← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 112

Sashe 102

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta yayi da jajayen idanunsa haÉ—e da tashi, kawai yawuce cikin bathroom.
"Afrah bazata taɓa ganewa bane, shi kaɗai yasan irin zogi da kuma ciwon da zuciyarsa keyi masa, aduk sanda aka ambato masa sunan Zahrah,  a yanzu so yake yasa aransa cewa, babu wata Zahrah, domin wacce yasani tajima da mutuwa, wanda yake gani a yanzu, wata Zahrah'nce daban kuma ta wani ce"  tsaida zancen zucin nasa yayi,  haɗe da cire rigar dake  jikinsa, direct gaban shower ya nufa, tsayawa yayi haɗe da sanya hanunsa  ɗaya, ya dafa jikin bango, ruwane keta dukan kansa dakuma bayansa, sauda dama idan yana acikin ƙunci, tsayawa yake gaban shower ruwa yaita dukansa, dahaka yake ɗan samun relief.

*** ***

Kwance take akan kujera, sanye take da wani dogon sket, wanda yake a tsuke daga sama har ƙasansa,   sket ɗin  irin roba ɗinnnan ne,  rigarta kuwa wata ƴar vest ce marar nauyi, fara ƙal da ita, tunda ta samu cikin nan, bata rabo dajin zafi, hakan yasanya bata cika zama da kaya masu nauyi ba,  wayartace rike a hanunta, kunnenta kuwa sanye suke duka da airpiece, waƙar film ɗin Sanam Teri Kasam takeji, harwani lumshe ido take, saboda tanason waƙoƙin film ɗin sosai,   sweet ne abakinta tana ɗan tsotsa, gudun tara yawu, dayake bata ƙure volume ɗin waƙarba, hakan yasanya tajiyo bugun ƙofar da akeyi mata,   da mamaki take kallon ƙofar falon, ita dai tasan batayi da kowa cewa yau zaizo wajenta ba, kuma yanzu ba lokacin dawowan Doctor bane, batajin zata iya tashi dan haka saita bawa me knocking door ɗin damar shigowa kai tsaye.

Da sallama ɗauke a bakinta, tashigo cikin falon.  Kallon kallo suka shigayiwa juna ita da Zahrah,  ita tana kallon Zahrah ne fuska ɗauke da murmushi, yayinda  Zahrah kuwa ke ƙare mata kallo, saboda batasanta ba ma ita kwata kwata.

"Da dai anbani izinin shigowa, aida sai na shigo" takatse Zahrah daga kallon da take mata, ta hanyar faÉ—an haka.

Murmushi Zahrah tayi haÉ—e da tashi zaune tace "Bismillah, shigo"

Ƙarasowa tayi tsakiyar falon, haɗe da zama akan kujera.

"Sannu da gida" tace tana murmushi.

"Yauwa sannunki da zuwa" Zahrah tafaɗi haka itama tana murmushi.    Miƙewa tayi da niyar takawo mata ruwa da lemo, da sauri tace. "A'a barshima basai kinkawomin komai ba, daga gida nake banajin ƙishi"
Kallonta kawai Zahrah tayi kana ta koma kan kujera ta zauna, cike da ƙosawa Zahrah tace.  "Baiwar Allah Bangane wace ke ba fa"

Murmushi takumayi akaro na barkatai.   "Sunana Afrah, dama nasan baki sanniba, amma ni nasanki, kiyi haƙuri bansaniba ko hakan danayi yaɓata miki rai, jiya naganki a hotel kinacin abinci keda wani, wanda nake kyautata zaton cewa mijinki ne, tunda naganki, naji kin kwantamin arai, kuma wallahi da zuciya ɗaya nake sonki, please idan bazan takuraki ba, inaso muzama ƙawayen juna"

Murmushi Zahrah tayi me sauti, haɗe da cewa "Nagode ƙwarai da ƙauna, amma kuma inaganin kamar akwai matsala, idan har muka fara ƙawance yanzu, dududu fa yau nafara ganinki, kinga dole kafun abota musan halin juna" inji cewar Zahrah.

"Da alamu bakida wata matsala nima kuma haka, kuma insha Allah bazakiyi danasanin ƙawancen mu ba"   taƙara da cewa "Akan hanya nake, watarana zanyi miki zuwa na musamman amma kafun nan,please samin number'n wayarki" miƙawa Zahrah wayarta da ta cirota cikin jaka tayi.
Babu musu Zahrah ta amshi wayar tasanya mata number'nta aciki, kana ta miƙa mata abarta.
Murmushi tayi haɗe da miƙewa tsaye, "nagode sosai" tace kana ta nufi hanyar fita daga cikin falon, Zahrah na ganin ficewarta ta sauƙe ajiyar zuciya, haɗe da komawa ta kwanta, aranta tana addu'an neman tsari daga sharrin mugayen mutane, da kuma aljanu....

*** *** ***

Gaba ɗaya yau tatashi jikinta arikice, ganin haka yasa Dr.Sadeeq hana kansa zuwa office, yazauna tare da ita, yanata amsar shagwaɓanta, zuwa yanzu sosai shagwaɓanta yafi na da, tun da tasamu cikin wani sakalci da taɓara ya tsiro mata,  shikuwa doctor biye mata yake, hakan yasa gaba ɗaya yanzu tazama wata, shagwaɓaɓɓiya da ita sai kace ƴar shekara 4.
Kwance take akan sofa yayinda kanta ke É—aure bisa cinyarsa, minti irin me tsinkenan ne abakinta, tana tsotsa a hankali, yayinda shikuwa ke shafa sumar kanta a hankali.
_______

Mamakine ya matuƙar kashesa, ganin unguwa da kuma inda Afrah ta kawosa, ɗago idanunsa yayi ya watsamata su, "Inane nan?" yatambayeta still idanunsa na kanta.

Murmushi tayi masa haɗe da cewa "Unguwar su ƙawartawa da nake gaya maka ne, kuma ganan ma gidan nata" taƙare maganar tanayi masa nuni da gidan dake gefensu,   bugawar zuciyarsa ne ya ƙara tsananta,  take yaji kansa nayi masa wani irin sarawa.

"Kimaidani gida Afrah, tunkafun ranki ya ɓaci!" cikin yanayi na ɓacin rai yake maganar.

Dama tasan za ayi haka,  hanunta ta ɗaura akan nasa cikin son ta rarrasheshi tace "Kayi haƙuri Dear, bazamu wuce 30 minute ba, nasan kasan gidan, kakuma san wacece acikin gidan, banyi haka donna ɓata maka ba, nayi hakane don kawai kasamu salama, ƙwarai nasan idan harta yafema kuma ayau idan kuka ga juna, tabbas komai zai wuce, duk da nasan sai ahankali, amma kuma dukanku zaku samu sassauci...."

"Kimaidani gida nace kona ɓaɓɓala ƙashinki gida biyu anan wajen!!" amatuƙar hasale yaƙare maganar.
Saida ta tsorita domin bata tsammaci wannan tsawan daga gareshi ba.  

"Fita" yace da ita murya a dake.
Sumi sumi ta fice acikin motar, dan ta fuskanci sam babu alamar wasa a tattare dashi. Fita shima yayi daga cikin motar ya koma wajen zaman driver domin dama a wajen mai zaman banza yake dazama, itakuma tana wajen zaman driver.

Yana shiga yatada motar, kallon  Afrah yayi fuska babu walwala, da sauri ta buɗe motar tashiga, da ƙarfi yaja motar sukabar ƙofar gidan.

Suna zuwa gida, ya wuce ɗakinsa kai tsaye, itama Afrah tayi nata ɗakin,  sam bataso haka yakasance ba, taso ace  abun da ta ƙudurta aranta shine ya faru.

Kayansa yashiga haɗawa acikin trolly ɗinsa, saida yatabbatar ya haɗa duk wani abun da yake buƙata,  dama kuma jiya aka kawo masa visa'n su.

Tana tsaye agaban mirror daga ita sai wata ƴar fingilan riga, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa,  akwatinta ya ciro acikin drawer, kallonta yayi itaɗinma kallonsa take.

"Kishirya kayanki, 6 pm zamu tashi gobe insha Allah" yanakaiwa nan azancensa yasakai yafice daga cikin É—akin.

Mamakine yakama Afrah,  "dama ya shirya musu tafiya shine baisanar da'ita ba?" tambayar da tayiwa kanta kenan,  ganin bata da wani wadataccen lokaci yasanya, tashiga shirya kayanta acikin trolly'n, da ya fito mata dashi. 

Zama yayi akan gado haɗe da jawo diary ɗinsa ya buɗe, abun rubutu ya ɗauka yaɗanyi rubutu, kaɗan kana ya rufe diary'nnasa ya  tura acikin wata ƴar ƙaramar jaka.

Washe gari

Kamar yanda ya faɗa ƙarfe 6 dai dai jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar America, a wannan karon baya tunanin zai waiwayo Nigeria, so yake ya koma America da zama gaba ɗaya,  wannan shine ƙudurinsa, sai dai idan Afrah tace zatazo  Nigeria bazai hanata ba, shikam dai yasa aransa cewa bazai zoba, saidai ko wani babban dalili, me ƙarfi.

***   *** ***

Abuja University Gwagwalada.

Yau suke bikin kammala degree ɗinsu, saboda haka gaba ɗayansu sunacikin farinciki.   Kowannensu yasha adonsa cikin shiga ta burgewa gwanin ban sha'awa.

Tsaye take ajikin wata bishiya tana waya,  sanye take da baƙar tie abaya gown ajikinta, wacce daga hanunta zuwa ƙasanta aka mamayeta da ado na flowers masu kyaun gaske.   Da babban mayafi tayi amfani wajen rufe jikinta, sai dai kuma duk da haka, saida cikinta ya bayyana kansa, sosai taƙara haske da kuma kyau, sai wani ɗaukar ido take, daganinta kaga me ciki, wacce take cikin jin daɗin,  yanzu watannin cikinta huɗu kenan amma kuma tuni ya bayyana kansa, ita kanta har mamakin girman cikin nata take, don watanninsa basukai ace girmansa yakai  har  haka ba.

"Zakizo mu kammala pictures ɗinne kokuma zaki tsaya soyewa"   Husnah dake tahowa ga Zahrah tafaɗi haka da ɗan ƙarfi. tayanda Zahrah'n zata jita.
Murmushi Zahrah tayi haÉ—e da kashe wayar, kana ta juyo da kallonta ga Husnah.

"Kinsan banagajiya da jin muryarsa ne, amma muje mukammala agurguje, saboda gida nakeson nakoma gaba ɗaya jina nake agajiye" Zahrah ta  faɗi haka tana ɗan yamutsa fuskarta.
Murmushi Husnah tayi haÉ—e da cewa "Nima sauri nake saboda yau Man É—ina zai turo magabatansa gidanmu, kuma ayau za'a sa mana ranan aurenmu, nasankuma baza asa ranan da yawa ba, just ba zai wuce 1 month ba"

Dariya Zahrah tayi haÉ—e da cewa "Lallai Husnah aure kikeso sosai, ji yanda lokaci É—aya kika falle."

Dariya sosai Husnah tayi haɗi da cewa "Laifine dan mace irina taso aure? nakai aure, nakuma cika mace me lafiya, kinga kuwa dole naso aure, ke nifa wallahi gaba ɗaya yanzu rayuwata, a daddafe nakeyinta, na ƙosa najini a ƙirjin mutumin, nima yakasheni da irin nasa salon" cikin yanayi na shauƙi ta ƙare zancen.

Dariya dukansu sukayi  kana suka tafa.
Basu tsaya an kammala bikin dasu ba, kowaccensu ta nufi gida.

(Kuyi haƙuri, wallahi kwana biu narasa ganewa kainane, gaba ɗaya typing yafita araina, kuma kunsan abun yana aiki ne da zuciya dakuma ƙwaƙwalwa, wallahi dana fara kaina sai yanamin ciwo,  saboda haka dole zan taƙaita muku labarin, insha Allah acikin satinnan zan kammala littafin, duk da bahaka naso ba, amma kuma abubuwa sunmin yawa, ina buƙatar hutu kusan na 1 month, idan na bari kuma banƙarisa ba, zan shiga haƙƙin masu karatu, kuyi manage da wannan, yau ko editing banyi ba, saboda ciwon kae, dan Allah kumin uzuri kunji, duk na naƙosa nagama labarin, saboda haka zanci gaba dayi muku shi a gurguje.)

   *✔️OTE ME ON WATTPAD*
            @fatymasardauna

#Love
#Romance
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SHU'UMIN NAMIJI!!*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

   
             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*CHAPTER 113*

Kwance take akan gado, hanunta riƙe da littafin hausa, tana karantawa,  sanye take da doguwar riga irin bubu gown ɗinnan, zuwa yanzu cikinta ya ƙara girma, har tsoro girman ke bata, ga yawan motsin da takeji acikin cikin nata.
Chapter 102 · 0% Book details