Sashe 64
Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Baffa yayi haɗe da cewa "Ƙwarai mungode da wannan ƙoƙarin naka, amma sai de nace kayi haƙuri, duk da cewa mahaifin Zahrah baya raye ni ƙaninsa ina raye kuma niɗin ma ubane a wajenta, zan yi amfani da ɗan abun da nake dasu wajen ganin namata kayan ɗaki iya dede ƙarfina, kamarde yanda kowani uba keyiwa ƴarsa, wannan shine kaɗai gatan da zamu iyayi mata a yanzu" Baffa yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..
Ajiyar Zuciya Dr.Sadeeq ya sauƙe, haƙiƙa shi Zahrah kawai yakeso bawai wani abu na daban ba, kuma shi baiso akawota da komai, domin musamman ya ware mata ɓangarenta, kuma tuni yabawa wani abokinsa me saida furnitures a Dubai order akan akawomasa setin kujeru dakuma gado harma da duk wani abu wanda yasan zai ƙawata ɗaki,, amma tunda yaga Baffa yadage akan cewa shima zaiyi iya nasa ƙoƙarin shikenan zai ware wani ɗaki na da ban idan yaso sai a sanya kayan da Baffan yayi mata acan,,, cike da mutuntawa Baffa da Dr.Sadeeq sukayi sallama....
Baffa na shiga gida ya kalli Inna dake zaune,, "Salame inajin fa tafiyana yola yagabato idan banje jibi ba to zanje gata insha Allah"
Fuska É—auke da mamaki Inna ke kallonsa, "Yola kuma Malam?"
"Ƙwarai kuwa, kinga fitana ɗin nan to yaron nan ne Sadeeq yazo min da maganar cewa inbasa dama yaturo magabatansa don sukawo sadaki akuma sa rana, to ni dai nace yaturosu duk sanda yakeso, yanzu dole zanje yola insanya fili dakuma gonan nan namu na gado a kasuwa idan aka siya intarkata kuɗin nan nasamu nasaiwa yarinyarnan kayan ɗaki dakuma kayan aikace aikace kamar de yanda kowani iyaye kemawa ƴarsu dan baiyiwuwa ace mu miƙata haka"
Ajiyar zuciya Inna tasauƙe haɗe da gyara zama " Duk naji batunka Malam, amma kuma mezai hana kabar shi mijin nata yayi mata komai, ae naga yana da halin da zai iyayi mata fiye da wannan ma"
Murmushi kawai Baffa yayi shi kam tun ba yau ba yasan cewa bakoda yaushe ne Inna take gane karatun da'ake biya mata ba, don haka baiƙara cewa da'ita komai ba yawuce ɗakinsa, domin yasan kozai shekara a wajen yanason ganar da'ita tofa bazata fahimcesa ba,,, Inna kuwa baƙin ciki ne yakamata ina ma laifin yace zaiƙara jari da kuɗin, sai yace wani wai zai siyawa Zahrah kayan ɗaki,, haka taita ƙananun maganganunta babu maijinta ma balle yatanka mata......
Da yamma Dr.Sadeeq yaƙira Baffa yasanar masa cewa Baffansa zaizo da dare donsu tsaida magana, duk da cewa Baffa yayi mamakin sauri irin na Dr.Sadeeq ɗin amma saiya share yace Allah yakawosu lafiya,,
Hargida Baffa yaje yasanarwa Alhaji Umar abun da Dr.Sadeeq yace, kuma dama Alhaji Umar ɗin tuni yasan da maganar saboda duk abun da yafaru Baffa yanazuwa ya sanarmasa har kawo lefen da akayi ma Baffa yasanar masa,, sosai Alhaji Umar yayi murna yakumace zaizo gidan Baffa'n da dare a ƙarɓi baƙin dashi......
Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakane yakasance domin ana idar da sallan Isha Baffa Amadu da wani shaƙiƙin amininsa suka zo gidansu Zahrah,, sosai Baffa da Alhaji Umar suka musu tarba na mutunci,, zama sukayi haɗe dayin magana ta fahimtar juna, nan Baffa Amadu ya miƙa sadakin Zahrah ga Baffa naira dubu ɗari (100,000) bawani ɓata lokaci Baffa yasanya lokacin aure wata ɗaya, aikuwa take kowannensu yacika da farinciki haka sukayi sallama cike da girmama juna.......
(Team Dr. Saiku fitarmana da ankon biki, nasan duk Baba Zaid ze saya mana auren Zahrah'nsa ne ae 🤣🤣😜)
*4/Junuary/2020*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
~Fatymasardauna~
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
     *SHU'UMIN NAMIJI !!*
  *Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
        *WATTPAD*
      @fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
   Â
   *CHAPTER 78 to 79*
Zahrah na zaune a É—akinta Inna takutso kanta cikin É—akin.
"Idan kin gama rubuce rubucen banzan naki kije Baffan ki nanemanki!" Inna tafaɗi haka aƙufule, ko jiran amsan da Zahrah zata bata batayi ba tayi ficewarta acikin ɗakin,,, da kallon mamaki Zahrah tabi bayan Inna wai meke faruwane tun dawowarta amakaranta tafuskanci cewa ran Inna a matuƙar ɓace yake da'ita, domin kuwa ko abincin rana Inna batayi mata tayi ba, kamar yanda ta sabayi mata kullum, to koma dai menene Allah yasa bawani abu bane me zafi... Tattara books ɗin dake gabanta tayi haɗe da miƙewa ta sanya hijab a jikinta kana tafice daga cikin ɗakin.....
Da sallama ɗauke a bakinta takutsa kanta cikin ɗakin Baffan nata,,  zama tayi akan tabarman dake shimfuɗe a tsakiyan ɗaki, haɗe dayi mawa Baffa barka da gida,, fuska ɗauke da fari'a Baffa ya amsa mata..
Gyara zama Baffa yayi haÉ—e da cewa   "Bakomai yasa nayi Æ™irankiba sai dan na sanar dake abun dayake faruwa sannan kuma na danÆ™amiki haƙƙin ki a hanunki,  yau da safe yaron nan likita yazo yasameni akan cewa zaituro magabatansa don sukawo sadakin ki, nakuma bashi dama, to yanzu dai sun riga da sun danÆ™amin sadakin ki a hanuna saboda haka ga abunki naira dubu É—ari ne cus nakine halak malak" Baffa yaÆ™are maganar yana me miÆ™a ma Zahrah maÆ™udan kuÉ—in dake hanunsa.... Â
Gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi laƙwas gaba ɗaya duk wani kuzarinta ya gudu, hakanan taji wani iri a cikin zuciyarta.
"Ki karɓa mana Zahrah" Baffa yafaɗi haka ganin da yayi ko ɗago kanta takasa yi.
Girgiza kanta ta shigayi a hankali cikin muryarta me sanyi tace "Duk abun da ka yanke a gareni Baffa dai dai ne, amma maganar sadaki ka riƙe a wajenka, saboda ko kabani babu abun da zanyi dasu!" taƙare maganar cikin ladabi.
"A'a Zahrah ki karɓi abunki haƙƙin kine, saboda haka nima babu abunda zanyi dashi ki karɓi abunki saiki adana a wajenki, idan kuma wani abu zaki saya saiki saya, amma kada kiyi almubazzaranci dasu, zaifi kyau kisaya abu me mahimmanci wanda zai amfaneki yanzu ko gaba" maganar da tafito daga bakin Baffa kenan.
Shiru Zahrah tayi ita tama rasa yanda zatayi gaba ɗaya yanayinta yasauya, cikin sanyin jiki Zahrah tasanya hanu ta karɓi sadakin nata a hanun Baffa bawai dan ranta yasoba sai dan Baffa ya matsa akan cewa saita karɓa..
"Yauwa kinga idan kika riƙe abunki a hanunki ae yafi ko, sai kuma maganar sa rana, nasa nanda wata ɗaya, ai inaganin hakan yayi domin kafun lokacin insha Allah mungama iya ƙoƙarin da zamuyi wajen sayan ƴan kayayyakin ɗaki"
Wannan magana ta sa rana yafi komai rugaza mata zuciya, fiye da maganan sadaki, haka nan taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta,, amma haka tayi mawa Baffa sallama cikin sanyin jiki tanufi ɗakinta...
Zama tayi akan katifarta haɗe da rumtse idanunta, take hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta suna gudu akan fuskarta,,  shikenan yanzu saura mata wata ɗaya tazamo matar aure? tambayar da tayiwa kanta kenan, bazata iya faɗan wani irin yanayi ta tsinci kanta aciki ba, fargaba ne ko kuma tsoro ne shine abun da bata sani ba,, idanunta ta buɗe haɗe da maida kallonta ga kuɗaɗen dake riƙe a hanunta,, tsurawa kuɗin idanu tayi tamkar mai son gano wani abu ajikin kuɗin,,  hawayene suka kuma ɓalle mata, batasan dawani idanu zata kalli Dr.Sadeeq ba, shi wani irin mutum ne? yasani ƙwarai cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace da ita da bazawara duk ɗaya suke, amma kuma shine ya cire maƙudan kuɗaɗensa yabada amatsayin sadakinta alhali kuma farashinta baikai haka ba, ita ba irin matan nan bane dasuka dace a sayesu da tsada har haka ba, domin kuwa acikin abubuwa goma da zasu ƙara farashinta babu kaso tara, saboda haka bata cancanci wannan sadaki ba,,  hanu tasanya ta share hawayenta, haƙiƙa bazatace batason Dr.Sadeeq ba amma kuma batajin son nasa acikin jini da jikinta, amma hakan bawai wani abu ne da zaisanya taƙi aurensa ba, domin shi ne ma mutum na farko aduniya daya cancanci ta aura, kodan halaccin daya gwada mata a rayuwa.... Cikin wata jakarta tasanya kuɗin sadakin nata, haɗe da dawowa ta kwanta akan katifarta, bazama ta iya ƙarisa assigment ɗin nata ba domin kuwa gaba ɗaya yanayinta yasauya damuwa ta bayyana a tattare da'ita,, da ƙyar ta iya jawo wayarta taƙira Husnah ta sanar mata da duk wani abun daya faru,, daɗine ya kama Husnah sosai take ta hau farinciki haɗe da cewa gobe zatazo yakamata su fara shirye shiryen biki tunda wuri, domin wata ɗaya bawani lokaci ne me tsawo ba idan har darai da kuma lafiya...
*****
"Kiyi kuka da kyau Saleema amma kuma kozaki mutu bazaki auri Sadeeq ba matuƙar bai fasa auren da zaiyi da waccar ƴar ƙasƙantattun mutanen ba, ni bazan iya haɗa iri da jinsin matsiyata ba!" Abunda Hajiya Habiba take faɗa kenan cikin ɓacin rai.
Ɗago kai Saleema tayi takalli mahaifiyarta ta fuska caɓa caɓa da hawaye, cikin muryar kuka Saleema tasoma cewa " Wlhy inasonsa Mom kuma bazan taɓa iya auren wani bayan shiba, nidai na amince zan aureshi a haka, idan yaso bayan auren sai nasan yanda zanyi naƙori ita yarinyar"
Kallon ke shashasha ce Hajiya Habiba tashiga yi mawa Saleema, cike da baƙin ciki taja tsuka haɗe da watsawa Saleema'n harara "Nibansan yaushe zuciyarki ta mutuba wlhy Saleema, ashe ke baki da hankali? to nifa kisani nagama maganata aure da Sadeeq ne anfasa, kuma suzo su kwashe lefensu bama buƙata, domin kuwa kamarni Hajiya Habiba bazan lamunci cinfuskaba, saboda abunda suke shirin yi yanzu cin fuskane a gareni" fuuuu haka tayi wucewarta sama, tabar Saleema tana ta ruskar kuka, saikace wanda akace ubanta ya mutu....
****
Baffa na zaune a wajen sana'arsa wasu maka makan motoci guda biyu suka faka adaf dashi.. Sosai yayi mamakin ganin Alhaji Ma'aruf yakuma dawowa garesa a karo na biyu, wanda ko kusa baiyi tunanin haka ba.. Â
Bayan sun gaisane Alhaji Ma'aruf ya nisa haÉ—e da cewa "Nasan zakayi mamakin dawowata gareka Malam Hayatu, sai de kuma me nema baikamata ya gajiya ba"