Sashe 31
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu kam kasa ɓoye dariyarsa yayi saida ya dara kafun ya ce " Bazan sauƙe kiba ai bani na ɗauko ki na saki ba, zaki iya fita da kanki ma, ai nasan ke jaruma ce zaki iya kare kanki ako da yaushe, har ma zaki iya shiga cikin ko wani abun hawa da ƙwarin guiwarki !"
Saurin kallonsa tayi domin kuwa sarai ta fahinci inda maganganunsa suka dosa, wato dai shima ya hango zallan tsoron dake kwance akan fuskarta.
"Shikenan tunda haka kace" tafaɗi maganar tana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar ta fita.
"Haba ƴar ƙanwata, nifa wasa nake miki, kiyi haƙuri ki bari na kaiki gida kinji ko!" Doctor yafaɗi maganar cikin lallashi, domin yafahimci cewa saurin fushi ne da'ita.
A cikin zuciyarta tayi hamdala, sakamakon hanata fita daga motar da yayi, domin dama burga ce kawai tsoron dake cikin zuciyarta bazai barta ta iya tafiya ba, duk runtsi tafiso shiɗin ya kaita domin tafi yarda dashi fiye da kowa a yanzun..
Kwantar da bayanta tayi akan kujeran motar haɗe da lumshe idanuwanta, gaba ɗaya jinta take a gajiye, ga wani irin ciwon kai dake damunta, a hankali take buɗe idanunta, a zabure tatashi zaune sakamakon ganin da tayi Doctor ya nufi wata hanyar da ita saɓanin hanyar gida.
"Inazaka kaini !" TafaÉ—a a razane, kuma cikin yanayin tsoro,
"Saidake zanyi!" Yayi maganar babu alamar wasa akan fuskarsa.
"Dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeni, ka barni naji da duhun dake cikin rayuwata, kada ka ƙaramin wani bala'in dan Allah!!" tuni hawaye sungama wanke fuskarta.
Wani irin kallo Doctor yayi mata haɗe da sakin murmushi bai kuma sake ce da ita komai ba, saima maida hankalinsa da yayi ga tuƙin da yake,
Yanzukam kuka mai sauti ta sanya haÉ—e da soma cewa " Dan Allah kada ka sake cutar da rayuwata, zan iya amincema ka kasheni amma bazan iya jure wa ba, idan kaci mutumcina, wlh na yarda ka wurgani kan titinnan mota ta taka ni, amma dan Allah kada kamin komai!!" taÆ™are maganar cikin matsanancin kuka mai taÉ“a zuciya. Daidai lokacin suka iso gaban wani makeken mall wanda yagaji da Æ™awatuwa,Â
yana parking motar baiko kalletaba yayi saurin ficewa daga cikin motar haɗe da dannawa gabaki ɗaya ƙofofin fita a motar luck, domin yasan dole zatayi ƙoƙarin fita daga cikin motar,
Kuka sosai Zahrah keyi haɗe da sanya ƙarfinta tashiga dukan glass ɗin motar, tana mai ihun neman taimako amma babu kowa a wajen balle tasaran za a temaketa, domin kuwa wajen parking space ne.
"Ashe duniya cike take da azzaluman maza, ashe itakam rayuwarta a haka zata ƙare? wayyo Allah itakam ƙaddaranta kenan" abun da take faɗa kenan acikin zuciyarta tana kuka mai tsuma zuciya,domin a zaton ta hotel ya kawota zai kuma lalata mata rayuwa.
Daidai lokacin Doctor Sadeeq ya dawo hanunsa É—auke da manyan manyan ledodi guda biyu, yana shiga cikin motar yakuma danna mata luck haÉ—e da mawa motar key da gudun gaske ya hau titi.
Zahrah kam muryanta har ya dashe kukanma harya daina fita domin gaba ɗaya ta gama sadaukar da cewa yau ce ranar mutuwarta,  kukantane yasoma tsagaitawa ganin sun nufi hanyar unguwarsu,  a hankali hawayenta suka daina zuba, yayinda tashiga sauƙe ajiyar zuciya akai akai, bakomai yasa hakanba face ganinsu da tayi sun shigo cikin unguwarsu tsulum, a bakin ƙofar gidan nasu yayi parking cike da kulawa yajuyo da kallonsa ga Zahrah wacce take ta sauƙe nannauyar ajiyar zuciya, alamar taci kuka ta ƙoshi.
"Banga laifin kiba Zahrah, domin dole zakiji matuƙar tsoro, a iya tsawon rayuwata bantaɓa cutar da wata mace ba, kuma bazan fara akan ki ba, bazan taɓa iya cutar dake ba Zahrah, inaso ki yarda dani, ban kuma yi haka don na cutar dake ba, nabiya dake ta mall ɗinne don inaso muje kiyi sayayyan abubuwan dakikeso da kanki, amma sai naga gaba ɗaya kinfirgita, kiyi haƙuri na tsorataki ko ƙanwata !!" Doctor Sadeeq yafaɗi maganar cikin tsananin tausayawa da kuma lallashi ga Zahrah'n..
Kuka kawai Zahrah takuma fashewa dashi haɗe da cusa kanta cikin cinyoyinta, a hankali ya kama hanunta haɗe da matsewa a cikin nasa hanun, "Banason kuka Zahrah, bana ce kiyi haƙuri ba!" Dr yafaɗa cikin damuwa.
"Bakaine zaka bani haƙuri ba likita, nice zanbaka haƙuri, nayi maka mummunar fahimta, dan Allah kayi haƙuri, wlh tsoro nakeji banso wani abu yasake faruwa dani...!" taƙare maganar tana kuka sosai.
"Idan kinaso nayi haƙuri to kidaina kuka kinji ƙanwata!" yafaɗi maganar yana mai ƙare matse hanunta a cikin nasa hanun.
A hankali tashiga share hawayen dake ambaliya akan fuskarta, ji takeyi zuciyarta tayi mata sanyi.
"Bakya kyau idan kina kuka, kinfi kyau idan kina dariya, kije gida kiyi wanka ki huta, banso kisake zubar da hawayenki kinji Zahrah, ungo wannan ledan kishiga gida, akwai waya a ciki na samiki sim da komai, akwai games dayawa a ciki,nasan zai ɗebe miki kewa, banson ganinki cikin damuwa Zahrah, kije gobe zanzo na kaiki school dakaina, Allah yasa bazakimin gardamaba " yaƙare maganar yana ƴar dariya.
Murmushi itama Zahrah tayi haɗe da ƙarɓan ƙatuwar ledan dayake miƙo mata, batare da tayi masa gardama ba, cikin rashin kuzari ta buɗe murfin motar tayi ficewarta, harsai da yaga shigewarta cikin gida kafun ya ta da motar tasa ya bar unguwar tasu..
Zahrah tanashiga cikin gida kai tsaye ɗakinta tawuce, jakarta da ledan da Dr Sadeeq ya bata ta ajiye. Kayan jikinta tashiga cirewa, zani ta ɗaura a kirjinta haɗe da sanya hijabi tafice daga cikin ɗakin,  zaune ta taradda Inna a tsakar gida, sannu da gida kawai Zahrah tayi mata, haɗe da shigewa cikin bayan gida, tana fitowa a wanka ta bi lafiyar katifarta domin dama dai bata wani jin yunwa, ledan da Doctor yabata ta jawo haɗe da buɗewa, kyawawan dogin riguna ne suka bayyana acikin ledar saikuma dangin su snacks dasu choculate, kyakkyawar kwalin wayar da tagani acikin ledar taciro SAMSUNG GALAXY S10 shine sunan da ke rubuce ajikin kwalin wayar,  wani irin faɗuwa gabanta yayi take nunfashinta yashiga gudu akai akai, bazata taɓa mantawa ba shima da haka yafara, daga ƙarshe kuma ya dasa mata babban tabo acikin zuciya da rayuwarta mai wahalan gogewa,  saurin sake kwalin wayar tayi haɗe dayin watsi da kayan da suke zube a gabanta,  talauci bahauka bane, bazata sake bari haka yafaru da'ita ba,  hawaye ne suka shiga sauƙa akan ƙuncinta,  haƙika soyayya bata mata adalci ba, kwanciya tayi lamo akan katifa tana nai sauƙe a jiyar zuciya, jin da tayi zuciyarta na shirin dawowa ɗanyea shakaf ne yasanyata tashi ta ɗauko littafi mai tsarki wato Al'Qur'ani tasoma karantawa domin rage damuwar dake damunta a zuciya....
"Salima kuma Hajiya?" Doctor Sadeeq yatambaya cikin muryar damuwa.
"Ƙwarai kuwa Sadeeq, ko ita Saleema'n tana da wani aibune? ƙwarai nayaba da hankalinta dakuma tarbiyanta, saboda haka nagama yanke shawarata, gobe zanfaɗamawa ƙanin mahaifinku yaje yatambayo maka aurenta, idan ma a so nane banso bikin yawuce nanda wata ɗaya " Hajiya tafaɗi maganar babu alamar wasa akan fuskarta.
Cike da sanyin jiki Doctor Sadeeq yace " Shikenan Hajiya, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma dakin ƙara haƙuri, nan bada jimawa ba zan kawo wacce nakeso"
"Hmmm ai aikin gama yariga daya gama Sadeeq, nagaji dajin wannan zancennaka, koda yaushe haka kake cewa, to yanzu dai nagaji da ƙaululan dakakemin saboda haka natsaida magana,zaka iya tafiya"
Gaba É—aya hukuncin da Hajiyar tasa ta yanke masa baiyi masa daÉ—i ba, amatsayinsa na Namiji bai dace ace anyimasa dole akan aure ba, shi sam Saleema ma bata É—aya daga cikin irin tsarin matan dayakeso, amma yazaiyi tunda dai Hajiya ta kafe, yasanta da wuyar sha'ani, idan tace eh zaiyi wuya kuma tace a'a, jiki a mace haka yafice daga falonnata, kaitsaye ɓangaren sa yanufa, yanashiga cikin falonnasa direct friedge yanufa, goran ruwa mai sanyi ya É—auko, haÉ—e da zama akan kujera, saida yasha ruwan fiye da rabin gora, kafun yashiga sauÆ™e ajiyar zuciya, wayarsa yaciro acikin aljihun rigarsa, kai tsaye lambar sim É—in dake cikin wayar daya bata, ya danna wa Æ™ira, saidai yaji saÉ“anin tunaninsa, domin kuwa cemasa akayi wayar a kashe take, nannauyar ajiyar zuciya ya sauÆ™e, haÉ—e da aje wayartasa a gefe,  "Maiyasa nadamu da'ita sosai ne?" yatambayi kansa, bayan kuma yasan baida amsa,Â
"Inatausayinta sosai,amma kuma bayan tausayi inajin wani abu na daban a ga me da'ita, menene wannan abun ? yazama dole nasan menene amma tabbas ina da burin inganta rayuwarta " Ƙaran wayarsane ya katse sa daga zancen zucin da yakeyi, ganin da sabon number ake ƙiran nasa yasa bai ɗauki ƙiranba, saima tashi dayayi yawuce cikin bedroom ɗinsa...
Washe gari.
Yau tunda safe takammala shirinta, tayi kyau cikin shigar ta ta atamfa riga da sket, yayinda lufayant dake jikinta ya kasance hot pink colour, sama sama tasha ruwan shayin da Inna ta dafa, tana kammala shan ruwan shayin ta ɗauki jakarta haɗe da nufar hanyar waje. domin batamaso likita yazo yasameta, tafiso tayi tafiyarta, sam bataso yanashiga cikin rayuwarta, takuma yanke shawaran gaya masa yafita acikin rayuwarta, domin sam baikamata tasake bawa wani namiji dama ba.
Turus haka taja ta tsaya, domin kuwa tsaye tagansa ajikin motarsa, yasha ado cikin wata blue É—in shadda, sam batai tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacinba.
Murmushi yayi mata haÉ—e da soma takowa harzuwa inda take tsaye.
"Baki tsammaci ganina a dai dai wannan lokacin ba ko?" yatambayeta kansa tsaye yana mai kafeta da idanu.
Ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa "Ina kwana"
"Lafiya ƙalau, yakika tashi?"
"Lafiya" tabasa amsa a taƙaice, haɗe da sunne kanta ƙasa, domin hakanan taji yamata wani irin kwarjini.
"Muje kada kiyi latti ko" Doctor yafaÉ—a yana mai yi mata nuni akan cewa tashige gaba.