← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 112

Sashe 4

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tafiya take tana kallon ƙasa, yayinda hannayenta ke naɗe akan ƙirjinta, da gudun gaske ya shawo kwanar saura ƙiris ya doketa, Allah ne kawai yasa tayi saurin matsawa gefe,, parking motar yayi haɗe da leƙo kansa waje ta window'n motar " Uh sorry Zahrah ina fata dai bantaka ki ba ?" ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa "A'a baka takani ba" wani irin shu'umin kallo yabita dashi haɗe da cewa "Ina zaki ne haka da tsakar rana ?" " Aika zani " Tabasa amsa a taƙaice,, "Okay shigo na rage miki hanya mana " yayi maganar yana mai yunƙurin buɗe mata murfin motar, "A'a kabarshi kawai nagode" bata jirayi mai zai ceba tasakai tayi tafiyarta,, murmushi kawai Bash yayi haɗe da figar motarsa yayi gaba.....

*Wacece Zahrah ?*

Malam Adamu Muhammad haifaffen ɗan jihar Yola ne, su biyu ne a wajen iyayensu shida ƙaninsa Hayatu, Malam Adamu yakasance mutum mai mutumci da kuma karamci, Matarsa ɗaya Zainab, Zainab, asalinta buzuwar Niger ce fatauci yashigo da mahaifanta Nigeria, Mahaifan Zainab dana Malam Adamu suna da kyakkyawan alaƙa kasancewarsu maƙotan juna, tun Zainab na ƙarama Allah yasanya mata soyayyar Malam Adamu acikin zuciyarta, kasancewarsa kyakkyawan bafulatani, duk da dai tafisa kyau nesa bakusa ba, cikin ikon Allah Zainab nakai lokacin daya kamata ace anyi mata aure, iyayenta suka Aura mata Malam Adamu, zama sukeyi na lafiya da ƙaunar juna,, watarana iyayen Zainab suka shirya don zuwa Niger, ahanyarsu ta zuwa sukai gamo da ƴan fashi, suka harɓesu, sosai Zainab tayi kukan rashin iyeyenta, da ƙyar dai Malam Adamu yasamu ya rarrasheta, akwana a tashi kwatsam ciki yabayyana ajikin Zainab, sosai sukayi murna da samun ƙaruwa da Allah yayi musu, cikin Zainab nada Wata Tara tahaifo kyakkyawar ɗiyarta mai matuƙar kama da ita, saidai ita ƴar harta ɗara Zainab a kyau duk da kuwa kyau irin na Zainab, anyi shagalin suna lafiya inda yarinya taci sunan mahaifiyar Zainab wato *FATIMA* ana ƙiranta da *ZAHRA* Zahrah tataso cikin gata da kulawar iyayenta, saidai muce masha Allah,, watarana ne Malam Adamu yatattara matarsa da ƴarsa suka koma garin Abuja da zama, cikin wata unguwa da'ake ƙira Suleja, yakama musu hayan wani ɗan ƙaramin gida,, sana'ar saida takalma Malam Adamu keyi, yana da ɗan teburinsa a nan yake kasa takalman roba da su silifas (slippers), cikin ikon Allah kuwa,Allah baya hanasa na abinci da kuma na ƴan biyan buƙatun da ba'a rasaba, Watarana Malam Adamu ya tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe a ƙasa, daya bincika kuɗin shine yataradda adireshi (Adress) na mai kuɗin acikin jakar daya tsinci kuɗin, a shema wanda ya wurgar da kuɗin, a nan gaba da unguwarsu kaɗan yake kuma yasanshi sunansa Alhaji Umar, Malam Adamu baiyi ƙasa a guiwa ba wajen kaimawa Alhaji Umar kuɗinsa, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗi sosai, nan yaɗauki maƙudan kuɗaɗe yabamawa Malam Adamu, amma Malam Adamu haka yaƙi karɓa acewarsa, shi don Allah yayi bawai don abiya saba, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗin hakan, haka dai Alhaji Umar da Malam Adamu suka soma zumunci, watarana Malam Adamu na zaune, Alhaji Umar yaƙirasa yace mai yasayamasa gida anan suleja, bakaɗan ba Malam Adamu yayi farinciki, har ƙwallan murna saida yayi, gidane daidai da zaman talaka Alhaji Umar yasai mawa Malam Adamu, ɗakuna huɗu ne acikin gidan sai ɗan madaidaicin filin tsakar gida, da kitchine da kuma makewayi, Koda Zainab tazo taga gidan itama taji daɗi sosai, bawani ɓata lokaci suka tattaro suka dawo gidan,, a kwana a tashi Asaran mai rai, wata rana aka wayi gari Baban Malam Adamu ya rasu, sosai mutuwar tajigata ƴaƴansa, amma babu yanda suka iya duk wani mai rai mamacine sunriga da sunyi imani da hakan,, bawani ɓatalokaci Malam Adamu ya ɗauko mamansa suka dawo garin Abuja da zama,, baifi wata uku da dawowar Goggo (Maman Malam Adamu) Abuja ba, tace ga garinku nan, Allah sarki su Malam Adamu sunkuma jin zafin rashin mahaifiyarsu,, bayan wani lokaci Hayatu yayi aure, Malam Adamu ne yace masa yadawo nan Abuja su zauna, tunda akwai ɗaki a gidansa, Hayatu bai ƙi ba, yaɗauko matarsa suka dawo,, tundaga kan Zahrah Malam Adamu da Zainab basu sake haihuwa ba, Zahrah tanada shekara huɗu Malam Adamu yasanyata amakarantar furamari (Primary) Zahrah yarinya ce mai hazaƙa sannan kanta yana ja sosai, kwanci tashi Zahrah ta kammala makarantar furamari (primary) ɗinta, bawani ɓata lokaci Malam Adamu yasama mata gurbin cigaba da karatu (Admission) a wata junior school dai dai da ƙarfinsa,, Zahrah na aji ɗaya a junior school, Mama (Zainab) takwanta rashin lafiya, abu kamar wasa hardai takaisu ga asibiti, kwanan mama ɗaya a asibiti Allah yayi mata rasuwa, kuka kam Zahrah da Malam Adamu sunsha shi, domin kuwa sunyi rashin jigon rayuwarsu, haƙiƙa Zahrah tayi rashin uwa ta gari, shiko Malam Adamu yayi rashin mace ta gari,, sati ɗaya da rasuwar Mama Malam Adamu yakwanta jinya, abu kamar wasa saigashi ko tashi baya iyawa, Wata rana ne aka wayi gari Malam Adamu baya numfashi, Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !! Zahrah tayi kuka bana wasaba lokaci guda tayi rashin farincikin rayuwarta,,,,, koda Alhaji Umar yazo ta aziya, baiyi ƙasa a guiwaba, cewa yayi ya ɗauki nauyin karatun Zahrah harta ƙare jami'a, yayinda riƙon Zahrah yadawo wajen Hayatu da matarsa (Baffa, Inna) sam Zahrah batajin daɗin riƙon da Baffa da Inna keyi mata domin tsananin tsangwama suke nuna mata, gahi Baffa yahau kan ɗan gadon da Babanta ya bar mata yacinye,,, Ayanzu Zahrah tana da shekara 20 aduniya, kuma harzuwa yanzu Alhaji Umar ne ke ɗaukan nauyin karatunta.....

Cigaban Labari

Adai dai bakin titin yayi parking motarsa, domin sam shikam baijin cewa zai iya shiga, wannan unguwar talakawan da tsadaddiyar motarsa, shi sam baisan ma uban me yasa Bash yayi guest house ɗinsa a wannan unguwar ba,, zama yayi a cikin motarsa haɗe da ɗaukar wayarsa yadanna mawa lambar (Number) Bash ƙira, ringing biyu kawai wayar tayi Bash da ke kwance jikin wata ƴar iskan sa ya ɗaga,, "Ina bakin titi " yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar tasa,, baiwani ɗau lokaci ba saiga Bash ya ƙaraso,

"kaga *SHU'UMIN NAMIJI* maifirgita ƴan mata, Shu'umi mai sace zuciyar duk wacce yaso, ko shaiɗan yana tsoron shu'umancin ka !!" Bash yafaɗa dai dai lokacin dayakema kansa masauƙi acikin motar, ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa " Kai ni duk ba wannan ba waishin meyasa ka tsalleki ko wani unguwa kazo nan kayi guest house ɗinka ?, ka duba fa gidajen area'nnan gaba ɗaya na talaka wane " Zaid yaƙare maganar yana maibin gidajen da kallon ƙyama,, murmushi Bash yayi haɗe da cewa
" Bazaka gane bane my man, amma wallahi ƴan mata nake samu a arean nan bana wasaba, kai bana ta ƙaice maka, yarinya sai ta kawomaka budurci (virginity) ɗinta a ɓagas, badon komai ba sai don tsananin talauci daya adda beta, yanzu haka akwai ƴan mata a ƙasa idan kana buƙata.." Bash yaƙare maganar yana murmushi mai ɗauke da nuna shi tantirin ɗan iska ne,,

taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa "Bazan iya iskanci da low class ba gaskia, kudai kuyita fama harku ɗaukomawa kanku wata cutar, yaƙare maganar yana ƴar dariyan mugunta,,

gyara zama Zaid yayi haÉ—e da cewa " Nazo maka da wani babban harka ne idan zakayi " shima Bash gyara zama yayi da kyau haÉ—e da cewa "Inajinka abokina "

Zaid ya buɗe baki zaiyi magana kenan idanunsa suka sauƙa akan wata kyakkyawar budurwa, wacce ke sanye da hijab iyaka guiwarta, hijab ɗin irin mai roba ɗinnan ne, hakan yasa ya bayyana duk wata sura na jikinta, wani irin abu Zaid yaji daga ƙasan ƙafarsa harzuwa cikin kansa, yayinda tsikar jikinsa yashuga zubawa, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa, da alokaci guda suka kaɗa sukai ja, koda yabuɗe su don sake kallon wannan halittar da'idanunsa sukai masa to zali da'ita, sai yaga saɓanin haka, domin ko a alamar gilma wanta baigani ba, saurin fita daga motar yayi haɗe da soma waige waige ko Allah zaisa yaganta, amma ko alamar ta bai gani ba........

(Tofa readers waishin wace budurwa ce Zaid ya gani ?)

*14/October/2019*

*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed 📵*

*Chapter 7*

" Lafiya kuwa Zaid wakake nema ne ?" Bash yatambayeshi,, ɗan taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa " bakomai kawai ina duba yanayin unguwar ne " yaƙare maganar yana mai komawa cikin motarsa yazauna,,, sama sama Bash da Zaid sukayi magana, domin kwata kwata hankalin Zaid baya jikinsa, burinsa kawai shine idanunsa su sake yi masa to zali da wannar kyakkyawar fuska da jikin, daya gani.....

Tunda Zahrah tafito daga gidan su Husnah tafuskanci cewa da akwai mai binta a baya, hakan yasanya taji wani irin tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, don haka ta ƙara ɗaga ƙafufunta, "Assalamu Alaikum !!" muryan Namiji mai cike da kamala ya doki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya da tafiyan da takeyi batare da ta juyo ba,, cikin takunsa na burgewa ya ƙaraso gareta, kyakkyawan saurayi ne, mai ɗauke da launin fata choculate colour, dogo ne amma ba har canba, yanada faffaɗan jiki mai burgewa, sannan yana da kwarjini ba laifi,, murmushi yayi mata haɗe da cewa "Ƴan Mata bazaki amsa sallaman nawa bane ?" saurin sunkuyar da kanta ƙasa Zahrah tayi haɗe da cewa "Wa'alaikassalam"
Chapter 4 · 0% Book details