← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 112

Sashe 23

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Sadeeq yakasance ɗa na biyu a cikin gidansu, Alhaji KHABEER SARDAUNA shine mahaifinsa, Alhj Khabeer wanda ake ƙira da Alhj Sardauna, mutum ne mai matuƙar karamci da kuma kyautatawa na ƙasa dashi, hakan yasa talakawa suke matuƙar sonsa, kasancewarsa ɗan siyasa,  Hajiya Habiba itace mahaifiyar Dr Sadeeq, mace ce itama mai tsananin karamci dakuma kyauta, tana da kyakkyawan hali wanda kowa yashaida hakan,  Dr Sadeeq shine ɗa na biyu a cikin gidansu, yanada yaya wacce ake ƙira da Aunty Raliya, Aunty Raliya dai, tana aure ne a cikin garin Abuja, tana kuma zaune  a unguwar Wuse Zone 2,  bayan Dr Sadeeq a kwai ƙaninsa Samad, Samad dai baya zaune a Nigeria yana zamane a  Australia, a can yake da karatunsa, tun Dr Sadeeq yanada shekaru 20, Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, mutuwar da ta matuƙar girgizasu, amma babu yanda suka iya dole su ɗauki dangana domin kowani bawa da kalan tasa ƙaddaran..  yanzu tsawon shekaru biyu kenan Hajiya Habiba tana matsawa Dr Sadeeq, a kan cewa yafito da matar aure, amma abun yagagara, da anfara maganar aure sai abun yalalace, ko daga baya yace baison yarinyar, ko yace  bata da nutsuwa, da haka dai magana zata ɓalakuce,, yanzu ne Hajiyarsa ta hura masa wuta akan cewa lallai tabasa nanda kwana kaɗan yafito da matar aure dan bazata ci gaba da zuba masa idanu babba dashi ace bai aje  iyali ba....

Washe gari..

Ƙarfe 3 da rabi na yamma Dr Sadeeq da kansa ya rubutawa su Zahrah sallama, domin ya fahimci cewa matuƙar bai sallamesu ba, za a iya nemanta a rasa, bakuma zai so hakan ba.

Koda suka fito daga cikin asibitin, duk yanda yaso Zahrah tashiga cikin motarsa ya kaisu gida ƙiyawa tayi,  dole haka yanaji yana gani suka tari mai taxi, baiyi ƙasa a guiwaba wajen shiga motar tasa ya rufamusu baya...

Suna isa bakin ƙofar gida, idanun Zahrah ya sauƙa a dai dai wajen da Zaid yake faka motarsa kullum idan yazo, wani irin muguwar faɗuwar gaba taji, take kuma zuciyarta tayi rauni, kuka ne ya kuma ƙwace mata, da sauri tafice a cikin motar dagudu tanufi cikin gida,,  saida Inna suka sallami mai taxi kafun suka lura da Dr Sadeeq dake tsaye a bayansu yana ƙarewa yanayin unguwar tasu kallo, "A'a Likita dama kana biye damune ?" Baffa ya tambaya washe da baki,,

"Eh Baffa ina biye daku, dama gani nayi yakamata ace nasan gidan saboda magungunan ta basu ƙareba, nakuma san basha zatanayiba matuƙar ba'a tilasta mata ba"

"Ƙwarai kuwa likita ai taurin kai gareta,  dole saida takurawa, to mushiga daga ciki mana "  Baffa yaƙare maganar yanamai yi mawa Dr S.S nuni da ƙofar shiga gidan.. Baiyi musu ba haka yabi bayan Baffa suka shiga cikin gidan,

Inna ce ta baje masa wani ƙaton tabarma ya zauna akai, yayinda ta ɗebomasa ruwa a  kofi ta aje mai.

Gyara zama Dr S.S yayi haɗe da cewa "Baffa inaso muyi wata magana ne idan har bazaka damuba " 

"FaÉ—i maganarka kai tsaye likita, kada kaji wani shakku" Baffa yafaÉ—a yana mai dawo da hankalinsa ga Dr Sadeeq.

"Maiyasa bazaku kai case ɗin Zahrah kotu ba? yakamata ace amatsayinta na marainiya a bimata haƙƙinta, bai kamata ace wani ƙaton banza ya keta mata haddi ba, sannan kuma abarshi yaci gaba da walwala, inaga yakamata ayi wani abu akai" Dr Sadeeq yafaɗa cike da damuwa.

Nannauyar ajiyar zuciya Baffa ya sauƙe haɗe da jinjina kansa, cike da  rauni yace "Bazanƙi shawaranka ba likita, sai dai a gaskia bazan ɓoye maka ba, hakan da kake so bazai samuba, domin yanda ka ganmu nan haka muke rayuwarmu, mu talakawa ne, cin yau da ƙyar na gobe da ƙyar, kuma maganan nan ma da nake maka, bansan wanene yayi mawa Zahrah fyaɗe ba, to ka ga kenan babu batun ma  ɗaukar fansa"

"Wanene ZAID ?" Dr S.S ya tambayi Baffa.

Washe da baki Baffa yace " shine yaron da Zahrah ta amince dashi, yake zuwa zance wajenta, idan kuma bazaka mantaba ai nafaɗa maka shiɗin yaron kirkine, na tabbatar da cewa baisan  haka yafaru da ita ba, da nasan dole zaizo" Baffa yaƙare maganar yana mai jinjina kai..

"Shine yayi mawa Zahrah fyaÉ—e !" Dr S.S yafaÉ—a murya a kausashe,

Gaba É—aya idanunsa Baffa ya zaro, alamar maganar ta dake shi, "Zaid fa kace likita !" Baffa yafaÉ—a cikin kaÉ—uwa,

"Ƙwarai kuwa domin kuwa jiya ta ambaci sunansa, nakuma ji da kunne na, amma tunda kace ba zaku kai case ɗin kotu ba, bakomai ni zan wuce" Dr Sadeeq yafaɗa yana mai  miƙewa tsaye, bayan yaciro damin kuɗi ya a jewa Baffa kan tabarma,,

"A'a hadda ɗawainiya haka likita? to to munagodiya!" Baffa yafaɗa cike da farinciki, 

(hmm mai hali dai baya fasa halinsa)

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Malam hayaƙi, hayaƙi Malam a ɗakin Zahrah !!" Inna tafaɗa cike da tashin hankali, ai da sauri Dr Sadeeq da baffa, suka nufi ɗakin Zahrah'n wanda hayakin haryasoma cika tsakar gidan, dayake ƙofar bata da wani ƙarfi duka ɗaya Dr S.S yayi mawa ƙofar ɗakin tabuɗe,  gaba ɗaya ɗakin yaturnuƙe da hayaƙi yayinda wuta kecin wasu kaya dake aje tsakiyar ɗakin, gefe da kayan kuma Zahrah ce durƙushe tana kuka, har wutan yakusa ƙarasowa gareta,

Cikin zafin nama, Dr Sadeeq yasanya hanunsa, ya janyeta daga tsugunnen da take,   kai tsaye waje yafito da'ita, domin kuwa hayaƙin yasoma shiga cikin maƙoshinsu, Baffa da Inna kuwa ruwa suka ɗebo suka kashe wutan,

Riƙeta yayi gam yayinda ya kafeta da idanunsa da suka rune tsabar ɓacin rai,

Baisan meyake damuntaba, rashin hankaline ko kuma sangartane baisaniba, yasan cewa tanajin ciwo a cikin zuciyarta, amma abun da take ƙoƙarin aikata mawa kanta, kama yake da taɓin hankali,  ƙoƙari yayi wajen danne zuciyarsa, haɗe da saisaita muryarsa, "Maiyasa Zahrah ? bazaki ɗau ƙaddaranki ba ?" yayi mata tambayar cikin tausasa murya,   hawayene suke gudu haɗi da ambaliya akan fuskarta,  gaba ɗaya jitakeyi duniyar najuya ma ta, dawowanta gida yasake tada mata da mikin dake maƙare cikin zuciyarta, duk da kuwa dama cewa mikin  bai wau ya kwanta ba ne,,

Saurin saketa yayi  sakamakon ƙarasowar Baffa da Inna wajen, zamewa tayi aƙasa dabas tana mai sakin kuka,

Kallon Baffa Dr Sadeeq yayi, kafun Baffa yace komai Dr Sadeeq yace, "Baffa ni nawuce sai nasake zuwa "

"To Likita mun gode ka gai da gida " Inna da Baffa suka haɗa baki wajen faɗa, da "To"  kawai Dr Sadeeq ya amsa musu haɗe da sa kai yafice daga cikin gidan,

Kama hanun Zahrah Inna tayi suka zauna akan tabarma, cike da damuwa Inna tasoma cewa "Maiyake damunkine Zahrah ? sai kace akanki aka fa ra yin fyaɗe? gaba ɗaya duk kinbi kinɗaga hankalinki, muma kin ɗaga mana namu hankalin, a gaskia nida Baffanki munsoma gajiyawa da wannan halin naki, bayan kinso caka mawa kanki almakashi, likita ya hana, yanzu kuma ƙona kanki kikesonyi, wai kina  cikin hankalinki kuwa Zahrah?"

"Gaya mata dai Salame, domin nima nan nasoma gajiya da rarrashi,  yanzu dakika ƙona kayayyakin daya baki, shiɗin kika ƙona ne? tambayanki nake shiɗin kika ƙona ?" Baffa yafaɗa cikin faɗa faɗa, domin ya lura idan suka biyewa Zahrah tofa bazata taɓa daina yunƙurin kashe kanta ba..

Zuciyar Zahrah ne tasakeyin rauni, " Allah sarki ni, komai nayi, ganin laifina suke, shin bancancanci rarrashi da kulawaba? fyaɗe akayimini amma hakan baiwani shiga jikin kowa ba, natabbata idan da iyayena suna da rai, to tabbas da bazasu taɓa kwantar da hankalinsu ba, kuma nasan dolene sai sun ɗaukarmin fansa,  bakuma zasu taɓa gajiyawa daniba, wayyo Allah na mutuwa tayi mini yankan ƙauna daku iyayena !!" maganar  da Zahrah take faɗa kenan a cikin zuciƴarta, hawayenta ne suka sake tsananta zuba,  sai yau ta tabbatar cewa Maraici bashi da daɗi, sai yau tasake tabbatar da cewa Allah ne kaɗai gatan ta,  Zaid ya cuceta, yayi mata babban tabo wanda hargaban abada ba zata taɓa mantawa dashi ba, "maiyasa Zaid ?" tasake tambayar kanta bayan kuma tasan bata da amsa,,

Haka Inna da Baffa suka wuce É—aki suka barta zaune a tsakar gida tana tsiyayar hawaye, babu mai rarrashi.

Tuƙin mota yake amma gaba ɗaya hankalinsa yanaga yanda yabaro Zahrah,  tsantsar tausayinta yakeji, yanason taimaka ma ta amma to tayaya? ta wacce hanya? duk alokaci ɗaya ya tambayi kansa,  wayarsa ce tasoma ƙara alamar shigowar ƙira,  Zabba'u shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da ɗaukan wayar yakara a kan kunnensa, 

"Cike da sangarta Zabba'u tayi masa sallama, amsa sallaman yayi a daƙile haɗe da cewa "Ganinan zuwa" ƙit yakashe wayar haɗe da cillata kan kujeran mai zaman banza, shi sam baisan yanda zaiyi da Zabba'u ba, amma a zahirin gaskia ɗabi'u da tarbiyanta basu masa ba,duk da kuwa cewa ƴar uwa take a garesa.

New York City

Tsaye yake agaban wani tangamemen cupboard paper, wanda yake liƙe ajikin wani abu kamar allo,  sanye yake da 3 guater jeans, yayinda yabar gaba ɗaya surar jikinsa a waje, kasancewar baisanya rigaba, babban abun  ɗaukar hankali ajikinsa shine lafiyayyun, 6 packs ɗinsa, dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa, riƙe yake da wani dogon pen a hanunsa da'alama dai wani abu yake zanawa mai mahimmancin gaske,, ƙayataccen murmushinsa yasake, haɗe da ɗaukan glass cup ɗin da wine ɗinsa ke ciki, yakai bakinsa, saida ya shanye duka wine ɗin dake cikin kufin, kafun ya aje kofin kan wani ɗan ƙaramin table dake kusa dashi,

Hanunsa yasanya akan kyakkyawar fuskar daya zana a jikin cupboard paper ɗin, a hankali yashiga shafa zanen , hanunsa yakai dai dai saitin bakinta, haɗe da shafawa, idonsa ɗaya yakashe haɗe da lasan laɓɓansa, 

"Kinkasa barina My Sugar Baby, maiyasa ? " yayi tambayar yana mai tsare zanen dake jikin cupboard papern da ido,

"Bazaki amsaminba ko? fushi kike dani ko sugar baby na?"

Yasake tambayar wannan zanen dake jikin cupboard paper'n.

Murmushi yakumayi haɗe da matsawa daf da cupboard paper'n bakinsa yaɗaura adai dai kumatun ta yamanna mata kyakkyawan kiss, "Kikulamin da kanki kinji My Zahrah!!" yafaɗi maganar cikin shauƙi,,  sai alokacin nalura ashe zanen fuskar Zahrah ne raɗau ajikin cupboard paper'n, bakaɗan ba kuma zanen yayi kyau,, kyakkyawan ƙyalle yasanya yarufe zanen, haɗe da ɗaukar wayarsa yafice daga cikin ɗakin...
Chapter 23 · 0% Book details