← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 112

Sashe 73

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saida kusan gabaki ɗaya mutanen da suka kawo Zahrah suka soma watsewa zuwa wajen dinner, kafun Husnah ta matso kusa da amarya Zahrah wacce take aikin kuka.   Hannayenta takamo haɗe  da zama gaf da'ita.

"Please Zahrah kidaina wannan kukan, yanzu haka Doctor yace inkai masa ke yana boys guaters, kuma kinga babu amfanin kije wajensa kina kuka" Husnah tafaÉ—i haka ga cikin lallashi.

Zahrah dai bata kumace da'ita komai ba bata kuma daina kukan ba,,  wayar Husnah ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Dr.Sadeeq ne keyawo akan screen ɗin wayar,,  tana kara wayar akan kunnenta yace

"Yadai Husnah, najiku shiru"

Sake kallon mutanen da sukayi ragowa acikin ɗakin Husnah tayi.  
"Gaskiya babu dama Doctor, saboda dazaran anga zamu fita za'ace ina zankaita" Husnah tafaɗi haka cikin ƙasa ƙasa da muryarta....

Ajiyar zuciya Dr.Sadeeq yayi haÉ—e da cewa
"Okay to bakomai zan san yanda za'ayi, ku shirya me meckup tana nan zuwa"

Cikin matsanancin ciwon kan dake ɗawainiya da'ita tashiga toilet ta ɗauro alwala, kan ƙaton darduman dake shimfuɗe a tsakiyar ɗakin ta hau ta kabbara sallah'n magriba,, tana idar da sallan meyi mata meckup ta ƙaraso, haka tanaji tana gani ta bada fuskarta aka zizara mata meckup wanda yaɗauki fuskarta sosai..  Yauma dai meyin meckup ɗinne ta shiryata tsab cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga (wedding gown) na wani tsadadden leshi me matuƙar kyaun gaske, riga ce doguwa har tana sharan ƙasa yayinda bayan rigar aka sanya wani haɗaɗɗen net me matuƙar kyaun gaske, sosai net ɗin da aka sanya abayan rigan yakuma ƙawata ɗinkin,   lace ɗin yakasance light pink colour yayinda kayan ƙyale ƙyale najikinsa yakasance golding ash colour,  sosai kayan yayiwa Zahrah kyau,,, haɗaɗɗen ɗaurin ɗan kwali aka tsantsara mata akanta, take tasake yin kyau,,,,   yau dai kwalliya da kuma kyawun da Zahrah tayi haryafi  wanda tayi a ranan kamu, komai nata yau na musamman ne tasha kyau sosai, ga doguwar riganta me ɗaukar hankali, daddaɗan ƙamshi kawai take fitarwa ajikinta me sanya nutsuwa,,  duk da irin wannan kyawun da tayi sai dai fuskarta babu wani wadataccen walwala domin kuwa idanunta sunyi luhu luhu dasu,  cikinta kuwa banda kukan yunwa babu abun dayake yi mata, amma kuma saboda masifar taurin kai irin nata taƙi sanyawa cikin nata komai na abinci..  Husnah ma yau zama tayi akayi mata meckup nagani na faɗa, sosai itama tayi kyau, tasha adonta cikin wata doguwar riga  na golding white lace,  idan ka kalleta dole ka ƙara domin itama tayi kyau sosai dama kuma itaɗin ma ko babu meckup tana da kyau masha Allah....

Yauma dai ango tare da amaryarsa zasu wajen dinner kowa yariga daya tafi harsu Auntie Raliya kuwa....

Husnah ce riƙe da hanun Zahrah suka fito compound ɗin gidan inda motar ango ke jiransu.  

Shikam gaba ɗaya kwana biyunnan salon kyawun  na Zahrah namatuƙar tafiya da imaninsa babu ma kamar yau, gaba ɗaya komai na surar jikinta ya bayyana bama kamar hips ɗinta yafito raɗau acikin rigan..          

Husnah ce ta buɗe murfin motar dayake zaune aciki, sai da ta tattaro ƙasan rigan Zahrah'n  kafun Zahrah ta'iya shiga cikin motar ta zauna,, lumshe idanunsa yayi haɗe da shaƙan daddaɗan ƙamshin daya kawowa hancinsa ziyara, wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe,, kallonsa yakuma dawowa dashi kan tauraruwar da haskenta yacika idanunsa,,,  murmushi yasakar mata me ƙayatarwa, yayinda ita kuwa kanta ke duƙe aƙasa tama kasa ɗago idanu ta kalleshi,,  hanunsa ya sanya ya ɗago haɓarta, sai alokacin ta iya jefa idanunta cikin nasa idon, wani irin abu yaji acikin jikinsa, ita ɗinma hakane, da sauri ta rumtse idanunta,,  abun daba ta tsammata ba, sai jitayi ya jawota jikinsa,   haɓanta yakuma ɗagowa da hanunsa na dama, haɗe da sanya ɗayan hanunsa yashafi gefen kumatunta  

"My Princess!"
yaƙira sunanta cikin wata muryarsa me sanyi. a hankali ta ware idanunta acikin nasa idanun,  ƙasa ƙasa yayi da idanunsa haɗe da maida kallonsa ga ɗan ƙaramin bakinta dayasha lipstick,  murmushi yakuma sakarmata haɗe da sake jawota ya ɗaurata akan cinyarsa.
 
"Kinyi kyau fiye da kullum my princess!" yafaɗi haka still yana me shafa gefen kumatunta da hanunsa,    wani irin kunyarsane yakamata tunda take dashi baitaɓa yi mata irin kallon dayakeyi mata a yanzu ba, haka kuma baitaɓa jawota yaɗaurata akan cinyarsaba sai yau. Marairaice fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa,,   sweet ɗin dake cikin bakinsa ya cire, haɗe da ɗago fuskarta ya sanya mata acikin bakinta,   kallonsa tayi da ɗara ɗara idanunta, kansa ya jinjina mata yana ɗan murmushi, ahankali tashiga juya sweet ɗin acikin bakinta, dama kuma tunsafe babu wani abu daya shiga bakinta inbanda ruwa, sai wannan sweet ɗin daya bata yanzu,,  hanunta yakama yashiga murzawa ahankali haɗe da kafeta da idanunsa wanda lokaci ɗaya suka wani marairaice....   Sauƙeta yayi daga kan cinyarsa haɗe da kama hanunta ya buɗe murfin motar riƙe da hanunta haka suka fito daga cikin motar,, kamar wata jela haka take binsa still hanunta na riƙe acikin nasa, direct wani dogon gini dake cikin gidan nasu suka nufa.   Ita dai kawai binsa take cikin takunta me ɗauke da nutsuwa yayinda rigar jikinta kuwa ke share wajen, don ma wajen babu datti,     wani haɗaɗɗen falo ta tsinci kanta a ciki, suna shiga cikin falon Doctor yatsaya daga tafiyan da yakeyi haɗe da juyowa gareta,  murza hanunta dake cikin nasa yayi haɗe da zaunar da'ita akan kujera,  kaitsaye wajen wani fridge dake aje cikin falon ya nufa,  buɗe murfin fridge ɗin yayi haɗe da ɗauko kwalin fresh milk wanda bashida sanyi sosai,   glass cup ya ɗauka ya tsiyaya fresh milk ɗin aciki, saida yakusa cika kofin kafun yamaida sauran cikin fridge ɗin ya aje..  Inda Zahrah ke zaune ta sunne kai ƙasa ya nufo, aje kofin fresh milk ɗin yayi akan ɗan ƙaramin table ɗin dake kusa da kujeran daya zauna,  jawo Zahrah yayi jikinsa haɗe da sake ɗaurata akan cinyarsa, kofin da fresh milk ɗin ke ciki ya kawo dai dai saitin bakinta, cikin muryar lallami yace
"AnfaÉ—amin bakici komai ba tun safe, banaso kina zama da yunwa fa, banso tayi miki illa, kisha ko kaÉ—anne kinji baby na!"

Tsintar kanta tayi da kasa musa masa, saidai amma kuma gaba ɗaya a tsarge take, bata taɓa zama akan cinyar wani haka ba, hakan yasa gaba ɗaya ta takura,,   a hankali take ɗan shan fresh milk ɗin wanda harkusa da bakinta Dr.Sadeeq yake kawo mata kofin, shan fresh milk ɗin take cike da nutsuwa yayinda shi kuma gaba ɗaya idanunsa ke kanta, bakinta kawai yake kallo, karo na farko kenan arayuwarsa dayaji wani irin muguwar sha'awarta na fusgarsa,,, kafun shida ita su ankara tuni  hartasha  fiye da rabin kofin,, ɗan ya mutsa fuskanta tayi  haɗe da sanya hanu ta shafi ɗakalallen cikinta

"Naƙoshi fa!" tafaɗi haka tana me langwaɓar da kanta gefe. 

"Um'um ban yarda ba nasan kinajin yunwa sosai, ki ɗan ƙarasha ko kaɗan ne kinji _MY WIFE_!"  

Kalmar nan ta_MY WIFE_ daya ƙirata dashi  shiyasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi mata wani iri,,, bakinta ta turo gaba haɗe da cewa
"dagaske ni na ƙoshi, gashi kuma duk kasa janbakina ya goge!" taƙare maganar akasalance.
Chapter 73 · 0% Book details