Sashe 54
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaid ne zaune a cikin falon sa dake guest hause ɗinsa, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa yana cikin tashin hankali, kwalaben giyane zube a gabansa, guda uku daga cikin kwalaben duk ya shanye giyan dake a
cikinsu,  ba abun dake gigita masa tunani da ƙwaƙwalwa kamar yanda Zahrah ta nunamasa tsana a fili ƙarara, kallonsa yakai ga hanunsa na dama wanda yake fidda jini, bakomai yajawo hakan ba face ƙarfen da Zahrah ta kwaɗa masa akan hanun,, runtse idanunsa dasuka kaɗa sukai jajur yayi, haɗe da cije laɓɓansa, wani irin zafi yakeji acikin zuciyarsa a duk sanda idanunsa suka hasko masa lokacin da Zahrah taje ta faɗa ƙirjin Dr.Sadeeq, jiyake kamar ya kurma ihu, ko zai samu salama acikin zuciyarsa.... Ahankali yamiƙe tsaye haɗe da nufar ɗakinsa, Da ƙyar yake iya tafiya, saboda abuge yake mankas, kai tsaye  ɗan ƙaramin drowern dake kusa da gadonsa yanufa, wani tablet yaɗauko haɗe da ɓarewa kusan guda takwas ya watsa a bakinsa, haɗi da korawa da ruwan swan... Faɗawa kan gado yayi yana me rumtse idanunsa, "Natsaneka" shine kalmar da tafi ɗaga masa hankali aduk cikin kalaman da Zahrah ta faɗa masa. itace kuma kalmar da takeyi masa yawo acikin kansa, cikin wani irin yanayi Zaid yatashi tsaye haɗe da nufar wajen da yake aje kayan shafansa, watsi yashigayi da duk wani abu dake kan dressing mirror ɗin nasa, lokaci ɗaya yayi buji buji da ɗakinsa, yayinda ya fasa gaba ɗaya kwalaben turarensa, har sai da wasu kwalaben suka yankesa a hanu da ƙafarsa, amma don tsabar baƙin kishi ko zafi baiji ba, idanunsa Zahrah kawai suke hangomasa kwance a ƙirjin Dr.Sadeeq. Lokaci ɗaya yaji wani irin juwa ta ɗebesa, harsai da yariƙe bango, a daddafe yaƙa risa kan gadonsa ya kwanta, ji yayi kansa yasoma juyawa, yayinda idanunsa suka soma rufewa, yasoma ganin komai bibbiyu, cikin mintuna ƙalilan idanunsa suka rufe ruf.....
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*25/December/2019*
*Wattpad user name fatymasardauna*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
        *SHU'UMIN NAMIJI !!*
   *Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*Â Â
    Â
     *WATTPAD*
  @fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
  Â
   *CHAPTER 68 to 69*
Â
Ba'itace ta farka ba sai wajen ƙarfe ɗaya na rana..
A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaɗa suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buɗe idanun nata ba sai yanzu. Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiɗin yacika ɗan iska kuma shu'umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji ɗar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiɗin acikin ƴan iska ma daban yake,, haka nan taji gaba ɗaya zuciyarta ta ƙeƙashe takuma bushe, lallai tunda ya nuna mata shiɗin babban ɗan iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako ƙafa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali... Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maƙurar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taɓa mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baƙin duhu, ya katse mata jin daɗi da kuma walwalanta, ya lalata mata rayuwa a rana ɗaya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata ƙarfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar ƴa mace? tasan ƙiyayya amma kuma zafin ƙiyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne, tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haƙiƙa ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ba'irin ƙuncin nan bane da yake fita, lallai ƙuncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roƙi Allah daya sassauta mata.....
Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haɗe da miƙewa zaune, babu amfanin ɓata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba.   Kayan jikinta tashiga cirewa, haɗe da ɗaura zani akan ƙirjinta kana ta sanya lufaya....
Tana fitowa daga cikin É—akin nata, Inna ta kalleta haÉ—e da cewa.
"Yauwa Zahrah kintashi ko? ya ƙarfin jikin naki de?" alokaci ɗaya Inna tajero mata duka waƴan nan tambayoyin..
"Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba ɗaya banajin daɗin jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah" tafaɗi maganar tana me ɗan rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana ƙoƙarin ɗibanta..
"Kinkuwa ci sa'a yanzu na ɗaura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki ɗiba, amma idan kin ɗiba ki ƙaramin ruwa acikin tukunyar" Inna tafaɗi haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin dake ɗaure kan murhu...
Sosai taji daɗin jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi, bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haɗe da ɗaukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta, ko powder bata shafa ba...
Doguwar rigar atamfa irin me sauƙin kuɗin nan tasanya ajikinta, haɗih da ɗaura hijab akan kayan nata mai kalar blue, yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuɗi).  Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba....
Kallon Inna dake Æ™oÆ™arin sauÆ™e tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace.  Â
"Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah"
"Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace ɗazu ɗazun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauƙin da zaki soma fita yawo?"
(Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol)
"Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!" Zahrah ta faɗi haka cikin yanayi na nuna zaƙuwa.
"Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi"
"A'a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci" takai ƙarshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan...
Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na mamaki...
Giransa ɗaya ya ɗage haɗe dayin murmushi....  "Ashe ma kinyi sauƙi, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me takowa zuwa wajen da take tsaye.
Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru ɗazu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taɓa mutumin da ba muharrami'n su ba, duk da cewa ba'acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba...
"Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita ɗakin mijinta" Dr.Sadeeq ƴafaɗi haka cike da zolaya.
Sai alokacin ta'iya ɗago kanta ta  aika masa da
hararan wasa,,,,,  " Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?"
"Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keÉ—in sauri kike zaki unguwa ko?"
Yaƙare maganar yana me leƙa fuskarta wanda ta sunkuyar da ita ƙasa.
Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da sanya haƙorinta na sama taɗan datse leɓenta na ƙasa..
"Yajikin naki?" yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya.
"Dasauƙi, dama ni lafiyata ƙalau" tabasa amsa a ta ƙaice..
"Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti"
Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace, "Lafiyan?" ta tambaya cike da mamaki.
"Eh itafa lafiyan, to baga example akan ki ba" yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya'isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa..
"Hmm" kawai Zahrah tace haÉ—i da É—an satan kallonsa, aikuwa karab suka haÉ—a idanu, saurin É—auke nata idon tayi.
Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiɗin ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya ɓanɓareta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya'iya saboda alokacin tana cikin halin buƙatar taimako, kum san nan shi be rungumeta don yaji daɗi ba.
"Inazakije ne haka, da rana tsaka?"Â yajefo mata tambaya.....
"Gidan su Husnah zani" ta basa amsa a taƙaice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba...
"Shikenan muje saina kaiki, domin kinsan samun abun hawa zaimiki wahala, saboda rana tayi sosai"Â
Kallonsa tayi naɗan sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Dama kabarni, koda ƙafana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma nasan zan samu"
"Da gaske zaki iya takawa da ƙafa daga nan har gidansu Husnah? to shikenan tunda zaki iya, zaimafi kyau ki taka da ƙafan, saboda kisamu ki ɗan rage wan nan ƙiban dakika haɗa, gaba ɗaya duk yasa kin yi muni, kin zama wata super mama dake" yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo.
Waro idanu Zahrah tayi haɗi da soma kallon kanta, wai tayi ƙiba, takuma zama super mama.
Take idanunta suka yi raurau dasu, yayinda ruwan hawaye ya soma cika cikin su, "ashe da gaske tayi ƙiba bata sani ba? gashi harya fara goranta mata, to me yasa ita bataganin ƙibanta?" tatambayi kanta...