Sashe 38
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙoƙari Mahmud yayi wajen tsaida dariyar tasa haɗe da gyara zama
"Yazama dole nayi maka dariya Sadeeq, a matsayinka na likita bokan turai, ka kasa jure zafin soyayya, amma kuma ko kaɗan banga laifinka ba, sai dai kuma, akwai ƙalubale a gabanka!" Mahmud yaƙare maganar yana mai waina pen ɗin dake riƙe a hanunsa.
"Wani irin ƙalubale kenan Mahmud?" Dr Sadeeq yatambaya cike da zaƙuwa, saboda shi mafita kawai yake nema.
"Nasara ko kuma akasinta, sune babban ƙalubalen da zaka fuskanta, amma ina mai maka fatan nasara, duk dacewa banganta ba, amma nasan tahaɗu sosai, saboda nasan abokina ya'iya zaɓe!" Mahmud yafaɗi hakan cike da barkwanci, wanda hakan kuma halinsa ne.
"Bazaka taɓa canjawa ba Mahmud, kai ko da yaushe idan ana magana mai amfani saikayi yanda kayi ka sako wasa a ciki." Dr Sadeeq yafaɗi hakan yana mai shafa suman kansa.
Ƴar ƙaramar dariya Mahmud yayi haɗe da ɗaukan cup ɗin juice ɗin dake gabansa yakai zuwa bakinsa.
"Babu amfanin ƙara tada zancen a gareta Sadeeq, tunda ta nuna maka bata sonka, inaganin kabata lokaci, ko ba komai zatayi tunani mai kyau, amma fa hakan danace bawai yana nufin kada kasake zuwa gareta bane, zaka iya zuwa gareta ako da yaushe, amma kada ka sake ɗago mata da zancen inaga haka zaifi!" Mahmud yafaɗi hakan cike da son ƙarfafamawa abokinsa guiwa.
Ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe, haɗe da haɗiyar yawu, sai yanzu yasomajin sanyi a cikin zuciyarsa, domin kuwa da gaba ɗaya kansa ne ya kulle.
"Zanyi yanda kace Mahmud, sai dai kuma inajiyewa kaina tsoro, kada a gaba taƙi amsata, sannan kuma yanzu bansan da wani ido zan kalle ta ba!" Dr Sadeeq ya faɗi haka cikin ɗar ɗar.
Dariya Mahmud yakuma kwashewa dashi a karo na biyu, lallai yayarda cewa so mugun abune, domin kuwa shi kaÉ—ai ke sa jarumi kuma gwarzon namiji acikin tsoro dakuma É—ar É—ar.
"Yanaga jikinka gaba ɗaya yaɗau rawa, kada dai kabani kunya, tsoronta kakeji tun yanzu, idan kuma akayi auren yaya kenan?" Mahmud yatambaya cike da shaƙiyanci.
Tsuka kawai Dr Sadeeq yakuma ja, haɗe da miƙewa tsaye, domin idan yabiye ta Mahmud to baƙin ciki sai ya cika masa zuciya, domin kuwa halin Mahmud ne tsokana da yawan barkwanci.
"Gwamma nayi tafiyata zaifi min, kayi dariyanka ka ƙoshi, ai nine nakawo kaina office ɗinka, kana da right ɗin da zaka iyamin komai" Dr Sadeeq yakare maganar yana mai gyara zaman suit ɗin dake jikinsa.
Ko sake sauraran Mahmud dake ta faman dariya baiyi ba, yayi ficewarsa daga office É—in Mahmud É—in.
Cikin ɗan kuzarin da yasamu yake tuƙa motar tasa, yanzu kam yagama aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa. Kai tsaye gida ya koma, wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wani haɗaɗɗen riga da wando na jeans masu kyaun gaske, sosai kayan sukai masa kyau a jiki, suka kuma fito da asalin kyawu da kwarjininsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turare. Makullin motarsa ya ɗauka haɗe dasakai yafice daga cikin ɗakin.
Zaune take akan ƴar katifarta, daga ita sai wata riga marar nauyi, jakan kayan shafanta ne aje a gabanta, da'alama daga wanka tafito, domin kuwa wani sashi na jikinta ɗauke yake da danshin ruwa.  Kallo ɗaya zakai mata kafuskanci irin ramar da tayi lokaci guda, gaba ɗaya ta zabge ta faɗa, hips da breast ɗin tane kawai suke a cike a jikinta. A hankali take shafa Vaseline ɗin dake riƙe a hanunta, Yanayin yanda take shafa vaseline ɗin idan ka gani, kace dole akai mata.  tana gama shafa mai ɗin, ta murza powder kaɗan akan fuskarta, haɗe da shafa kwalli a cikin idanunta, take fuskarta ta tasakeyin fayau, yayinda idanunta, suka sake bayyana girmansu a fili,kasancewar kwallin yana taimakawa wajen bayyana girman ido.
Kallonta tamayar kan É—an Æ™aramin agogon bangon dake É—akin nata, Æ™arfe 5 na yamma kenan, kuma dai dai lokacin sukayi da Husnah cewa zataje ta sameta a gida. Cikin rashin kuzari, ta miÆ™e haÉ—e da É—aukan kayanta riga da sket na atamfa tashiga sanyawa, duk da cewa atamfar mai sauÆ™in kuÉ—i ne, amma hakan baihana ta yi mata kyau a jikinta ba. Wani irin zazzaÉ“i takeji yana sanÉ—an jikin ta, idan ba don tariga da tamawa Husnah alÆ™awarin cewa zata zo yau É—in ba, to tabbas da ta É—age zuwa gidansu Husna'n saboda bata wani jin daÉ—in jikinta, takumasan cewa damuwace kurum tayi mata yawa.  Â
Inna ce tashigo cikin É—akin, adai dai sanda Zahrah ta gama sanya hijab É—inta.
"Au ashema kinsan da zuwansa kenan?" Inna tatambaya tana mai ƙarewa Zahrah kallo.
"Banganeba Inna, zuwan waye kuma?" Zahrah taje fawa Inna tambaya cikin rashin fahimtan inda kalaman Inna'n suka dosa.
"Naga kinshirya tsab kamar kinsan da zuwansa, to koma dai menene kije yanajiranki a waje!" Inna tafaɗi hakan tana mai ƙoƙarin barin ɗakin.
"Waye Inna? kuma ni shirin nan da kika ga nayi, gidansu Husnah zani, amma waye ke nemana ?" Zahrah takuma tambaya cike da son ƙarin bayani.
"Waye kuwa zaizo neman ki a yanda kike ɗinnan, ai sai dai shiɗin da har ya yarda zaiyi JIHADI ya aure ki a haka, amma wai saboda son zuciya da butulci irin naki, kike neman watsa masa ƙasa a idanu!" Inna taƙare maganar dai dai sanda tayificewarta daga cikin ɗakin.
Wasu irin siraran hawayene suka samu nasaran gangarowa daga cikin idanun Zahrah, tabbas gaskia Inna ta faɗa, babu wani mai nemanta sai shi ɗin shi kaɗai, kuma tabbas tayadda shima JIHADI yayi kamar yadda Inna tafaɗa, ashe dagaske ne itakam ƙaddaranta tayi mata mummunan zane a goshinta,  saurin share hawayenta tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin.
Tsaye yake a jikin motarsa yayinda kansa ke duƙe a ƙasa, ɗan makullin motarsa ce riƙe a hanunsa yana kaɗawa, wannan karon kam sosai yake yaƙi da zuciyarsa don bayaso tasake sanya masa tsoro kokuma ɗarɗar.
A hankali take taku cike da nutsuwa har ta ƙaraso garesa, ɗan nesa dashi ta tsaya haɗe da yimasa sallama cikin sassanyar muryarta wadda bata fita sosai.
Lumshe idanunsa yayi haÉ—i da buÉ—esu a lokaci guda, badon komai ba sai don yanda sassanyar muryarta ta daki jiki da zuciyarsa.
"ZAHRAH!" yaƙira sunanta cikin murya marar fidda ƙaƙƙarfan sauti.
"Um!" Zahrah ta amasa masa batare da ta'iya motsa bakinta ba, haka kuma kanta a duƙe yake tunda tazo bata'iya ɗaga kai ta kallesa ba.
Kallonta yashiga yi tundaga ƙasanta har sama, tabbas duk da cewa a cikin hijab take, amma hakan bai hanasa hango rahamar da tayi ba, take yaji zuciyarsa tayi sanyi, tausayinta yasake kamasa.
"Inaso kimini iso cikin gida, inaga maganar mu acan zaifi, domin ina buƙatar zama!" yafaɗa cike da ƙosawa da tsayuwan da yakeyi.
Sumi sumi haka ta juya ta nufi cikin gida, harta shige cikin gidan bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, "Wallahi Zahrah ta haɗu, komai nata mai kyau ne!" yafaɗi hakan a fili, cike kuma da shauƙin soyayya.
Jim kaɗan Zahrah tafito, tana mai wasa da yatsun hanunta, "Kashigo!" kawai ta'iya furtawa cikin murya mai sanyi. Tana gaba yana biye da'ita haka suka doshi cikin gidan.
Katuwar tabarma tabaje musu a hanyar zaure, yayinda ta je ta zauna a can ƙarshen tabarman ta takure waje ɗaya, tamkar amaryar da aka kaita ɗakin miji yau yau, lol.
Murmushi Dr Sadeeq yayi bayan yayimawa kansa mazauni,  dole dai shi zai ci gaba da zama jarumi ako da yaushe.
" Miye haka? ai ko da yanka naman jikin mutane nake, ya kamata ace kin matso kusa dani, balle ma kuma ni ba'abun da nakeyi, ko na taɓa miki wani abune ?" Dr yafaɗi hakan cike da kulawa.
Saurin É—ago da kanta tayi ta kallesa, domin yadawo mata asalin Likitan da tasani, kuma gaba É—aya ya sauya wasu É—abi'un nasa.
Giransa É—aya yaÉ—age sama, haÉ—e da cewa "Yadai, ko nayi wani sabon laifi ne akan wancan banda labari?"
Girgiza kanta tashiga yi ita kaɗai tamkar ƙadan garuwa, domin ita tama rasa maizata ce dashi domin kuwa da wani salon yadawo.
"Matso kusa dani mana!" yafaÉ—a cikin sanyin murya, mai É—auke da lallashi.
Cikin rashin kuzari, ta koma tsakiyar ta barman ta zauna, bayan ta haÉ—a jikinta duka ta takure waje É—aya.
Ajiyar zuciya Dr Sadeeq ya sauƙe haɗe da sanya hanunsa yashafi ƙasumbar dake kwance akan fuskarsa.
"Maiyasa zakisa kanki a damuwa Zahrah? yawan kuka dakuma yawan tunani marassa amfani, basa haifar da komai sai gajiyar da ƙwaƙwalwa, please banso kina wahalar da ƙwaƙwalwarki, nasan cewa abaya banine sila ba, amma yanzu nine sila.!" ɗanjim yayi kana yaci gaba da cewa..." Kiyi haƙuri Zahrah, nasan bankyauta ba, amma inaso kimanta komai, inaso ki fuskanci karatunki, ki maida hankali sosai kinji ƙanwata, bawanda zaimiki dole, ke mutumce kuma kowani ɗan adam yana da ƴanci, kema kina da ƴanci, saboda haka ki daina kuka kinji ƙanwar Likita!" Yanayin yanda yaƙare maganar kaɗai ya'isa yasanya zuciya hucewa daga cikin fushi.
Kuka kawai Zahrah ta fashe dashi mai sauti, domin kuwa sai yanzu nadaman abun da ta'aikata a garesa yadawo mata sabo fil. A hankali ta ɗago idanunta da suke ɗigan hawaye tamaida kallonta garesa,  wannan fuskar ta mara? ta tambayi kanta, tabbas batayiwa kanta adalci ba, Dr Sadeeq baicancan ci mari daga gareta ba. kukane yakuma ƙwace mata, don batasan tayanda zata soma basa haƙuri akan abun da tayi masa ba.
Cike da damuwa ya dawo kusa da'ita, har suna iya juyo ƙamshin turaren juna.
"Subahanallah Zahrah kuka kuma? kinfasan banaso, kidaina kuka kinji, ki faɗamin idan ganina ne bakiso, yanzu zantafi Zahrah, nazo ne dama nabaki haƙuri akan abun da yafaru tsakanina dake, kiyi haƙuri Zahrah haka bazata...." Kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon Zahrah da ta sanya duka hannayenta biyu ta toshe masa baki.
"Dan Allah kada ka ƙasƙantar da kanka awajen wacce bata dace ba, bata kuma cancanta ba, bakaine yakamata kabani haƙuri ba, nice yakamata na baka haƙuri, bai kyautu ace na mareka ba, nayi nadama Doctor, dan Allah kayi haƙuri, bansan yanda zanyi ba ne banda zaɓi, kayafemin!" Zahrah ta ƙare maganar cikin kuka, haɗe da karyewar zuciya.
Take yaji tausayinta yasake ninkuwa acikin zuciyarsa.
A hankali ya sanya hanu yazame hannayenta dake kan bakinsa, domin kuwa hakan da tayi masa har ya sanya tsikar jikinsa sun soma motsawa.
"Kinaso nayi haƙuri?" Dr yatambayeta.