← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 112

Sashe 106

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alokacin da Doctor yakarɓi jaririn ahanun Hajiya, kafesa yayi da manyan idanunsa, wani irin ƙaunar ɗan nasa ne ke fusgarsa, sosai yaron ke kama dashi, rungume ɗan yayi acikin ƙirjinsa, sai kawai ga hawaye nafita daga cikin idanunsa, kallonsa ya maida ga Zahrah wacce take bacci, wutar sonta ne ke ƙara ruruwa acikin zuciyarsa, lallai Zahrah tana da babban matsayi agareshi, ta basa farinciki me ɗorewa, tahaifa masa ɗa, tayi masa komai a duniyarnan, baisan damene zai saka mata ba.

Hajiya dakanta ta ƙira Inna tasanar mata maganan haihuwan, dama tuni Aunty Raliya kam ta tsofe a asibitin, koda su Inna sukaji cewa Zahrah ta haihu, ba ƙaramin farinciki sukayi ba, sunji daɗi sunyi murna sosai, ita da Baffa duka suka rankayo zuwa asibitin.

Ba ita tafarkaba sai bayan azahar, bathroom ɗin ɗakin da take ciki ta shiga, haɗe da sake tsabtace jikinta, tana fitowa kuwa tasamu Doctor ya karɓo musu takardan sallama. Gaba ɗaya likitotin asibitin babu wanda baitaya Dr.Sadeeq murnan samun ƙaruwan da yayi ba, har ɗaki suke zuwa su duba Zahrah, sukuma tayasu murna.

Hanyar da Hajiya taga ya miƙa ne yasanyata cewa.
"Wai ina zaka damu ne Sadeeq?"

Da compidence É—insa ya juyo gareta haÉ—e da cewa. "Gidana mana Hajiya"

"Gidanka? to ba gidanka zamuba, gidana zamuyi, hauka kake na É—auki yarinya da É—anyen jiki, na baka? wama zai tsaya ya kula da ita? maza juya akalar motarnan" Hajiya tafaÉ—i haka babu alamar wasa akan fuskarta.

Sam bahaka yasoba, amma babu yanda zaiyi, shikenan shi baza abarsa yaji ɗumin matarsa dana ɗansaba, haka yata ƙunƙuni acikin ransa shi kaɗai, har suka isa gidan Hajiya.

Abinci mai rai da lafiya Hajiya ta kawowa Zahrah, ga kuma gasashshen nama, bayan taci abincin Hajiya dakanta, tasakeyi mata wanka.
Zama tayi agaban mirror tashafe jikinta da manta me daɗin ƙamshi, powder tashafa afuskarta, bata tsaya nanba harda janbaki tashafawa laɓɓanta, ga kuma kwalli da ta sanyawa cikin idanunta, mascara ta ɗauko ta zizira akan eye lashes ɗinta, take fuskarta taƙarayin kyau. Wani riga da sket na material me tsada tasanya ajikinta, take takoma ƴar baby kamar yanda take da, dogon gashinta ta kanannaɗe a bayanta, haɗe da hayewa gado, zataci gaba da bacci, miƙo mata yaron Inna tayi haɗe da cewa "Wani kwanciya kuma zakiyi bayan baki bawa yaron nono ba?"

Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, da ƙyar ta iya ciro nonon nata ta kai bakin yaron, yana kamawa ta runtse idanunta da ƙarfi, saboda wani zafi da taji, haka dai ta ɗan daure, shikuwa yaron sai zuƙeta yake, gajiya tayi dajin zafin ta cire nonon abakinsa, kwantar dashi tayi, itama kana ta kwanta agefensa, baccin gajiya ne ya kuma ɗaukarta...

Idan dai hartaji sauƙan numfashinsa akan wuyanta, to yazame mata dole ne farkawa daga baccin da take, yanzu ma sauƙan numfashin nasa taji adai dai saitin kunnenta, a hankali take ware idanunta harta sauƙesu akansa. Murmushi yasakar mata haɗe da ɗaura kansa akan ƙirjinta.

"INA SONKI!!!" yafaÉ—a murya a sanyaye....

*(Insha Allah gobe zanmuku update, yau naso nayi da yawa, to wallahi tsoron editing nake, amma Insha Allah gobe kujira sabon posting, maybe ma yanzu kullum zanna baku update saboda mugama book É—in da wuri)*

*28/February/2020*

*✅OTE ME ON WATTPAD*
@fatymasardauna

#Love
#Romance
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      *SHU'UMIN NAMIJI !!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

         
*WATTPAD*
@fatymasrdauna

     *CHAPTER 115*

"NIMA INASONKA!"

Tafaɗa tana me lumshe idanunta. Iskan bakinsa ya hura mata akan fuskarta, haɗe da sake rungumeta,  ɗayan hanunsa yasanya ya shafi kan jaririn nasa, dake ta bacci.   Murmushi Zahrah tayi ganin yanda Dr.Sadeeq ya kafe yaron nasa da ido.    Hajiya da Inna ne suka shigo cikin ɗakin atare, da sauri Zahrah ta janye jikinta daga na doctor, shima a kunyace ya sauƙa daga kan gadon yana sosa kai.

"Hmmm Allah yashirya, Inna kina gani ko, wai da ahakan yakeso na basa ita" inji cewar Hajiya.

Murmushi kawai Inna tayi batace komai ba.  ( Su Inna anzama nitsaljin🤣)   Kallon Doctor Hajiya tayi haɗe da cewa "Zo muje inason magana dakai"  babu musu yabi bayanta suka fice daga cikin ɗakin.

Zama tayi akan kujera haÉ—e da maida hankalinta garesa.
"Me dame kake shiryawa sunan nanne?  sannan kuma da wani suna kayiwa yaron huɗu ba?"

Murmushi ya ɗanyi haɗe da cewa  "Ai nagama shirina tuntuni Hajiya, dama lokaci kawai muke jira,  sannan kuma dama tuntuni sunan babanta nake son sawa yaron, dashi kuma nayi masa huɗu ba"

Hajiya tace "Masha Allah, To Allah Ubangiji ya rayasa, hakan da kayi kuma ka kyauta, tashi kaje dama maganan da zamuyi kenan" 

Miƙewa yayi haɗe da yi mata sallama yafice daga cikin falon.

Lokacin da Husnah tazo ganin Baby kusan haukacewa tayi, sai santin yaron take wai yayi mata kyau sosai, komai nasa irin na babansa, ga idanunsa kyawawa, itadai Zahrah dariyanta kawai take, saboda itama Husnan tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki.

Akwatuna guda biyu Dr.Sadeeq ya  kawo wa Zahrah, ɗaya nata ɗaya na baby'nsa  wai kayan barka,  kayane masu kyau da tsadar gaske sosai ya kashe kuɗi, wai ahakanma wasu kayan nanan zuwa.

Kulawa Zahrah take samu a wajen Hajiya sosai, idan kaganta ma kamar ba itace ta haihu ba, sosai jikinta ya murje, tasakeyin fresh, hasken fatarta ma sosai ya ƙaru, komai nata ya cika, taƙara kyau akan nada, shikansa Dr.Sadeeq idan yaganta, ko son ɗauke idanunsa  akanta bayayi, saboda yanzu tasake zama wata mace ta musamman,  duk inda ta zauna kuwa ƙamshi take rabawa.

Ranar suna yaro yaci sunan baban Zahrah wato Adam, za'ana ƙiransa da (Asad) lokacin da labarin sunan  da aka sawa yaro yazo kunnen Zahrah sosai taji daɗi, wani irin farinciki taji acikin ranta, girman Doctor kuwa ya ƙaru acikin idanunta, ta tabbatar cewa shiɗin mai so da ƙaunarta ne.
Da sassafe meyi mata meckup tazo ta tsantsara mata ado, sosai fuskarta tasha kwalliya,  wani haɗaɗɗen lace orange and milk colour tasanya ajikinta, wanda yaji ɗinkin riga da sket irin 12 piecess ɗin nan, sosai kayan sukayi mata kyau, domin sunja kuɗi wajen sayansu da ɗinkasu, kowa yaga Zahrah da babynta saiyace masha Allah. Saboda  sunsha kyau sosai. Hidima sosai akayi tundaga kan abinci da abun sha, har izuwa abubuwan da za'a rabawa baƙi,  akwati guda biyu Hajiya tayiwa Zahrah da ɗanta, haka Baffa ma akwati yayi mata Inna ma zagewa tayi tayiwa Zahrah akwati shaƙe da kaya, Auntie Raliya ma akwati ta mata,  sosai Zahrah tasha kaya, har rasa inda zata sa kayan tayi,  ana cikin haka saiga kayan Dr.Sadeeq sun iso, akwatuna huɗu, biyu natane shaƙe da kaya,  sauran biyun kuwa  na yarontane,  bata gama mamakin irin dukiyar da Dr.Sadeeq yakashe mata ba, saiga Aunty Raliya tana rangaɗa guɗa, hanunta riƙe da key, danƙawa Zahrah key ɗin tayi ahanunta, haɗe da cewa "Ungo amsa kyautace ta musamman daga mijinki, ya baki kyautar gidansa dake cikin asokoro" mamakine ya kusan kashe Zahrah

"Gida kuma Aunty?" ta tambayi aunty Raliya don tayi tunanin ko kunnuwanta ne basu jiye mata da kyau ba.

"Ƙwarai kuwa gida, saima kinga gidan, don gidane me tsananin kyawun gaske, yafa kashe kuɗi sosai wajen ƙawata gidan"  Inji cewar Aunty Raliya.

"A'a Aunty gaskiya nikam banaso, wani irin kyautane haka? hidimar da Doctor yakeyi dani tayi yawa, daga haihuwata zuwa yau yakashe kuÉ—i yafi 3 million fa Auntie, yanzu kuma yace yabani kyautar gida suku tum, inajin tausayinsa Aunti banason nazama rauni acikin arzikinsa" Zahrah tafaÉ—i haka da iyaka gaskiyarta.

Murmushi Auntie Raliya tayi haÉ—e da sanya hanu ta dafa duka kafaÉ—un Zahrah.

"Kada ki damu Zahrah, shi ɗinfa mijinki ne, kuma kome zaimiki aduniyarnan bazai biyaki ba, kamar yanda kema bazaki iya biyansa duk abun daya miki ba, saboda haka babu wani abun damuwa don yamiki wannan kyautar, kin cancanci hakanne agareshi, don haka amshi makullin gidanki, ke dai kawai kiyi masa godiya, irin wacce ta dace" Aunty Raliya ta faɗi haka tana me damƙawa Zahrah makullin gidan ahanunta.

Kuka Zahrah ta fashe dashi tana jin ƙarin ƙaunar mijinnata na huda mata zuciya, lallai yazama dole agareta taƙara ƙaimi wajen kyautata masa. 

Yamma nayi aka haÉ—a walima me rai da lafiya, bayan malama tazo tagabatar da wa'azine akayi ciye ciye, aka kuma sha drinks, duk wanda yazo sunan kuwa babu wanda baisamu kyaututtuka ba, abun sai dai ace Alhamdulillah, kafun magriba tuni mutane sun watse, gida ya saura daga Hajiya sai Zahrah da kuma Aunty Raliya.

Wanka tasakeyi ta tsantsara ado cikin wani irin meterial me kyau da tsada, wanda yana cikin kayan da Doctor ya ɗinka mata don fitan suna, doguwar riga akayi mata wanda ya matuƙar kama jikinta sosai,  dogon gashinta dayasha saloon ta kanannaɗe atsakiyar kanta, ba abun dake fita ajikinta sai ƙamshin humra dana body spray.
Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan wayarta tashiga kan whatsapp, yaronta kuwa tuni dama yana wajen su Hajiya dake zaune a falo suna hira,   Sadiya me aikin Hajiya ce tashigo cikin ɗakin haɗe da sanarwa Zahrah cewa wai tayi baƙo yana falo.
Jitayi gabanta yaɗan faɗi, amma saita dake tace da Sadiyan tace da baƙon tana zuwa.
Mayafi ta É—auka ta yafa ajikinta, kana ta zura flat shoe É—inta, tafice daga cikin É—akin.

Su Hajiya tasamu zaune afalon, sai kuma wani, wanda bata ma taɓa ganin fuskarsa ba.  Kafun takai ga gaishesa, shiya ɗago mata gaisuwa, amsawa tayi tana ɗan murmushi,    gyara tsayuwansa yayi haɗe da cewa..

"Saƙone dama akabani nakawo miki, yana waje, idan ba damuwa muje saiki gani"

Kallon tsoro tashiga yi masa, saboda batasansa ba balle tasan wanene ya aikosa.

"Badamuwa, Raliya rakata sai kuje kuga saƙon ko"
Hajiya tafaÉ—i haka, don ta lura da tarin tsoron daya bayyana akan fuskar Zahrah'n.

Hakan kuwa akayi tare suka fita da Aunty Raliya.

A compound ɗin gidan suka tsaya gaban wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar mercedes maroon colour,  mutuminne ya bubbuɗe ƙofofin motar, take kayan dake shaƙe acikin motar suka bayyana, ɗan makulli ya miƙowa Zahrah haɗe da cewa
"Ranki ya daɗe gashi ni nacika umarnin da aka bani, wannan kyautace daga megida na, yace na ce miki Allah ya raya" 

Mamaki haɗe da al'ajabi ne suka kama Zahrah da Aunty Raliya. 
Chapter 106 · 0% Book details