← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 112

Sashe 98

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye abincin anan, yafaɗa yana me nuna mata kan sofa, cikin jin daɗi ta aje abincin,  harta juya zata fita kuma, saita tsaya, haɗe da dawo da kallonta garesa.   "Kayi haƙuri, ko badanni ba,  kaci abincin" juyawa tayi tacigaba da tafiya, hartakai bakin ƙofar fita Zaid yace
"Afra"
Juyowa tayi garesa, ƙwalla yagani kwance acikin idanunta,  da hanunsa yayi mata nuni alamar tazo,  kanta aƙasa hartaƙaraso gareshi, domin gaba ɗaya, yacika mata idanu, sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa, ta ƙayatar da ita.

Bata tsammata ba saiji tayi, yasanya hanunsa, ya jawota jikinsa, rungumeta yayi, haɗe da ɗaura kansa akan kafaɗanta, ya lumshe idanunsa,   jikinta ne gaba ɗaya yayi sanyi, hanunta duka biyu tasanya itama ta rungumesa, ƙam, haɗi da lumshe idanunta, wani irin shauƙi ke ratsata, ƙamshin sa mai matuƙar daɗi, shi yayi sanadiyar dulmiyata cikin wata duniya....

Yana rungume da ita amma kuma zancen zuci yake.

"Tabbas, abun da Abid yafaɗa masa, gaskiyane, Afra itace matar da Allah Ya zaɓa masa kuma daidai dashi,  wannan zaɓin Allah Ne, bazaɓinsa ba, kuma zaɓin Allah Yafi zaɓinsa, saboda haka, dole zai karɓi Afra amatsayin matarsa, kuma zai yi ƙoƙari wajen ganin, ya yi mata adalci, bayajin sonta aransa, amma zaiyi iyaka, bakin ƙoƙarinsa wajen ganin, yazauna da ita lafiya , idan ya rabu da ita, baisan wace  buɗaɗɗiyar zai kuma samu ba, shidai yasan irin Zahrah ita kaɗaice, kuma yariga daya rasata, saboda haka dole zaiyi haƙuri da Afrah, kodan son kyautata masa daya lura tanayi"

******

Zaune take akan kujera, ta ɗaura ƙafafunta,  bisa kan wani table na glass, dake cikin falin,   wata ƴar ficikan riga maroon colour ne, sanye ajikinta,   saman wuyan rigan net ne, yayinda hanun rigan kuwa, ya kasance na vest, wato siririn hanu,   tayi kyau sosai acikin shigar nata, hanunta riƙe yake da kofi, wanda ƙe ɗauke da Banana Smothie aciki, sai kaɗa kanta take da alama, taji daɗin Banana Smothie'n da take sha, duk da cewa,  har yanzu bata wani jin daɗin jikinta, amma haka ta daure,  take abu kamar me lafiya, miƙewa tayi daga zaunen da take, haɗe da ƙarasawa gaban tangamemen tv plasma'n dake aje cikin falon, remote ta ɗauka, ta ƙara volume ɗin tv,  ta aje remote ɗin kenan, wutan nepa ta ɗauke, gashi magriba ta somayi, ɗakin babu wadataccen haske,  babu zato ba kuma tsammani, taji an sanya hanu an rufe mata idanunta, wani irin ƙara tasake alokaci guda,  sai kuma ta yanki jiki tafaɗi ƙasa,   da hanzari Dr.Sadeeq wanda shi yayi mata haka, yasanya hanu ya tarota tafaɗa cikin jikinsa, wayarsa ya laluɓo ya kunna torchlight, daidai lokacin ne kuma wutan nepan ya kuma, dawowa haske ya baibaye ɗakin,   amatuƙar razane yashiga girgizata, yana ƙiran sunanta,  amma ina ko motsi batayi ba, hanunsa  yakai kan hancinta, yaji babu alamar shiga da fitar numfashi,  tsorone yakamasa, haɗe da ruɗewa,  akiɗime yashiga jijjigata, amma bata motsaba, saboda babu numfashi ajikin ta.....

   *13/February/2020*

*✅ote me on Wattpad*
       @fatymasardauna      
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Lovely Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

                 *WATTPAD*
           @fatymasardauna

      
        *CHAPTER 110*

A matuƙar ruɗe yake girgizata, yana me ƙiran sunanta, sosai ya tsorita da al'amarinta, gaba ɗaya ya ruɗe, yama manta da cewa shi ɗin likita ne, sungumarta yayi acikin ƙirjinsa, direct sai cikin mota,  a gidan baya yasakata, yafigi motar da wani irin gudu,  saboda tsabar gudun da yakeyi, mintuna kaɗan, suka kawoshi, cikin asibitinsu,   a ruɗe yaje wajan, abokin aikinsa Dr.Salim, yasanar masa abun dake faruwa, emergency aka wuce da ita direct,    shikam Dr.Sadeeq kasa shiga cikin emergency room ɗin yayi, suke karɓan emergency patient  idan aka kawo,  amma kuma sai yau,  gashi shine da kansa ya kawo,  sai kaikawo yake tayi, aƙofar shiga emergency room ɗin, kwata kwata hankalinsa baya jikinsa.. 

Bayan Mintuna 30

Yana tsaye ajikin bango, idanunsa a lumshe suke, zuciyarsa kuwa, bugawa takeyi da ƙarfi, tamkar zata faso cikin ƙirjinsa, ta fito.

Dr.Salim da sauran doctors, ɗinne suka fito daga cikin ɗakin, har yanajin tuntuɓe, agarin saurin ƙarasawa inda suke.

"Salim ya ya take? tafarfaÉ—o ne? Meke damunta dan Allah? Allah Yasa tana lafiya?" Duka waÆ´annan tambayoyin, Dr.Sadeeq ya jerawa Dr.Salim su.

Murmushi Salim yayi, haɗe da sanya hanunsa,  ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq.
"Haba Man, saikace ba doctor ba, duk kabi ka ruÉ—e, bawata babbar matsala bace bafa, kaida kanka ma zaka iya maganceta, amma duk karuÉ—a kanka"

Ajiyar zuciya me ƙarfi, Dr.Sadeeq ya sauƙe, sakamakon jin daɗin kalaman  da Dr.Salim  yayi.

"Masha Allah! kada kaga laifina, wallahi Salim, inasonta sosai ne, banason wani abu, ya sameta shiyasa" Dr.Sadeeq yafaɗi haka,  yana me lumshe idanunsa.

Murmushi Salim yayi, haɗe da cewa.  "Muje office"
Babu musu Dr.Sadeeq yabi bayan Salim, suka wuce office É—in Salim É—in.

Suna shiga suka zauna, su dukansu akan kujera ɗaya,  murmushi Salim yayi haɗe da maida kallonsa ga Dr.Sadeeq, hanu yasa ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq ɗin, cikin son kwantar masa da hankali yace.
"Kada ka damu Sadeeq, ba wani abu bane, tsananin tsorone kawai,  ya sata suma, amma bayan haka babu wani ciwo dake damunta, sai dai naga tana da hawan jini,  amma kuma gaskiya abokina, ka iya aiki,  wai ma watanku nawa da aure ne yanzu?"

Harara Dr.Sadeeq,  ya jefawa Salim.  "Wannan wani irin iskanci ne Salim?  me ya haɗa ciwonta da tambayan watannin auren mu?  yanzu ba lokacin wasa bane, ina tsananin son matata, bana ƙaunar naga wani abu yasameta, idan akwai wani abu bayan wannan, ka sanar dani, idan kuma kaƙi zan bincika da kaina, daɗin abun nima likita ne"   Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙoƙarin miƙewa tsaye, sarai yasan iskancin Salim, iya shegensa yayi yawa, gwamma ma yaɗauki Zahrah'nsa, kawai su koma gida, inyaso shida kansa, zaiyi checking ɗinta agida, dama ruɗewan da yayine, yasanya ya kawota asibiti.

Hanunsa Salim ya riƙe haɗe da cewa.
"Meyayi zafi kuma? daga tambayar watannin aure,  yanzu duk ba wannan ba, miye tukuicina wanda zaka ban, idan nafaɗama wata magana me daɗi?"

"Tukuici kuma? wace magana me daÉ—i kenan? nida matata bata da lafiya, har akwai wata magana da za'a faÉ—amin wacce zatayimini daÉ—i? nace maka kadaina min wasa ko Salim, yanzu ba lokacin wasa bane." Injicewar Dr.Sadeeq.

"Koma dai menene can maka, kuma tukuicina ne sai ka bani, ina tayaka murna, saboda madam ɗinka, tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki, na wata biyu!" Salim yaƙare maganar yana faɗaɗa fari'ar, dake kan fuskarsa.

Zama daɓas Dr.Sadeeq, yayi akan kujera, haɗe da sanya hanunsa, ya kama duka kafaɗun Salim, cike da tsananin farinciki yace "Dagaske kake Salim? Zahrah na ɗauke da ciki na ajikinta? Kafaɗamin gaskiya, dan Allah karka yaudareni!"

Dariya Salim yayi haɗe da cewa "Wallahi ba wasa nake maka ba Sadeeq,  da gaske matarka, kuma Zahrah'n ka, tana ɗauke da ciki, sannan kuma yana da kyau, ka kiyaye ɓacin ranta, dakuma duk wani abu, da kasan zai sanya ta tsorita, saboda yawan tsorita zai iya haifar da zubewan cikin.."

Kafun ma Salim yaƙarisa zancensa tuni, Dr.Sadeeq ya sulale ƙasa yayi sujjada, na tsananin nuna godiyarsa ga ALLAH, Haƙiƙa ya matuƙar jin daɗin, wannan albishir ɗin da Salim yayi masa, rungume Salim yayi cike da farinciki.

"Thank you so much Salim, haƙiƙa yau kasani farinciki sosai, kuma kaima insha Allah, zan saka farinciki, ta hanyar baka tukuici, wanda zakaji matuƙar daɗinsa"  yanakaiwa nan a zancensa ya sake Salim, haɗe da ficewa daga cikin office ɗin, direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa.

Shigowarsa, yayi daidai, da buɗe idanunta,   wani irin ƙawataccen murmushine, kwance akan fuskarsa,   ƙarasowa yayi, kan gadon ya ɗagota, haɗe da rungumeta, tsam acikin ƙirjinsa, wani irin daɗi yakeji na musamman,   kwanciya tayi luf acikin jikinsa, cikin muryan shagwaɓa tace.

"Hubby me mukeyi a asibiti?"

Sake matseta yayi, acikin jikinsa, haɗe da sanya hanunsa, yashiga shafa bayanta,  cikin wata irin murya yace. 
"Bansan dame zan iya biyanki  ba Zahrah, haƙiƙa ke ta musammance, kinkawo min farinciki, na musamman, kinsani acikin wata duniya,  me ɗauke da wasu surruka, wanda suke da wuyar mantawa, Inasonki My Wife! ina tsananin ƙaunarki, nagode miki sosai, Allah yayi miki albarka!"    "Inaasoonki!!" yakuma faɗa, in a slow sound, yana me sumbatar goshinta.

Mamakinsa ne yacika Zahrah, ita sam bata gane me yake nufi ba,  kyawawan fararen idanunta, ta zuba masa da'alamu tanason jin ƙarin bayani daga garesa.

Hanunsa yasa ya shafi gefen kumatunta, idanunsa É—aya, ya kashe mata, haÉ—e da cewa.
"Verry soon, ni da ke, zamu zama parents!"

"Parents?" ta maimaita sunan abakinta, da É—an mamaki.

"Yes, ni dake munkusa zama iyaye, saboda kina É—auke da, ciki!" yafaÉ—i haka yana murmushi.

Waro manya manyan idanunta tayi, haÉ—e da sanya hanu ta shafi kan É—akalallen cikinta.

"Ciki! inada ciki fa naji kace?"

"Eh kina ɗauke da cikina, yanzu haka ajikinki,  saura lokaci ƙanƙani kizama mummy's boy"

Wani irin madaran farinciki ne, taji yana ratsa duk wani ƙofar sadarwa dake jikinta, ko kusa koda wasa bata taɓa, kawo hakan acikin tunaninta ba,   rungumeshi ta sakeyi ƙam ƙam, haɗe da sakin wani irin murmushi, gaba ɗaya sai tanemi ciwon jikin nata ma ta rasa, "Ashe itama zata zama Mama? lallai  ALLAH  Abun godiya ne" tafaɗi haka acikin zuciyarta.

"Babyna mu koma gida ko?" yatambayeta, cike da tarairaya.
Dama ita uwar shagwaɓa ce, aikuwa tuni ta narke masa, haɗe da kaɗa masa kai, alamar
"Eh"

Karɓo musu takardan sallama yayi, haɗe da dawowa cikin ɗakin,  ɗagata yayi caɗak, yasanyata acikin ƙirjinsa, haka yanufi ƙofar fita, daga cikin ɗakin, shagwaɓa tasakamai, akan cewa ya sauƙeta ƙasa, zata iya takawa da ƙafafunta, amma fir yaƙi, waishi bayasone ko kyakkyawan motsi tayi, bayaso tasha wahala, haka suka fito cikin asibitin, kowa sai kallonsu yake, abokan aikinsa kuwa, dariya kawai sukeyi masa, sam basuyi mamaki ba, domin kuwa duk wanda yasan Dr.Sadeeq, to yasan,cewa, yana matuƙar ƙaunar Zahrah'n shi, domin ko da yaushe sunanta, nanan raɗau acikin bakinsa.
Chapter 98 · 0% Book details