Sashe 25
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Ki tsaida kukanki Zahrah, kuka baya maganin komai, sai dai ya sanyamiki ciwon kai, addu'a ita kaɗai ce magani, nasanki Zahrah, inakuma da yaƙinin cewa baki kai kukanki ga Allah ba, kiji rani inazuwa " Husnah tafaɗa tana me miƙewa tsaye, kaitsaye ficewa tayi daga ɗakin, yayinda Zahrah tafaɗa kan katifa taci gaba da kukanta,,,
Mintuna kaɗan Husnah tashigo ɗakin hanunta riƙe da wasu magungunan da likita ya kawowa Zahrah, wanda takarɓo wajen Inna,,
Ledan da tashigo dashi ta jawo, haɗe da ƙarasowa wajen Zahrah, tamkar ƴa da uwa, haka Husnah ta jawo Zahrah jikinta, cike da tausayi haɗi da rauni tace " Kidaina kuka dan Allah Zahrah, kinga ko na tahomiki da abincin da kikafi so, Shinkafa da Kifi, Mom ce ta dafa " Husnah taƙare maganar tana mai buɗe wni kula, wanda ta ciro a cikin ledan da tazo dashi,
"Nasan bakici komaiba, kuma koda nace kici ma, cemin zakiyi kin ƙoshi, amma dan Allah kici ko kaɗanne zanji daɗi Zahrah, baki da kowa sai Allah, amma kada kimanta nidake tamkar gudan jini muke, damuwarki damuwata ce " Husnah tafaɗa tana mai zub da ƙwalla,
Kallonta Zahrah tashigayi, take kuma zuciyarta ta karye, sai kawai tafaɗa jikin Husnah, tashiga sauƙe ajiyar zuciya,,
Cike da lallami Husnah tashiga bawa Zahrah shinkafa da kifin da takawo, duk dacewa maɗaci yafi abincin daɗi a bakinta, amma hakanan ta daure takeci, badon komaiba sai don Husnah tacancanci tayi mata komai a rayuwarta, itace mace ta farko data fara bata kyakkyawan kulawa wanda tunda abunnan yafaru da ita babu wanda yabata, sai likita..
Duk da cewa bata wani ci mai yawa ba, amma zaiyi mata amfani,  domin kuwa cikinta yajima ba'asa mai komai ba a cikinsa,,
Husnah nagama bata abincin, ta ɗauko musu Al'Qur'ani guda biyu, miƙawa Zahrah ɗaya taƴi, haɗe da buɗe mata fejin farko, cemata tayi su karanta a tare, duk da cewa da ƙyar muryarta yake fita amma sosai tayi ƙoƙari wajen karanta Al'Qur'ani,n.
Babu abun da yagagari Allah, Al'Qur'ani littafine mai cike da tarin haske, yana wanke zuciyar maikarantasa, yanasanya nutsuwa ga ma'abocin karantashi, take ƙuncin dake maƙare acikin zuciyar Zahrah yasoma ragewa, sunacikin karatun wani irin bacci ya yi gaba da'ita,, take ta kwanta a wajen tahau bacci,,
Murmushi kawai Husnah tayi haɗe da ɗaukar Al'Qur'ani'n, dake riƙe a hanun Zahrah ta aje gefe,
"Kayafe ma ta ya Allah! domin nasan tsananin tashin hankali da damuwa, su sukayi tasira a cikin zuciyarta, wajen mantar da'ita kai kukanta gareka!" Husnah tafaɗa tana mai kallon sama, gudun kada ta tashi Zahrah a bacci yasanya tasoma karatun nata ƙasa ƙasa...
((Ƙawaye: bawai nishaɗantarwa kaɗai shine amfanin muba, mu mata ne, kuma mu ƙawayen juna ne, yana da kyau, mu ƙaunaci junanmu, tsegumi, ƙyashi, baƙinciki, hassada, duk banamu bane, kamar yanda akace ciwon ƴa mace na ƴa mace ce, yana da kyau muɗauki hakan da matuƙar mahimmanci, du kanmu zamuso ace munsamu ƙawa kamar Husnah, to amma ta yaya zamu samu ƙawa kamar Husnah? dole ne mu tsarkake zuciyoyin mu, mudaina mawa junanmu ƙyashi da hassada, mudaina bawa junanmu mugayen shawara, mudaina zuga wasunmu sukai kansu zuwaga halaka, kada ki bata gurguwar shawara wanda zata cutar da'ita, wai don takawo kanta gareki domin kibata shawara, kada ki zugata akan cewa ta aika ɓarna, idan har bazaki faɗa mata alkhairi ba, to kada ki faɗa mata sharri, dukanmu mata ne, kuma dukanmu zuciyoyin mu suna da rauni, ta yarda dake, saboda kunyi shekara da shekaru kuna tare, hakan yasa ta ɗauki duk wani sirrinta ta zazzage miki, maiyasa tayi haka? saboda ta ɗaukeki ƴar'uwa, tunda ta sanar dake duk wani sirrinta, mai yakamata kiyi? saiki riƙe mata amana, ki tsare mata sirrinta, amma saiki kaje ki ka tona mata asiri a wajen mutanen duniya, idan kikayi haka kincancanci a ƙiraki da suna ƙawa? maiyasa muka ɓata kanmu ? mukaraba kan abotanmu ? saboda bama iya riƙe sirrin juna, kuma bamaso kowa ya ƙaru, ko ya samu buɗi, saimu kaɗai, yana da kyau muriƙe abotarmu da kyau, domin a matsayinmu na mata idan bamuyi abota da junan muba, da waye zamuyi? da maza? suda basusan yanda zasu magance mana matsalolinmuba, sirrin mace fa sai mace ƴar uwarta, please Sisters dan Allah muyi ƙoƙari wajen gyara zuciyoyinmu, domin mukasance abokai na ƙwarai, masu rufa asirin juna.))
Zaune yake a katafaren wajen shaƙatawa dake farfajiyar gidan, sanye yake da riga da wando na jamfa hadda hulansa, bakaɗan ba yayi kyau, kasancewarsa matashi mai jini a jika, sannan kuma dama akwai kyau ɗin tubarkalla, Wayarsace ƙirar iphone Xs Max riƙe a hanunsa yana faman latsawa da dukkan alamu abu mai mahimmanci yakeyi, ƙamshin turarenta ne yafara cika hancinsa, a hankali yaɗago kansa yakai dubansa zuwa gareta, sanye take da doguwarriga na atamfa wanda yakama jikinta sosai, yayinda ta saƙala wani ɗan ƙaramin vail a wuyanta, balaifi tayi kyau, tunda dama kyakkyawace.
cike da takun ɗaukar hankali taƙaraso wajen dayake zaune bakinta ɗauke da sallama,
Amsa mata sallaman yayi yana mai É—auke idanunsa daga gareta, domin komai najikinta bayyane yake a fili.
Kujeran dake kusa dashi ta ja, ta zauna, cikin sauyawa murya amo tace, "Barka da zuwa Jarumi na"
Kai kawai yaɗaga mata alamar yaji, batare daya Kuma kallon taba, sake lanƙwasa murya tayi, takuma cewa "Yakamata mu'isa falon baƙi ai, sai nake ga kamar zaman mu anan baiyiba, kasan fa kai ɗin maidaraja ne baidace ace nabarka anan ba" taƙare maganar tana mai kaɗa idanunta, alamar yanga.
"Inaganin nan É—in ma yayi ai basai munshiga ciki ba" Dr Sadeeq yafaÉ—a yana mai gyara zamansa,
Harara Zabba'u ta ɓallamasa ƙasa ƙasa batare daya gani ba, a zuciyarta kuwa cewa tayi "Inbanda Allah yaɗigamin soyayyarka a cikin zuciyata, da mai zai sanyani tsayawa, har ka wulaƙantani "
ÆŠago da kansa yayi ya kalleta, cikin muryan dakewa yace "Ni zan wuce " Â
"Haba Yaya Sadeeq maiyasa kakemin hakane wai ? ko minti 30 fa bakayi da zuwa ba, amma kuma kace zaka tafi " taƙare maganar tana kwaɓe fuska tamkar wata ƙaramar yarinya, ko kaɗan kuma hakan baimata kyau ba, domin kuwa shekarunta ya wucewa abun da take ƙoƙarin yi, (wannan saimu nida bestyna jikar Hajiya sweet 19,lol)
Hanu yasanya a cikin aljihunsa yaciro kuɗi, aje mata yayi akan table ɗin dake gabansu, haɗe da tashi tsaye yasoma tafiya,, ganin haka yasa Zabba'u daɗa ɓata fuska, cike da ƙuncin zuciya, tarufa masa baya.
Mai gadi na buɗe masa gate yafice da motarsa, Zabba'u naganin fitansa, tasaki tsuka cike da takaici, wai ace kamar ita babbar yarinyar da maza suke mararin samunta, amma wai ita wani ke wulaƙantawa, kwashe kuɗin da ya aje mata akan table tayi haɗe da sakai tayi shigewarta gida...
Zahrah kuwa ba'ita tafarka daga wannan baccin da takeyiba, sai ƙarfe 6 na yamma, lokacin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba, har zuwa lokacin kuma Khausar tananan bata tafi ba,,
Koda ta tashi a baccin, ji tayi gaba ɗaya tayi sakayau da'ita, a cikin kaso ɗari na ƙunci da damuwarta, babu kaso talatin, Allahu Akbar haƙiƙa karatun Al'Qur'ani warakace ga duk wani damuwar zuciya, harma da ta rayuwa.
Matsowa kusa da'ita Husnah tasakeyi, cike da tausasawa takama duka hannayenta biyu,
"Bazan gajiya da faɗa miki ba Zahrah, yin imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau, shi'ake so ga ko wani musulmin ƙwarai, kuma Allah baya ɗaurawa bawa abun da bazai iyaba, idan kika ƙara haƙuri ki kaɗau ƙaddaranki, to ina mai tabbatarmiki da zaki samu kyakkyawan sakamako awajen ALLAH, haƙiƙa nasan Zayd ya cutar da rayuwarki, amma Allah bazai barshi ba, da sannu Allah zai saka miki,kimin alƙawari bazaki na yawan kukaba, sannan bazakina yawan damuwa ba, duk da nasan hakan abune mawuyaci, amma idan kika daure zaki iya, sannan kuma kuka baya maganin damuwa, karatun Al'Qur'ani kaɗai zaki riƙa, insha Allahu damuwarki zata gushe, sannan kuma, kinyi kuskure Zahrah kinbari tarin damuwar da kika shiga, ya hanaki kai kukanki ga Allah, kin manta shine maikowa mai komai, dan Allah Zahrah kimin alƙawarin cewa zaki rage sanya kanki a damuwa, duk sanda wani tunani yake shirin zuwa miki, to ki gaggauta ɗaukan littafi mai tsarki, ki karanta hakan zai sanyamiki nutsuwa !!" Husnah tayi maganganunta cikin lumana dakuma son sawa ƴar uwarta ƙwarin guiwa,,
"Bansan mai zance miki ba Husnah, amma haƙiƙa kinwuce ƙawa ke ƴar uwace, kuma koda a cikin ƴan uwanma keɗin ta da bance, namiki alƙawari cewa zan maid komai nawa ga Allah, haƙiƙa rayuwata tana cikin ƙunci da kuma baƙin ciki, amma nasan babu a bunda yagagari Allah, kuma da sannu rayuwata zatayi haske, duk da banda tabbacin hakan !" Hawayene kawai ke tsiyaya daga idanun Zahrah, domin sosai takejin ciwon abun da Zayd yayi mata, yanzu tayarda cewa dama haka Allah yatsara mata, kuma zata rungumi Ƙaddaranta, har Allah yakawo ma ta mutuwarta,, amma dudduniya bata taɓa jin matsanancin tsana ga kowa ba bayan Zayd,,
Sosai Husnah tabawa Zahrah shawara masu amfani, wanda zasu taimaka wajen cireta a damuwa,, saida akayi sallan Isha kafun driver'n gidan su Husnah yazo ya É—auketa...
Tiryan tiryan Baffa ya ɗebi ƙafa, har ofishin Alhaji Umar, gaba ɗaya abun da yafaru da Zahrah, Baffa ya kwashe ya faɗa masa, bakaɗan ba hankalin Alhaji Umar ya tashi, domin kuwa shi Zahrah tamkar ƴa yaɗauketa, saboda mahaifinta yayi masa taimako sosai, cikin faɗa da hargowa Alhaji Umar kecewa zai kai case ɗin koto, saurin dakatar dashi Baffa yayi, haɗe da yagyara zama,  ban baki Baffa yashiga yi wa Alhaji Umar, akan cewa kada yakai case ɗin kotu, domin kuwa yaron yafi ƙarfinsu, sannan kuma idan har aka kai case ɗin kotu, tofa sunan Zahrah ne zai sake ɓaci, wanda basusan an ma ta fyaɗe bama zasu sani, sannan kuma zata rasa mijin aure, domin wasu zasuce ba fyaɗe aka mata ba, ita takai kanta, kuma dole su zasukwan a ciki, domin basu da kuɗi, a yanzu yanda rayuwar duniyar nan take, mai kuɗi shine sarki, kuma mai kuɗi shi kaɗaine mutum, haka wasu suka ɗauka, ko shari'a ake mai kuɗi shiyake nasara,,  sosai jikin Alhaji Umar yayi sanyi, domin kuwa tabbas maganganun da Baffa yafaɗa haka yake, kuma yasan duk kuɗinsa bai isa yaja da wanda suka fisa ba, domin shi ɗan ƙaramin mai arziki ne akan wasu...