← Book details Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 112

Sashe 3

Shu'umin Namiji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Alhaji Ma'aruf Chanji* shine sunan maihafin Zaid, Babban mutum ne da ake da mawa dashi acikin Nigeria, yana da kuɗi sosai, sannan mutum ne mai kyautatawa na ƙasa dashi, bashi da rowa ko kaɗan, matarsa ɗaya *Hajiya Safara'u* kuma itace ma haifiyar Zaid, daga Alhaji Ma'aruf har Hajiya Safara'u shuwa arab ne, Allah yayi musu baiwar kyau ga dukiya, shekaransu biyu da Aure Allah ya azurtasu, da haihuwan ɗa Namiji, wato Zaid, Zaid dai kyakkyawan gaske ne, domin tsananin kyawunsa ke sawa yake shiga ran jama'a, Zaid tun yana ƙarami yataso da wani irin Shu'umanci, ga mugunta, haka zalika baruwansa da shiga harkan kowa, hatta iyayensa kuwa, gaisuwa kawai keshiga tsakaninsu, duk yanda suka so yasake dasu amatsayinsu na mahaifansa, amma abun yaci tura, Sosai Iyayen Zaid ke nuna masa tsananin ƙauna, da tattali, asalin sana'ar Alhaji Ma'aruf shine Chanjin kuɗaɗe, yayi ƙaurin suna a sana'ar, sannan kuma yatara maƙudan kuɗaɗe, ganin harkan nasa natayin gaba dukiyarsa na ƙara yawa, yasanyashi tattarawa yakoma America da zama, can ya cigaba da business ɗinsa, duk ko yanda yaso Hajiya Safara'u tabiyo sa America suzauna ƙiyawa tayi, saidai Zaid yayarda yabi mahaifinsa, inda a can yasoma karatun sa,, Zaid yanada shekaru goma a duniya mahaifiyarsa ta haifa masa ƙanwa maisuna Labisat, Labisat dai kyakkyawar yarinyace suna kama da Zaid, saidai a gaskia Zaid yafita kyau sosai, domin idan kaga Zaid zakai tunanin ba ɗan Nigeria bane,,,, acan America mahaifin Zaid kasuwancinsa kawai yasa a gaba, amma sa'i da lokaci yana zuwa Nigeria duba iyalansa,, Yanayin yanda yake gudanar da kasuwancinsa a America yasanya bashida wani kyakkyawan lokacin da zai kula da ɗansa wato Zaid, kullum Alhaji Ma'aruf idan yafita office baya dawowa sai dare, shikuwa Zaid rayurwasa yakeyi da turawan abokansa, wanda yayisu acikin school ɗin dayake, kunsan dai su turawa, babu wani abun daya damesu iskanci sun maidashi kamar ruwan sha, domin dai dayawansu ba addinin Allah suka sani ba balle su kiyaye, tun Zaid na da shekara 17 yafuskanci abokansa na school suna neman mata, shikuwa sam alokacin mata basa gabansa, duk da kuwa cewa suna kawo masa tallen kansu, amma baya sauraransu, duka abokan Zaid turawa ne, sai mutum ɗaya wato *ABID* Abid cikekken ɗan Nigeria ne cikin garin Abuja shima gidansu yake, sannan babansa shine Minister'n Man Fetur na Nigeria gaba ɗaya, Abid hatsabibin ɗan iska ne kuma tantiri domin kuwa tun yana ƙaraminsa yasan yanda zai jagwalgwala mace, Zaid da Abid a bota suke sosai, domin jininsu yazo ɗaya,, duk da cewa Zaid yana da ƙarfin sha'awa amma bayabin mata, saidai wani zubin yakan ɗan mawa mace kiss da dai sauransu,, lokacin da Zaid yake matakin lavel 2 na degree ɗinsa lokacin yana da shekara 21, Allah ya jefomasa ƙaddaransa kuma Hargitsi mafarin halakarsa,,, wata rana sunje yawon shaƙatawa shida saiɗanun abokansa, ya haɗu da wata ƴar iskan baturiya mai suna Nicky, abun daya fa ra ɗaukar hankalin Zaid game da Nicky shine kyawu da surarta, Nicky irin fitinannun matan nanne, shu'umai wanda idan suka ɗiga tsamansu akan abu tofa sai sun sameshi, tunda Nicky tayi ido huɗu da Zaid gaba ɗaya hankalinta yatashi, domin kuwa Zaid yayi mata hundred percent, bawani ɓata lokaci tabayyana masa soyayyarta a gareshi, Zaid kuwa dake ɗan izza ne saiya soma ja mata aji,, daga ƙarshe dai daya tabbatar da cewa itaɗin bata bibiyar maza sai ya amsa soyayyarta suka cigaba da shan love ɗinsu,,

Watarana Zaid yana kwance a ɗakinsa, sai ganin Nicky kawai yayi sanye da wani irin ɗan iskan kaya wanda yabayyana komai na surarta a fili, ganin da yayi mawa Nicky a haka baƙaramin ɗaga masa hankali yayiba, wata irin sha'awa yakeji mai ɗaga hankali, koda Nicky tafahimci haka saita yi amfani da damanta tasake ruɗa Zaid da irin salonta, jawo Nicky yayi jikinsa yashiga sun batarta tako ina, a rannan sheɗan yaribaci Zaid har yakusanci Nicky, tun da yake a duniya baitaɓa sanin ya daɗin Sex yake ba sai awannan ranan, baisan ya ƴa mace take ba shidai kallon su kawai yake, amma sai gashi yau yasani,, wani irin gamsuwa Nicky tasamu da Zaid a ranan wanda bata taɓa samun irin shi da ga wani ɗa Namiji ba,, tundaga Wannan rana Zaid yazama mashahurin ɗan iska kullum yana tare da Nicky suna aikata Zina, arana sai Zaid yayi Sex da Nicky sau Biyar,

Zaid mutum ne mai ƙyan ƙyami, shiyasa kwata kwata baya neman sauran matan turawa domin yasansu kowa buɗe ma ƙafa suke yashige,, Nicky ce kaɗai abokiyar watsewarsa, itama dan yafuskanci cewa bata mu'amala da kowani na Miji ne, sannu ahankali Zaid yasoma shan giya, koda Abid yafuskanci cewa abokinnasa ya soma baza iskancinsa, sai yasake haɗasa da wasu ƴam mata gangariya, aikuwa Zaid baiƙiba, nanfa iskancinsa yaci gaba da tumbatsa, haryazo ya fi ƙarfin Nicky, Ƙaurin isknacin Zaid har yaɗara na abokansa,domin ko Abid yanzu Zaid yafisa sanin kan mace da kuma iya iskanci,,,, duk wannan halin da Zaid ke ciki Dadynsa Alhaji Ma'aruf baisaniba, yanacan yasa harkan kuɗinsa a gaba, yakuwa mallaki dukiya masu mahaukatan yawa,, akwana atashi Zaid ya kammala degree ɗinsa, cikin ikon Allah kuwa yasamu kyakkyawan result, domin dai yanada ƙoƙari sosai, iskancinsa baisa yadaina karatu ba,, bawani ɓata lokaci Zaid yawuce London domin yin masters ɗinsa acan, hmmmm zuwansa London yaƙara masa iskanci sosai, shima Abid biyosa london ɗin yayi suka ci gaba da zuba iskancinsu acan,, Zaid yazama tantirin shu'umi idan yaga mace matuƙar tayi masa tofa saiyayi sex da'ita,, duk wannan tsawon shekarun da Zaid yaɗauka aƙasashen duniya, sauɗaya tak yazo Nigeria nanma satinsa biyu kacal ya tattara ya koma,,

Kwanci tashi Zaid yakammala Masters ɗinsa, take kuma wani Babban banki dake london suka nemi da yayi aiki dasu, sam bai amince da buƙatarsu ba, domin shi yafiso yayi kasuwanci, maƙudan kuɗaɗe Dadynsa yasanya masa wajen gina masa wani katafaren kamfani a London, shahararren kamfani aka gina masa na ƙera takalma da jakakkuna new styles, masha Allah cikin ƙanƙanin lokaci kamfanin Zaid ya shahara a faɗin duniya domin, kaya masu kyau da inganci suke bugawa,, Zaid yana karatu kuma yana kasuwancinsa harya kammala P.H.D ɗinsa, isakanci kuwa yaci uban na da,, wasa gaske saiga Zaid ya mallaki Company's a ƙasa she da dama, lokaci ɗaya Zaid yayi wani irin mahaukacin kuɗi, baiyi ƙasa a guiwa ba ya dawo Nigeria yakuma gina wani kamfani'n da ake ƙera gyalelluka wato vails, tunda ya dawo Nigeria baisake komawa ko wacce ƙasa ba, domin yaji ƙasar tasa wato Nigeria tayi masa daɗi, company's ɗinsa na ƙasashen waje kuwa, yasanya amintattun mutanensa suna kula masa da su......

Cigan Labari...

Daga Club É—innan Zaid baizarce ko'ina ba sai guest house É—insa, koda ya isa yasamu tuni Asmee tazo tana jiransa,, tundaga falo Zaid suka soma watsewa shida Asmee,, ........

((Kuyi haƙuri jiya kunjini shiru, walƙahi wayatace ba charge.))

*13/October/2019*

*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed 📵*

*Chapter 5 то 6*

Haka Zaid da Asmee suka ɓata dare suna iskancinsu, basa ko tsoron Allah mahalicci,, haƙiƙa zuciyar Zaid ta bushe ƙarau, baya ko tuna azabar da Ubangiji zaiyi masa, aduk sanda yaje garesa batare da ya tuba ba.......

Kasancewar yau basu da lecture sai 12 pm yasanya gaba ɗaya aikin gidan itatayi shi, yayin da Inna ke kishingiɗe akan tabarma,, da bala'i Baffa yashigo cikin gidan " Wallahi ni nagaji bazan iyaba ehe, ace akan yarinya kwara ɗaya tol duk inda nagilma mutane zagina sukeyi, to bata saɓuwa, ke Zahrah inakike ne dan Ubanki ?" Baffa yaƙare maganar cikin hargowa, Zahrah dake cikin kitchine tafito jikinta a sanyaye domin tasan kwanan zancen,, "Lafiya kuwa Malam kashigo gida kana ɓaɓatu ?" Inna dake kwance tatambayeshi, " Kema kinsani ai akan wannan yarinyar ce mana Zahrah taƙi fito da Miji tayi aure, tananan koda yaushe cikin bulayin zuwa makaranta, makarantan da ba tsinana mata komai zaiyi ba, to wallahi nagaji, ko ina gulma ake wai nakasa riƙe amanar da ɗan uwana yabani, naƙi aurar da yarinya nasata karatu, bayan nafi kowa tsanar wannan ɗan iskan karatun da takeyi " "Ke Zahrah !!" yaƙira sunan Zahrah da kakkausar murya, batare da yabari ta amsa masa ba yaci gaba da cewa " bazan iyawa zagin mutane ba, nabaki nanda wasu kwanaki ki fito da miji koda kuwa musaki ne na tattaraki nayi miki aure batare da wani kayan ɗakiba, kije can ki ƙarata " Baffa nakaiwa nan a zancensa ya sakai yashige cikin ɗaki, Inna tarufa masa baya,,, ɗaki Zahrah ta koma haɗe da zama akan ƴar yalolon katifarta, " ya Allah gani gareka kafi kowa sanin halin da nake ciki ya Allah kakawomin ɗoki " wasu zafafan hawayene suka shiga sauƙa daga kan fuskar Zahrah, maganar kenan koda yaushe Miji Miji, wai shin ina zata samo mijin da zai aureta ? tun da take a duniya Namiji ɗaya ne yataɓa cewa yanasonta, kuma shima tundaga wannan ranan bata sake sashi acikin idanun taba, tayi imani cewa tana da tsantsar kyau da kuma sura, wanda zai iya janyo hankalin ko wani ɗa namiji zuwa gareta, amma maiyasa babu wani Namiji dake kallonta ballan tana harya furta mata kalman so ? tayi mawa kanta tambayar da bata da amsa,, jin motsin Inna a tsakar gida yasa tayi saurin share hawayenta, haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, kuɗi Inna taciro daga kunkuminta, haɗe da miƙamawa Zahrah tace "Ungo maza kaima wa Ladidi mai adashe kice mata ga zubina na jiya " "to" kawai Zahrah tace haɗe da nufar hanyar fita daga gidan, domin dai dama sanye take da hijab ajikinta, al'adar ta ce bata zama babu hijabi, saidai idan a ɗakinta take....
Chapter 3 · 0% Book details