Sashe 57
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai ana ƙiran Zahrah a waje" yaron yafaɗa yana me kallon Zahrah domin kuwa yasan cewa itace wacce aka aikosa yayi ƙiranta..
Sai alokacin Zahrah taɗago kanta ta kalli yaron, haka nan taji gabanta yafaɗi, to waye kenan yake sallama da'ita? ta tambayi kanta, wayarta dake kusa da'ita ta ɗauka haɗe da dubawa, 1 missed call tagani na Dr.Sadeeq, dayake wayartata a silent tasanyata shi yasa bataji ƙiran nasa ba, kenan shine yazo yaƙira wayarta bata ɗauka ba shiasa yaturo yaro.  "Jekace inazuwa" ta bawa yaron amsa a taƙaice..
Miƙewa tayi haɗe da tattara takardunta tayi ɗaki. Mayafi taɗauka  ta yafa akan kayan dake jikinta...
Tsaye yake ajikin motarsa yayinda yakifa kansa asaman motar yana me kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa..
Kanta a Æ™asa tafito daga cikin gidan tana me duba wayar dake hanunta. Tsayawa tayi cak bayan ta haÉ—e wani miyau dayazo me É—aci ya maÆ™ale mata a maÆ™oshinta.Â
Murmushi yasakarmata haÉ—e da soma takowa zuwa gareta..
Lokaci É—aya idanun Zahrah suka sauya kala daga fari zuwa ja, juyawa tayi a fusace tanufi hanyar shiga gida, da sauri Zaid yasha gabanta haÉ—e da marairaice fuska cike da tashin hankali yasoma cewa....
"Dan Allah Zahrah kitsaya ki saurareni, dan Allah kada kimin haka Zahrah, inaso ki saurare....." kasa ƙare maganar nasa yayi sakamakon kyakkyawan marin da Zahrah ta shimfiɗa masa akan kyakkyawar fuskarsa...
Cikin ƙuna da kuma zafin zuciya   haɗi da raɗaɗi Zahrah ta haɗa yatsanta na tsakiya dakuma babbar yatsarta, ta kaɗa ade de fuskar Zaid duk da kuwa cewa yakerema tsayinta..
"Natsaneka tsana mafi muni, natsani jin kowani irin kalma ce da zata fito daga bakinka, wlh wlh nayi rantsuwa sau biyu, idan har ka sake naƙara ganin fuskar ka to zanyi maka abun da baka taɓa tunani ba!" cikin matsanancin ɓacin rai taƙare maganar tana me raɓan gefensa zata wuce, Zaid da zuciyarsa tariga da ta karye baiyi ƙasa a guiwa ba yasake shan gabanta.
"Kimin duk abun da kikeso Zahrah, zanfi jin daɗima idan akace kece zakiyi silan mutuwa ta, dan Allah ki saurareni mana Zahrah!!" yaƙare maganar cikin rawan murya...
Kuka ne ya ƙwacewa Zahrah me tsanani cikin muryan kukan tasoma cewa.....
"Miye laifina Zaid? Menene aibuna? shin wani abu na aikata maka da ka zaɓi cutar da rayuwata? ashe de ganganci ne don na ɗau soyayyata na baka? me yasa ka yaudareni Zaid? meyasa dole saini kazaɓi ka tozarta? Kacutar da rayuwata ka dasamin ƙunci a cikin zuciyata, wlh natsaneka Zaid, Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mezaka amfana dashi acikin rayuwarka? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci? Natsaneka Zaid! Natsaneka!! Bana fata Allah yaƙara haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada! Dan Allah kafita a rayuwata Zaid!!!" cikin matsanancin kuka taƙare maganar tana me durƙushewa ƙasa domin kuwa zuwa yanzu tsayuwa ya gagarewa ƙafafunta...
Idanun Zaid ne suka kaɗa suka zama jajur dasu tamkar wanda aka zuba musu jan barkono.  gaba ɗaya jikinsane yasoma ɓari, shi ɗin ma durƙusawa yayi agabanta cikin murya me tsananin rauni yaƙira sunanta,, saurin ɗaga masa hanu Zahrah tayi alaman batason jin komai daga garesa..
"Banason nasake koda jin muryarkane Zaid, kafita a rayuwata, wai mekake nema dani ne? ko kana tunanin zan sake aminta da kai ne? hmmm kayi babban kuskure Zaid idan kuwa har haka kake tunani, zaifi maka kyau, kamanta dani kakuma manta da wacece ni, ni na barwa Allah cutarwan da kayi agareni, kuma insha Allah nasan zai É—aukarmin fansa,, sai de inaso kasani cewa har abada bazan taÉ“a yafe maka ba, inaso kuma kada kamanta da cewar natsaneka !" a fusace ta faÉ—a cikin gida haÉ—e da banko Æ™ofar gidan nasu.Â
Tashi yayi daga durƙuson da yake haɗe da bin bayanta da kallo, gaba ɗaya zuciyarsa tagama karaya, wani irin abu yakeji ajikinsa yayinda kansa yayi masa wani irin masifaffen nauyi, zafi yakeji azuciyarsa irin sosai ɗin nan.
Zahrah kuwa zamewa tayi jikin ƙofar gidan nasu tasaki wani irin kuka me tsuma zuciya. Se yaushene zata warke daga raɗaɗi dakuma ciwon abun da Zaid yayi mata?  ganinsa yasake tasomata da mikin daya ƙi warkewa tsawon lokaci acikin zuciyarta, maiyasa Zaid yazame mata bala'i acikin rayuwarta? kuka tashiga yi sosai da sosai...
Zaid kuwa daƙyar ya iya jan ƙafafunsa yanufi motarsa, kasa tuƙa motar tasa yayi, gaba ɗaya idanunsa duhu suke gane masa, tabbas bazai taɓa iya tuƙa mota yana a irin wan nan halin ba,, da ƙyar ya'iya laluɓa wayarsa yaƙira driver'nsa... Mintuna kaɗan drivern Zaid yazo ya wuce dashi....
Saida tayi kukanta son ranta har sai da taji kanta yasoma ciwo kafun ta tsagaita, haɗe da miƙewa daga jikin ƙofar tashige cikin gida, direct ɗakinta ta wuce ta kwanta numfarfashi kawai take sauƙewa, lokaci ɗaya zazzaɓi yarufeta, harsaida tajawo mayafi ta lulluɓi jikinta....
Sanda yashiga falonsa ko gani bayayi sosai, wani irin ciwo kansa ke masa me tsanani wanda yasanya idanunsa sukayi nauyi, da ƙyar ya'iya jan ƙafansa yashiga ɗaki, kalaman Zahrah ne sukeyi masa yawo acikin kansa,, yatsani jin kalmar tatsaneshi da take yawan faɗa ɗin nan, wlhy a gurinshi da ta faɗi wan nan kalman gwamma ta sharara masa maruka koda kuwa guda biyarne akan ƙuncinsa..   Ya yanke shawara da de yakasance a irin wan nan yanayin ya gwammace yafita daga cikin hayyacinsa idan yaso bayan wasu tsawon lokaci yadawo cikin hayyacin nasa,, wasu ƙwayoyin magani yaɗauko harkala biyu, wanda suke gusarwa mutum da hankalinsa, maganin suna da hatsari sosai hakan nema yasanya ba'a sai dasu a bayyane sai de a ɓoye, kuma suna mugun sa bacci sosai...  Saida ya ɓalli guda uku uku daga jikin kowani sachet, kafun ya watsa maganin cikin bakinsa, wan nan karon ko ruwa baisha ba haka ya haɗiye magungunan, yanda kalaman Zahrah ke dawowa cikin kunnensa yafi komai ɗaga masa hankali, kwanciya yayi lamo akan gado yayinda yake ƙwato numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwace masa da ƙyar. wani irin fusga numfashinsa yayi lokaci ɗaya kuma komai najikinsa ya sake...
Zahrah kuwa zazzaɓine ya dirarmata me zafin gaske, wanda yasanya lokaci ɗaya jikinta yasoma ɓari ta fara rawan ɗari, har zuwa yanzu hawayenta bai tsaya ba. Zaid ya cuceta itakam duk irin ƙuncin daya jefata a baya bai ishe saba saida yakuma da wowa gareta, sai yaushene hawayenta zasu tsaya? sai yaushene zata samu farinciki ingantacce wanda babu algus acikinsa? tunda ta haɗu da Zaid ƙuncin rayuwarta yasoma, wani irin annoba Zaid yazame mata ne?.....
*(Kuyi haƙuri kuyi manage da wan nan, headache ke damuna, nida Zaid duk cutarmu ɗaya😜 banyi posting da wuri ba wlh network ɗin sim ɗi nane gaba ɗaya ya ɗauke😥)*
  *29/December/2019*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
    *SHU'UMIN NAMIJI !!*
Â
   *Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
     *WATTPAD*
  @fatymasardauna
*(💗Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareku my wattpadi'ans inagodiya sosai a gareku💗)*
*Editing is not allowed📵*
 Â
   *CHAPTER 72 to 73*
Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haɗe da ɓata fuskarta duk wai akan don Mom ɗinsu tace taƙira mata Zaid a ɓangarensa ne yasa take wan nan abun...
"Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki ƙiramin yayanki ba!" Mom tafaɗi haka cike da faɗa, ganin Labisat ɗin bata da niyar zuwa aiken datayi mata.
"Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!" Labisat tafaÉ—i haka cikin shagwaÉ“a.Â
Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon...
Aranta kuwa roƙon Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faɗa baya masa kaɗan ko kaɗan, jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haɗata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya😂)
Kusan sau huɗu Labisat tana knocking ƙofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura ƙofar tashiga,,  bakowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshinsa dake tashi.. Direct ƙofar bedroom ɗinsa tanufa haɗe da soma knocking ƙofar,, jin shiru ne yasanya tashiga ƙiran sunan sa...
"Brother! Brother!"Â ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin É—akin ko baya ciki ba..
Gajiya tayi da knocking ƙofar ta juya tayi tafiyarta...
"Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door É—insa amma bai amsa ba"
"Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita ba, miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin ƙyaliya ba" Mom tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take..
Itama ɗin de knocking tayi masa haɗe da ƙiran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta kutsa kanta ciki bakinta ɗauke da sallama..
Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..
"Zaid!" taƙira sunansa cikin kakkausar murya... Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..
Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma'abocin yawan bacci ba'a bisa ƙa'ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa ɗayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan ƙwayoyi, "Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?" tajeromawa kanta waƴan nan tambayoyin, "Haƙiƙa Zaid ɗanta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa ƙa burgesa ba yanada wani shegen shu'umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi"...
A hankali tashiga takawa zuwa gaban gadon nasa..