← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 112

Sashe 46

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bazanyi kuka ba" tafaɗa cikin muryar da bata fita sosai, da badon yana kusa da'ita sosai bana ma  to tabbas da bazaiji maitace ba..

"Kinyi alƙawari?" yatambayeta

"Eh" tafaɗi haka  bayan taɗanyi jim.....

"Yauwa Zahrah na, nasan ai kina da cika alƙawari, taso muje mota na baki magungunanki"  babu musu ta miƙe daga zaunen da take, haɗe da rufa masa baya.

Murfin motar ya buɗe haɗe da fiddo  wata ƙatuwar leda.

"Ungo magungunan suna ciki, akwai bayanin yanda zakisha a jiki, please ki kulamin da kanki kinji" yafaɗi haka cikin lallashi, haɗe da miƙa mata ledan dake hanunsa.

Kasa amsan ledar tayi, saima kawar da kanta gefe da tayi.

Murmushi Dr Sadeeq yayi, domin kuwa sarai ya fuskanci hakan da tayi metake nufi.

"Kiyi haƙuri ki karɓa kinji Zahrah na" yakuma faɗan hakan cikin lallashi.

Baki Zahrah taturo gaba haÉ—e da cewa ...
"Kasan tun ba yauba nafaÉ—ama cewa banaso domin kuwa hidiman da kakemin yayi yawa, mai yasa bazaka bari haka ba!" ta tambayesa cike da sakalci..

"Saboda kina da mahimmanci, kinkuma cancani namiki fiye da haka,  amma yanzu dai banso kice a'a ki karɓa kinji" still cikin lallashi yayi maganar.. Badon ranta yasoba haka ta karɓi ledan.  

"Saida safe" tace dashi cikin sanyin murya haÉ—e da juyawa ta nufi hanyar shiga gida.

"Kada kimanta kin ɗauki alƙawarin cewa bazakiyi kuka ba, bakuma zaki shiga damuwa ba, kada ki karya alƙawari kinji mai kyau na!"

Murmushi kawai tayi masa haÉ—e da É—aga masa kai alamar taji.
Yana ganin shigewarta cikin gida, shima yashiga motarsa haÉ—e da bata wuta yabar unguwar tasu..

Tanashiga cikin gida, Inna tayo kanta haɗe da fusge ledar dake hanunta,   babu magana ba komai ta shiga zazzage ledan akan tabarma, kallonta kawai Zahrah ta tsayayi cike da takaici, sai yanzu take godewa Allah dayasanya ba Inna bace ta haifeta, domin kuwa da Innace ta haifeta to tabbas da nan gaba kaɗan zuciyarta zata fashe, saboda  wannan halin da Inna keyi ba hali bane na iyayen ƙwarai, batama tsaya ganin menene acikin ledar ba, ta wuce cikin ɗakinta, domin ita dama ba wannan bane a gabanta, yanzu babban damuwarta shine, yanda zata samo maganin matsalarta.

Ɗaukan kwalin nan da aka kawo mata  tayi, haɗe da soma kiciniyar buɗewa, kasancewar bakin kwalin a nane yake da wani gam me kyau..

Tana buɗe cikin kwalin wani tsadadde kuma kyayyawan agogo na mata ya bayya, gefen sa kuwa wani irin awarwarone haɗe da zobe  masu kyaun gaske, wanda dagani kasan na gold ne, domin kuwa kyawunsu kaɗai ya'isa ya bayyana haka, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da mai da murfin kwalin ta rufe kamar yanda ta samu,   ɗaukan kwalin tayi dukansa, haɗe da ɓoyesa a cikin kayanta, dawowa tayi kan katifarta ta kwanta zuciyarta cike tab da tunanin son gano wanda  ya soma
bibiyar rayuwarta...

Hajiya Habiba (mahaifiyar Dr Sadeeq) ne zaune  akan kujera gaba ɗaya ta tattara nutsuwarta ta miƙasa ga Baffa Amadu dake zaune akan ɗaya daga cikin  kujerun falon...

Baffa Amadu ne yaci gaba da cewa " Banzo nan don na yi miki dole ba, amma Hajiya Habiba yana da kyau  wasu lokutan muna ƙoƙari wajen bawa ƴaƴanmu dama akan abun da suka nuna zuciyarsu naso, musamman ma aɓangaren abun da yashafi aure, haƙiƙa Sadeeq yasameni da wannan maganar yakuma min bayani tayanda zan fahimta, Alhmdlh nakuma fahimta, yanzu saura ke,  kada kice wai don ƙaddara ya taɓa faɗa mata, ɗanki bazai aure ta ba,  kada kiyi haka, domin ita ƙaddara tanakan kowa mai kyau da marar kyau,  sannan abu nagaba danakeso kisani, ko da ace alal misali yarinyar  ta kasance karuwa ce,  addini bai hana masa auren taba, wala Allah saboda auren saiki ga ta shiryu, balle kuma ma bahakan take ba, amma bazan miki dole akan cewa saikin amince ba, ɗan kine kuma kina da iko akansa"...

Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauƙe, haƙiƙa Baffa Amadu yazo mata da magana mai girma.
ɗan nisawa tayi haɗe da cewa "Bawai naƙi aurensa da ita bane, saboda wani abu ba ne, kawai dai inajiye masa yanda tarbiyan yaransa zai kasance  ne matuƙar takasance tana cikin gidansa, domin na tabbatar rashin wadataccen tarbiyan da aka bata a gidansu, shiya jawo faruwar haka a kanta,  kaga itama bata samu tarbiya mai kyau ba, balle tayi ƙoƙarin bawa nata yaran, haƙiƙa Sadeeq yarone mai biyayya agareni,  kuma harcikin zuciyata na ƙudurta aniyar cewa bazai taɓa auren wannan yarinyar ba, amma tunda harka shigo cikin al'amarin shikenan na'amince, amma kuma fa sai dai idan su biyun duka zai haɗasu ya aura, kaga dai Salima ƴar wajen ƴar uwata ne, haka kuma mamarta aminiyata ce, bayanda za'ayi na watsa musu ƙasa a ido, tahanyar cewa Sadeeq bazai auri Salima ba, kuma kaga yanzu saura ƴan satika ne suka rage, har anriga da anfara shirye shiryen biki"

"Ƙwarai kina da gaskiya ta wani wajen, amma kuma bamu iya ja da haɗin Allah, yanzu zansanar da Sadeeq ɗin duk yanda mukayi dake, zan kuma faɗa masa amincewarki,   nasan shi ɗinma zai amince da umarninki, amma inaga zaifi kyau ayi bikin nasu a rana ɗaya, domin babu amfanin jan lokaci"

"Eh duk yanda kukace shikenan" Hajiya tafaÉ—i haka badon ranta yaso ba.

"Shikenan to duk dai yanda ake ciki, zai zo yasanar dake" Baffa Amadu yafaɗi haka bayan yamiƙe tsaye ya gyara zaman garen dake jikinsa...

Cike da mutun ta juna sukayi sallama shida Hajiya...

Zama Hajiya tayi afalon haɗe da yin jigum, tabbas ba'ason ranta ta amince da wannan auren ba, saboda ita gani take tamkar yarinyar ba kimtsatstsiya bace,  ta amince ne kawai saboda Baffa Amadu yashigo cikin maganar, kuma tana matuƙar darajasa haɗe da basa girma, domin tana masa kallo ne tamkar marigayi mijinta,  amma da ba haka ba da bazata taɓa amincewa ba, yanzu dai kawai sai dai tayi addu'an Allah yabasu zaman lafiya, amma ta wani ɓangare na zuciyarta, tunani take taya zataje ta tunkari ƴar uwarta Hajiya Furaira da wannan maganar, tasan Hajiya Furaira macece mai zafi,  bazata taɓa son hakan ba, domin saboda bala'inta da zafin kishin ta, ne ma yasanya mijinta haryau yakasa ƙara aure bawai kuma don baya so ba, to ina kuma da idan taji cewa ƴarta ɗaya tilo zata haɗa miji  da wata daban wacce bata da galihu, gaskiya zaiyi wuya ta amince... Haka dai Hajiya tadinga saƙawa da kuncewa daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakinta....

Cikin matsanancin farinciki Dr S.S ke kallon Baffa Amadu sakamakon jin cewa wai mahaifiyarsa ta amince da aurensa da Zahrah, masha Allah ashe  dai mafarkinsa zai zamanto gaskia, sai dai kuma farincikin nasa bai zama cikakke ba, domin kuwa sosai maganar haɗa auren Zahrah da Salima ya daki zuciyarsa, saboda shi a tsarin sa baida burin aje mata biyu acikin gidansa.

"Yanaji kayi shiru ne Sadeeq, ko baka amince da sharaÉ—in mahaifiyartaka bane?" Baffa Amadu yatambayeshi cike da kulawa.

Kansa yashiga sosawa yamakasa ce da Baffan nasa komai..

Murmushi Baffa Amadu yayi domin yafahimci halin da Sadeeq ɗin yake ciki.    "Kada ka ɗaga hankalinka Sadeeq,  atunanina ka kai namiji wanda zai iya riƙe mace sama da biyu, don haka wannan ba abun damuwa bane, kayarda da sharaɗin mahaifiyartaka, addu'anmu shine Allah yatayaka riƙo, yakuma baka dama da ikon yin adalci a tsakaninsu, yanzu yaushe kakeso muje gidansu ita yarinyar?"

Gaba É—aya jiyayi jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa kuwa jiyayi tayi masa wani iri. "Zansanarda Baffan yarinyar idan yafaÉ—amin ranan da zakuzo, saina faÉ—a maka" inji cewar Dr Sadeeq..

"To shikenan Allah yakaimu" daga haka sukayi sallama, Dr S.S yabaro gidan Baffa Amadu zuciyarsa cike da tarin tunani kala kala, yana farincikin cewa Zahrah zata zamo matarsa, amma kuma ta wani ɓangare na zuciyarsa kwata kwata bayajin daɗi.   Zahrah tana buƙatar farinciki da kuma kulawa mai kyau, baikamata ace anraba mata farinciki ita da wata ba, to amma "Miye mafita?" yatambayi kansa, bayan yasan baida amsar tambayan nasa, amma koma dai mene ayau zaije yasamu Baffa yasanar dashi cewa yana neman abashi izini yaturo magabatansa don abasa auren Zahrah, yakuma ƙudurta aransa cewa, dakansa zai bada order a Dubai, na kayan lefen Zahrah, domin kuwa zaiyi rawar gani sosai, wajen ganin komai na Zahrah yafita da ban....

Amatuƙar mamakance Alhaji Ma'aruf ke kallon Zaid wanda yafaɗi maganar daya matuƙar basa mamaki.... "Aure fa kace Zaid, dagaske kake, yanzu kashirya zakayi aure?"

"Da gaske nake Dad aure zanyi, kuma inaso kaje da kanka ka tambayamin, banaso auren yawuce nan da sati biyu Dad"

Cike da tsananin farinciki Alhaji Ma'aruf yace "Alhmdlh! naji daɗi ƙwarai da gaske, domin zuwa yanzu yakamata ace ka aje iyali, insha Allah, zan je na tambaya maka aurenta, ƴar wayene kuma a ina take?"

"Ba Æ´ar kowa bace Dad, talakawa ne ma, amma ni ahaka naji na aminta ina kuma son na aureta" yafaÉ—i haka da iyaka gaskiyarsa..

Jinjina kai Alhaji Ma'aruf yayi haÉ—e da cewa "Zan sa rana sainaje naga mahaifinta"

"To" kawai Zaid yace haÉ—e da tashi yabar falon Dad É—innasa....

Fitowarta amakaranta kenan, tana sauri ta samu abun hawa, don bata son tsayuwa a bakin makarantar, kasancewar Dr Sadeeq aiki yamasa yawa bazai samu daman  zuwa ɗauko ta ba...

Wani matashin saurayine yanufo wajenta, hanunsa ɗauke da wani babban kwali wanda aka rufesa da wani irin abu mai kyau, aka kuma ƙawatasa da flower mai walwali..

"Ranki ya daɗe barka da yammaci"  saurayin yafaɗa.

"Yauwa barkan ka dai" itama ta mayarmasa amsa cikin É—ari É—ari dashi..

"Saƙo aka bani nakawomiki" yafaɗi maganar yana me miƙa mata kwalin dake hanunsa..

Cikin mamaki Zahrah ta shiga kallon saurayin nan dake tsaye a gabanta..

Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake miƙo mata kyakkyawan gift ɗin dake hanunsa.

"Waye ya aikoka?" tayi masa tambayar cikin dakiya...

"amsar tambayarki duka suna cikin nan" yaƙare maganar yana me nuna mata kwalin dake hanunsa.

Hakanan taji zuciyarta ta aminta da ta karɓi saƙon.. Hanu biyu tasa ta karɓa,  batace dashi komai ba tayi wucewarta dai dai lokacin mai taxi ya ƙaraso tashiga.

Tsurawa  kyakkyawan kwalin  idanu tayi, sosai adon jikinsa yayi kyau haɗe da ɗaukar hankali, gaba ɗaya ta ƙosa, tabuɗe kwalin don ganin ko wanene yake son yin wasa da hankalinta, ta hanyar turo mata da saƙonni, batare da yabari tasan kowaye shiɗin ba.
Chapter 46 · 0% Book details