sosai asamansa"  taƙare maganar tana haɗiye yawu.

Dariya sosai tabashi, yanayin yanda tayi maganar kaÉ—ai, ya isa tabbatar maka cewa, cike take da kwaÉ—ayin gurasan.
"Okay kome kikeso ni me samamikine, matuƙar a kwaishi acikin duniyar nan, ni dakaina kikeso nayi miki gurasan ko kuma, nemo miki zanyi a waje?"

Dariya tayi haɗe da dubansa cikin shagwaɓa tace "Kai ka iya gurasa ne?"

"Ko ban iyaba akanki ai zan koya" yafaÉ—i haka yana murmushi.

"Nidai banaka nakesoba, kawai ka nemomin, kuma ma ni nafison wanda akayi a gida, bawai wanda ake sayarwa a waje ba!" taƙare maganar tana me turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

"Wannan me sauƙi ne, yanzu kuwa zan kaiki,  gidan da za'a miki gurasa" yafaɗi haka yana me karya akalan motar tasa, zuwa wani hanu daban.

(Wallahi nima kwaɗayin gurasan nake😋 batun yauba, ko ta wayane, kuturomin please.😥)

Mamakine yakamata, ganin sun tsaya agaban gidan Hajiya, kallonsa tayi haÉ—e da zaro idanunta
"Gidan Hajiya fa,  ka kawo mu" tafaɗa tana wuƙi wuƙi da idanu.

"Eh mana, kinsan Hajiya, ƙwararriya ce, wajen iya sarrafa abinci, kuma ina databbacin cewa ta iya gurasa, taso mushiga" yafaɗi haka yana me miƙa mata hanunsa, alaman takama.

"A'a gaskiya nidai mukoma gida, yanzu idan ta tambayi, DALILINA nason cin gurasa, muce mata me?"

Murmushi yayi haɗe da cewa "Baza ma tatambaya ba, ai itama tasan watarana, mutum yakan jin son cin irin waƴannan abubuwan"  Da haka Zahrah ta yarda suka shiga, cikin gidan.

Suna Sallama a falon, Hajiya dake zaune, tana duba wasu lace's, dake zube a gabanta, ta amsa musu, cike da fari'a, da kuma mamakin ganinsu da tayi, domin kuwa sam bata tsammaci ganinsu, nan kusa ba, saboda basu jima da zuwa ba.

Kan Zahrah a ƙasa, ta ƙaraso cikin falon, cike da ladabi ta durƙusa, akan guiwowinta, ta gaida Hajiya.

Cike da fari'a, Hajiya ta amsa mata, haÉ—e da kamo hanunta, ta zaunar da ita, akusa da ita.

"Batun yauba na faɗa miki, nima uwace, ki saki jikinki dani, zanfi jin daɗin haka!" Hajiya tafaɗi haka cikin son nunawa Zahrah ƙauna.

"Nidai yanzu agidannan, ba a wani damu dani ba, idan nazo ma ba a wani bani kulawa"  abun da Dr.Sadeeq yafaɗa kenan, yanayin yanda yayi maganar kamar wani ƙaramin yaro.

Dariya sosai yabawa Zahrah, ta lura shidai shagwaɓaɓɓene na ƙarshe.

"Ai ni bana yayin tsoho, idan har nasamu sabo, dama ba ɗiya mace ƙarama nake da shiba, to Allah yabani sainace banaso? kariga daka zama goɗo goɗo dakai, me zanyi dakai, ko kinga ya dace na bashi kulawa ne Zahrah?" Hajiya ta tambayi Zahrah.

Kunyarsu ne su duka yakamata, amma kuma yazatayi, Hajiya nason janta ajiki, dole itama ta sake da ita.

"A'a Hajiya, idan kika basa kulawa, zai ƙara shagwaɓewa da yawa!" Zahrah tafaɗi haka, tana me satan kallonsa, ta gefen idanunta, tasakar masa gwalo.

"To kaji abun da matarka ma tace, saboda haka, sai kayi haƙuri" inji cewar Hajiya.

"To ya na'iya, idan banyi haƙuri ba,  kuma tunda kikace haka, saina gayawa Hajiya komai" yafaɗi haka yana kallon Zahrah.

Wayyo Allah, Zahrah ina ƙasa ta ɓule tashige ciki, tsabar kunya, tasani, ƙaramin aikinsa ne, ya gayawa Hajiya, cewa ta nada ciki, amma ko daya kunyatata.

Kallon tuhuma, Hajiya tashigayi musu dukansu biyu.
"Me kuke ɓoyewa?" ta tambayesu.

"Hajiya waifa kwaɗayin gurasa take, kuma wai na gida takeso, shine na kawota ki mata" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙara faɗaɗa fari'arsa.

Kallon Zahrah, Hajiya tashiga yi, na ƴan wasu sakanni, tsab tafahimci abun da take son fahimta,  take wani irin farinciki, ya ɗarsu acikin zuciyarta, hakanan taji ƙaunar Zahrah, ta sake shiga zuciyarta.

"Alhamdulillah! Masha Allah!! aikuwa yanzu zakici gurasa, da kaina ma zanyi miki" Hajiya tafaɗi haka cike da tsananin jin daɗi.   " Ashe dai akwai, tsananin rabo, dake tsakanin Dr.Sadeeq, da kuma Zahrah,  yanzu da ace ta dage, ta kafe kai da fata, ta hanasu aure, shikenan kuma da wannan cikin, alayi za'a sameshi, daga nan kuma, ta ɓata  sunan zuri'arta, domin kuwa aje azo yaro ko yarinyar da aka haifa wajensu zai dawo, tunda Sadeeq shine uban sa" Hajiya tafaɗi haka acikin zuciyarta.

Zama Zahrah tayi, acikin falon, tana me hararan Dr.Sadeeq ƙasa ƙasa, Allah ma yasota da bai ce ciki ne da ita ba, da itakam yagama kasheta, sam bata fahimci cewa Hajiya, ta gane hakan ba.

Bayan mintunan da basu da wani yawa sai ga Hajiya, hanunta ɗauke da plate, wanda ke shaƙe da gurasa, sosai yaji ƙuli, da kuma mangyaɗa, gashi an ƙawata samansa, da dangin su albasa da kuma tumatur, hadda kabeji, ga kuma cocumber,  wayyo wannan gurasar fa tayi, tuni yawun Zahrah ya tsinke, haka ta shiga lasan bakinta, kamar wata mayya, ai Hajiya na aje plate ɗin gurasan, Zahrah ta jawo shi gabanta, sam tama manta da cewa Hajiya surukarta ce,  hanu baka hanu ƙwarya, haka Zahrah kecin gurasan, abun daya yi matuƙar bawa, Dr.Sadeeq mamaki kenan, shidai yasanta, ita ba mutum bace, me cin abinci da yawa, hasalima idan zataci abinci, aɗan ƙaramin kwano take  ɗebowa, amma yau gashi tana cin gurasa, tana wani lumshe idanunta,  kamar bata taɓa, cin abinciba, haka takeyi, idanu kawai, ya zuba mata, aduk ko wani minti ɗaya ƙaunarta sake cika zuciyarsa take.

Sosai Zahrah, taci gurasan nan, sai da tajita ta ƙoshi nak, kamar tunbinta, zaiyi bindiga, kafun ta ɗauki, goran ruwan faro, takai bakinta, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa, akai akai, kamar wacce tayi tsere.

"Sannu" Dr.Sadeeq, yafaÉ—a mata haka, cike da kulawa.
Murmushi tasakar masa haɗe da  ɗan matsowa kusa dashi, dayake Hajiya bata falon.

"Naci gurasa saura shaka" taƙare maganar tana tanɗe ɗan ƙaramin bakinta.

Idanunsa ya zuba mata, haÉ—e da cewa.
"Wani irin baby ne haka na samiki, me masifar ci, da kuma kwaÉ—ayi?"

Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa.
"Wallahi inaji, idan bansha shaka ba, akwai matsala, batun yauba nake jin kwaɗayi matsananci, amma na yau ɗin dai yayi over, har inajin idan bansamu, abun da nakeso ba, bazan iya koda yin  bacci ba " taƙare maganar tana me shagwaɓe fuska.

Murmushi yayi, haÉ—e da sanya hanu, yashafi kan kumatunta, cike da kulawa yace.
"Allah Yasauƙeki lafiya, My Acici na!"

Dariya suka saka, su dukansu biyun.  
Hajiya dake tsaye, tana kallonsu, batare da saninsu ba, itama ta saki murmushi.
"Ashe da tahana Sadeeq auren Zahrah, ƙwarai da ta tauye, musu haƙƙinsu, Allah sarki, ashe suna son junansu har haka?"
Da wannan zancen zucin taƙaraso cikin falon.

"A'a Hajiyar gurasa, kin ƙoshine kodai a ƙaro miki?" Hajiya tatambayi Zahrah.

Ƙasa tayi da kanta,  haɗe da cewa "Naƙoshi Hajiya, saidai zan tafi da sauran gida, saboda inaso naci kafun na kwanta"

"Wannan ai me sauƙi ne, na aje miki wani ma a kula, idan kin tashi saiki tafi dashi" Inji cewar Hajiya.

"Hajiya bakida Shaka acikin gidan nan ne?  kinsanfa mutumiyar taki, kwaɗayi ta koya, yanzu kuma wai shaka take son sha" Dr.Sadeeq, ya tambayi Hajiyarsa.

"Ai kuwa akwai shaka, acikin fridge, domin kuwa jiya da dare, banajin daÉ—in bakina, shine na haÉ—a nasha, to akwai ragowan, yayi sanyi ma sosai, ae inaga" Hajiya tafaÉ—i haka tana me nufar wajen da fridge É—inta ke aje.

Shaka'n ta ɗauko, ta kawowa Zahrah, wayyo Zahrah tasamu abun da takeso,  gyara zama tayi daɓas, tashiga zuƙan shakanta abunta, daɗi kamar kunnenta zai fita haka takeji.

Hmmm Zahrah, dai basu bar gidan Hajiya ba, saida tayi ƙat,  har guzuri, na gurasa, da kuma, kayan ƙwalama, Hajiya tayi mata,  tatafi dashi,  koda sukazo tafiya, Dr.Sadeeq ya keɓe da mahaifiyarsa, inda ya gayamata cewa,  Zahrah na ɗauke da ciki, duk da tagane hakan, tun kafun ya faɗa mata,  amma sai jin datayi daga bakinsa, yasanya taƙara jin daɗi, sosai,  takuma ƙarfafa masa guiwa, akan cewa kome Zahrah takeso, yayi mata waya, ya sanar da ita, zatayi mata shi ko menene, ta bawa driver, yakai mata har gida, sosai yaji daɗin hakan...
Chapter 99 · 0% Book details