← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 112

Sashe 107

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kyauta daga me gidanka kuma? wayeshi to?" Zahrah tayi masa duka waÆ´annan tambayoyin cike da son jin amsa, haÉ—i da kuma mamaki, gani take kamar mutumin baida cikakken hankali.

Murmushi kawai ɗan aiken yayi haɗe da sake miƙo mata makullin motar  yace
"Kiyi haƙuri bai bani damar sanar miki dashi ɗin kowaye ba, amma yace dan Allah ki karɓa"

Ta buÉ—e baki zatayi magana kenan motar Dr.Sadeeq ta kutso kai cikin gidan.
Kasa cewa komai tayi har Dr.Sadeeq yafito daga cikin motarsa, ya ƙaraso garesu,  kallonsa Zahrah tayi shima kallonta yakeyi. 

"Hajiya ga makullin ni zan wuce" wannan mutumin yafaɗi haka, yana sake miƙa mata ɗan makulli.

"Ko ma waye ya aikoka, kace masa banaso, don bana buƙata" tafaɗi haka tare da juyawa daniyar komawa inda ta fito.

"Zahrah!"

Sunanta da Dr.Sadeeq yaƙirane yasanyata tsayawa cak haɗe da juyowa tana kallonsa.

"Zoki amsa, ki kuma yi masa godiya" Dr.Sadeeq yafaÉ—i haka, yana me karantar yanayinta.

Cike da mamaki tace "Amma..."  

"Banaso kice komai ki amsa kawai nace" yakatseta daga maganar da take ƙoƙarin yi.

Jiki asanyaye ta karɓi makullin motar.
Ciki ciki tace "Kace nagode"

   "To" kawai ɗan aiken yace kana ya juya yafice daga cikin gidan.

"Wai meke faruwa ne, waye ya aikosa?" Aunty Raliya ta tambayi doctor, don ta lura kamar yana da masaniya akan wanda ya aiko motar da cikinta ke shaƙe da kaya.

Murmushi Doctor yayi haÉ—e da cewa "wani aminina ne dake zaune a Dubai, shine dana gaya masa ta haihu yayi mata wannan kyautar"

Dafe ƙirji Aunty Raliya tayi tare da cewa
"Lallai wannan koma wayeshi yanaji da naira,  wannan motarfa zatakai 4million inma bata fi ba, ga kuma kayan dake cikinta, wanda suma kaɗai sun haura 1m, me kenan yake nufi?"

"Babu wani abun da yake nufi Aunty, haka dama shi yake kyautarsa, muje ciki ko" yaƙare maganar yana kallon Zahrah wacce ta daskare a wajen. 

Cike da mamakin kyautar abokin Doctor ɗin Aunty Raliya taja ƙafanta takoma falon Hajiya,  Zahrah ma jikinta a sanyaye tabi bayanta, shima falon yanufa, yanda yaga tana tafiya asanyaye ne yasanyasa yin murmushi kawai.
Bata tsaya a falon ba direct ɗakin dayake masauƙinta ta wuce, tsayawa tayi a gaban mirror zuciyarta cike da tarin tambayoyi  kala kala, sam bataji zuciyarta ta aminta da kyautar nan da'akayi mata ba, kwata kwata  batama yarda cewa wai abokin Doctor bane ya bata.  Tana acikin tunanin, yaturo ƙofar ɗakin yashigo bakinsa ɗauke da sallama.

Amsa masa sallaman nasa tayi haÉ—e da zuba masa idanunta, dagani kai kasan tambayoyine cike a bakinta.

takowa yayi ya ƙaraso daf da ita, hanunsa yasanya ya jawota jikinsa, saida yashaƙi daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta, ya sauƙe ajiyar zuciya, kana yace.

"Kinyi kyau sosai"

Murmushi ta ƙaƙalo haɗe da cewa.   "Nagode"

Cikinsa yashafa  tare da cewa. "Yunwa nakeji sosai, nayi missing sweet cook ɗinki, please ko zaki kawomin abinci?"

"Meyasa kake barin kanka da yunwa? kasan banaso, yanzu me zakaci na kawo ma?" tatambayeshi cike da kulawa.

"Koma me idan kika kawomin ni mai iya ci ne" yafaÉ—i haka yana me zama a bakin gado.

Harta kusa fita daga cikin ɗakin sai kuma  ta tsaya cak,  haɗe da juyowa, idanunsu yafaɗa cikin na juna, domin dama shima kallonta yake.

"Waye ne yaturomin da mota? Nasan kasan ko waye, domin zuciyata tafaɗamin cewa,  ba abokinka bane ya turo, kamar yanda kafaɗa a baya" tambayar da tayi masa kenan, cike da burin samun amsa agareshi.

"Baki yarda da abun dana faɗa ba kenan?"   ya tambayeta yana me ƙara tsareta da manyan idanunsa.

Murya a sanyaye tace "Kayi haƙuri, bawai ina nufin kamin ƙarya bane, kawai dai naji zuciyata ce bata gamsu da amsar da ka bayar ga Aunty Raliya ba"

Murmushi yayi haÉ—e da cewa "Zuciyarki tafaÉ—a miki gaskiya, domin kuwa ba abokina bane yaturo kamar yanda na faÉ—a a baya"

Waro idanunta tayi, duk da zuciyarta ta raya mata cewa ba abokinnasa bane, amma kuma duk da haka bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba.

"Waye?" tatambaya murya na rawa.

"ZAID" yabata amsa ataƙaice...

  
(Nagaji kuyi manage, idan nasha ruwa zan É—ora daga inda na tsaya)

      *29/February/2020/*

 
*✔️OTE ME ON WATTPAD*
          @fatymasardauna

#Love
#Romance

#One Love My Wattpadians
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

    *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

         *WATTPAD*
  @fatymasardauna

     *Chapter 116*

"ZAID!" ta maimaita sunan abakinta cike da tsananin mamaki.

Yanda yaga jikinta na ɓari shine abun daya basa mamaki, zallan tsoro ya hango kwance akan fuskarta, yayinda cikin idanunta kuwa, suka bayyana soyayyar dake kwance acikinsu, wato soyayyar ZAID, shi yasani ba tun yauba, bakuma zai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah na son Zaid, so ba irin na wasaba, so matsananci, amma kuma babu yanda zaiyi, dayana da iko to daya cire mata son Zaid acikin zuciyarta, amma wannan banasa bane, na Allah Ne, yasan Zahrah tana sonsa, amma soyayyar da takewa Zaid ta dabance,  da ace zai iya, to daya danne zuciyarsa, ya miƙata ga Zaid, yasan hakan zai samarmusu da farinciki, ita da Zaid, amma kuma yasan koda yayi hakan to ba mafita bane, domin ayanzu yasan dole idan baya tare da Zahrah tayi kewarsa, yana sane da cewa yakafa mata tutar son sa, wanda bazata ankara da hakan ba, har sai randa yazama baya tare da'ita, baya fatan wata ƙaddara ta rabasu, amma yasani ko mai daren daɗewa sai sun rabu, saboda akwai mutuwa, koshi ko ita, watarana ɗaya dole zai bar ɗaya, yau idan baya raye, baya fata Zahrah ta auri wani namiji idan ba Zaid ba,  tunaninsa yayi nisa, baisan da cewa ta ƙaraso inda yake ba, saida yaga ta zube a gabansa, tana kuka, cikin muryar kukan takecewa.

"Kada kamin haka doctor, wallahi ni banason duk wata kyauta da zatafito daga garesa,  namantasa acikin rayuwata, banaso kuma nasake tunasa, kamayar masa da kyautarsa, bana buƙata farincikin da kake bani kaɗai ya isheni"

Tunda tafara maganan yake kallonta,  ajiyar zuciya yayi, haɗe da kamo hannayenta, cikin murya me sanyi yace.  "Kinsani bakyau maida hanun kyauta baya, meyasa to zakiyi haka? mekike tunani akan Zaid?" ɗan dakatawa da maganar yayi, tare dayin wani murmushi, kana ya miƙe tsaye, daga zaunen da yake.
 
"Kyautace kawai ya miki, ai atunanina hakan ba wai yana nufin wani abubane,  bazan tilasta miki ba, amma nasan abundake cikin zuciyarki, don gashi har a idanunki sun nuna, so ba ƙarya bane Zahrah,  haka kuma ba laifi bane, don zuciya na dakon so, wannan ma wata ƙaddarace, wanda babu wani wanda ya isa ya kauce mata"  yanakai ƙarshen zancen nasa yanufi hanyar fita daga ɗakin.

Da sauri taje ta faɗa jikinsa, kuka take sosai, durƙusawa tayi haɗe  da zube  guiwowinta a ƙasa, kana ta riƙe rigarsa, kanta tashiga girgizawa, tana kuka tace.    "A da na sosa fiye da yanda naso kaina, amma ayanzu baya acikin zuciyata kamar yanda kake tunani,  Inasonka da duka zuciyata, bana fatan wata ƙaddara tazo wacce zata rabani dakai, kabani farinciki, kajiyar dani daɗi, kashayar dani zuman soyayyarka, bazan iya watsa maka ƙasa idanunka ba, kai mijinane wanda bayan kai bani da wani tamkarka,   nasan kai ɗin me sonane, amma meyasa kayi haka? mai yasa kai da kanka, zaka amince da na karɓi kyautar wanda yazama silar rugujewar rayuwata?"

Durƙusawa yayi agabanta, haɗe da sanya hanunsa ya share mata hawayen dake gudu akan fuskarta, cike da kulawa yace.   "Banason kukanki Zahrah, keɗin wata babban jigo kuma mahaɗi ne acikin rayuwata,  nasan Zaid ya cutar da rayuwarki, amma kuma hakan bazai hana ki amshi kyautarsa ba, ayanzu kowa yasan cewa ke matatace, saboda haka Zaid bazaiyi miki kyauta da wata manufa ba, kuma kafun ya miki kyautar saida ya tambayi amincewata tukunna, nakuma amince masa,  nayarda da Zaid Zahrah, nasan idan duka mutanen duniya zasu taru su cutar dake, to Zaid bazaiyi hakan ba, haka kuma idan ni zan iya cutar dake, to ina tabbatar miki idan Zaid yasan da hakan, to  bazai bari na cutar dake ba, Zaid ɗin da kikasani ada bashine wanda yake a yanzu ba, kada kiyi tunanin wai ko zanji haushi akan kyautar da Zaid yayi miki, niba jahili bane Zahrah, haka kuma halina ya banbanta da na wasu mazan, ni mutum ne me saurin fahimta, sannan kuma abune mawuyaci nayiwa wani na mummunan zato,  agurin wasu mazan, hakan zai iya zama matsala, amma a wajena hakan ba komai bane, tunda nasan cewa keɗin tawace ni kaɗai, bakuma wai don bana kishinki bane yasa hakan tafaru ba a'a, ni kalan nawa kishin ba irin na wasu bane,  inakishinki sosai, sai dai kuma kome acikin nutsuwa nakeyinsa, ke kinsan inasonki ina kuma kishinki " yaƙare maganar yana me lakace mata dogon hancinta.

Kukane yakuma ƙwace mata sai kawai tafaɗa jikinsa, ta rungumesa ƙam, shima rungumeta yayi yana shafa bayanta ahankali, haɗe da hura mata iskan bakinsa, acikin kunnenta.
Saida tayi kukanta sosai, kafun ta soma sauƙe ajiyar zuciya,  cikin murya me sanyi tace.
"Kai na da banne Mijina, irinka basu da yawa acikin duniya, haƙiƙa nafi kowacce mace sa'a dana sameka,  dakai kaɗai zan rayu har izuwa mutuwa ta, kaima ka rayu dani ni kaɗai kaji, bazan iya jure ganinka da wata mace ba bayanni, Ina maka son da bansan iyakarsa ba!"

Murmushinsa dake ƙara masa kyau yayi, haɗe da sanya iskan bakinsa ya hura mata fuska.

"Dake kaɗai Zan rayu Zahrah na, ni nakine ke kaɗai,  amma idan kina kukan nan fa, dole zan ɗan yi ƙasa da idanuna, na hango wata, saina kawota ko wanke wanke ne tanayi mana ko, idan dare yayi kuma sai ina raba muku kwana ko..."

Bata bari yakai ƙarshen zancen nasa ba, ta muntsine sa aciki, saida yasaki wata ƴar ƙaramar ƙara,   cike da shagwaɓa tace "Wallahi nidai babu ruwana dakai, idan dai har kace zakamin kishiya!"

Dariya yayi sosai haɗe da cusa kansa acikin ƙirjinta.  "Ni na isa ma nayiwa ƴar sakalalliyar matata kishiya,  amma bandai saniba wataƙila idan naga kin tsofe na miki!" yanzuma cikin zolaya yayi maganar.
Chapter 107 · 0% Book details